← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 123

Sashe 66

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana karbar masu daki aka basa makulli ya bar reception din, ita dai tana biye da shi, babban daki ne mai kyau da makeken gado, ganin tsaye tayi bakin kofa ya juya yana kallonta, taki barin su hada ido, murmushi yayi yace "Yar shariyar ce a kusa baby?" Kin cewa komai tayi ta ki kallonsa kuma har lkcn, bai kuma ce mata komai ba ya kunna Ac yyi kwanciyarsa, ko minti goma bai yi da kwanciya ba bacci ya daukesa, har fa lkcn Samhan ku na tsaye tana kare ma daki kallo, lkci lkci kuma ta kallesa, can dai da taga kmr baccinsa yyi ta karasa dakin ta ajiye ledan kayan hannunta ta xauna can karshen gadon tana satan kallonsa, can ta mike a hankali ta dawo gefensa ta xauna tana kallon fuskarsa, sosai taga ya rame lkci daya jikinta yyi sanyi, ta fi minti ashirin tana xaune wajen kafin ta sauka kasa a hankali ta kwanta kan tiles din dakin, har aka fara kiraye kirayen magrib tana k'asa kwance, jin xa a tada sllh ta mike xaune tana kallonsa, ganin ya juya kansa xuwa daya side din ta mike ta isa kusa da shi a hankali ta durkusa tace "Xa a tada sllh fah doctor" jin baxae taba jin ta ba a haka ta dan tabo hannunsa a hankali, dauke hannunta tayi jin jikinsa da xafi, ta mike ta karasa xuwa daya side din ga mamakinta sai taga idonsa biyu, durkusawa ta kuma yi gabansa da damuwa tace "Are you sick?" Murmushin karfin hali yyi mata a hankali yace "it's just headache dear" xaunawa tayi gefensa kamar xata yi kuka tace "toh baka sha magani ba kuma" mikewa yyi xaune da kyar yace "Xan sha" xata yi magana yayi mata murmushi ya kamo hannunta yace "I will be alryt baby, bari in je sllh xan siyo magani" daga haka ya tashi ya shiga bathroom, tana nn ynda ya bar ta har ya fito yace mata ya tafi masallaci, kai ta gyada masa ya fita, sai kusan karfe bakwai ya shigo rike da leda hannunsa yana ajiyewa ya kwanta hade da rufe ido, karasawa tayi kusa da ledan ta bude taga abinci ne sai drugs, ta bude abincin ta dawo kusa da shi tace "Toh ka tashi ka ci abincin sae ka sha maganin" ba tare da ya bude idonsa ba yace "Later" da ganinsa kasan karfin hali kawai yake, ta fashe da kuka sosai, ae bae san lkcn da ya bude ido ya mike xaune da sauri ba ya kamo hannunta yace "Kuka kuma baby" ganin kukan sae karuwa yake ya mike tsaye da kyar yace "Toh xan ci yanxu" haka ta sa shi gaba yana tura abincin da kyar ko rabi bai ci ba yace "Am full dear" ita ta bude magungunan ta mika masa ya sha snn ya koma xai kwanta ta rikosa, ya kalleta a hankali yace "Baby..." Bata bari sun hada ido ba ta shiga unbuttoning din masa shirt din jikinsa ta cire gaba daya ya rage masa singlet, tace "Baxa ka yi wanka ba" girgixa mata kai yyi yace "Ltr" daga haka ta rabu da shi ya kwanta, tana xaune har aka kira isha ganin kmr bacci yake ta mike ta cire kayan jikinta ta nufi ledan kayanta me dauke da turarruka me yawa har da kaya da Zainab ta bata xata dau xani, juyowa yyi jin motsin leda, ta xaro ido ta durkushe wajen da sauri, murmushi yyi ya dauke kansa, ta dau xanin ta daura da sauri snn ta saka hijab, karasawa tayi kusa da shi ta xauna ba tare da ta bari sun hada ido ba ta taba forehead dinsa taji xafin ba mai yawa bane, bakinta kadai ne yyi motsi wajen cewa "Sorryy...." Ya jawota jikinsa ya rungumeta hade da lumshe ido, kasa yin komai tayi, tayi lamo tana jin bugun xuciyarsa, a hankali ya kai bakinsa kunnenta cikin sanyin murya yace "I love you Samantha" bata iya tace komai ba, jin hannunsa cikin hijab dinta ta kwace kanta da sauri ta mike, murmushi yyi bai bude idonsa dake lumshe ba, tayi shigewarta bayi, ko da ta fito kasa tantance ko bacci yake ko kuma idonsa biyu tayi, ta je daya side din ta durkusa tana yi tana lekensa har ta gama shirinta cikin doguwar riga mara nauyi ta feshe jikinta da turare, drink kawai ta sha don bata jin yunwa, ta xauna har kusan sha daya, ynxu kam ta gane bacci yake, jin ta fara jin bacci ta mike tana tunanin inda xata kwanta don dakin ya dau sanyi sbda ac dake kunne hakan yasa baxata iya kwanciyar k'asa ba, a hankali ta isa kan gadon ta kwanta can nesa da shi ta rakube gu daya, sai kuma ta nemi baccin ta rasa, ta gaji da juye juyenta ta mirgina a hankali kusa da shi ta taba jikinsa taji har lkcn da sauran xaxxabi, gani kawai tayi ya juyo ya jawota jikinsa, kkrin sauka ta shiga yi da sauri taji ya kirata murya can kasa, still tayi bata kuma motsi ba, ya kwantar da kansa jikinta yace "I will love you till my last breathe wife" shiru tayi bata ce komai ba, ya maidota jikinsa ta lumshe ido, a hankali yace "Can i kiss you?" bai jira amsarta ba taji bakinsa cikin nata, kasa hanasa tayi sai dai yana jin ynda xuciyarta ke bugawa, ya lumshe ido ya shiga kissing dinta daga nn kuma ya fara xarcewa ba tare da ya sani ba, hawayenta da yaji a hannunsa yasa ya kyaleta da sauri yace "Baki so koh baby?" Kai ta gyada masa, ya rungumeta sosai yace "Toh na bari..." A haka bacci ya dauketa jikinsa, bai kuma yin bacci ba, can dai ya kwantar da ita a hankali ya mike ya shiga bathroom, wanka yyi ya dauro alwala ya fito, yana xaune kan darduma kusan karfe biyu yaga tana juye juye sai kuma ta sauko daga kan gadon, mikewa yayi ya isa gabanta ya durkusa yace "What happened" daura kanta tayi kan gadon tace "Cikina" ya dagota suka xauna gefen gadon yace "Maganin ki ya kare ne?" Girgixa masa kai tayi kmr xata yi kuka tace "Na mance su can gidan" shiru yyi yana kallonta snn ya kalli agogo, sae kuma ya mike ya shiga bathroom.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By Khaleesat Haiydar
_This page goes to you my Sharifath a sis frm another mum, sai ki shirya mai da ni_
61.....

Ba a dau lkci ba ya fito ya dau goran swan water ya koma bayin, k'asa ya sameta xata fara kuka ya iso gabanta rike da goran da ya xuba ruwa me d'an xafi a ciki ya ajiye, ya dagota ya kwantar kan gadon, daga rigar jikinta taga xae yi ta xaro ido hade da mikewa ta rike rigar tace "Doctor..." Yace "Yea, am a doctor, ko kin mance ne" tashi take son yi kan gadon ya mayar da ita ya kwantar yace "You stay still ko in yi kwanciyata in kyale ki da ciwon ki" tace "Ehh kayi kwanciyar ka, bana so" bai kuma sauraranta ba ya kwantar da ita ya dage rigar ta rike da karfi ta sakar masa kuka tace "Ni ka kyaleni me xaka min, nace bana so" dariya ta basa ya dake yace "Xan tsayar da ciwon ne baby, ko nayi laifi?

Am just tryn to be of help" kmr xata yi kuka tace "Toh dole sai ka daga min riga?" Yace "Ehh mana dear" ganin da gaske yake tace "Toh ni dai ka kashe wutan bana so" murmushi yyi yace "Wai kunyata kike ji yarinya, xa ma ki daina ne soon" daga haka ya mike ya kashe wutan dakin ya dawo, tana yi tana rike hannunsa har ya daga rigar ya dau ruwan goran, kwacewa tayi tace "Xan yi da kai na, i can my self" kallonta ya tsaya yi xata mike ya mayar da ita ya kwantar ta fashe da kuka tace "Ni nace bana so doctor, let me" kyaleta yyi, yayi kwanciyarsa ya juya mata baya, bai san ynda ta kare ba dai daga karshe yaji ta kwanta, yana jinta tana ta juye juyenta bai ko juyo ba bare yace mata komai, bayan kusan awa daya yaji tana kuka a hankali, murmushi yyi can ya juyo yana kallonta, baya ta juya masa ita ma, a hankali ya isa kusa da ita ya jawo ta jikinsa ya kai hannunsa Abdomen dinta murya can kasa yace "Kina min gardama in maki abinda xa ki ji kunya ynxu" ita dai tasan ba dainawa ciwon yyi ba amma taji ta d'an samu relief, lamo tayi jikinsa idonta lumshe, jin ya fara canxa salo ta buge hannunsa xata mike ya juyo da ita ya kankameta murya can kasa yace "Are you daring me?" bata fuska tayi ta boye kanta a kirjinsa, har kusan karfe biyu suna nn a haka yaji alamar bacci ya dauketa.
Chapter 66 · 0% Book details