← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 123

Sashe 81

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan la'asar Samha ta fito don daura dinner, yana xaune da su Ilham a parlor gaba daya hankalinsu na kan laptop, ya bi ta da ido har ta shiga kitchen, can ya mike ya bi bayanta, Ilham da Khaleesat suka kalli junansu, a tare suka tabe baki, Ya rungume hannayensa yana kallonta yace "Me xa kiyi baby?" Tace "Abinci xan daura" yace "Ki bar su ilham su yi, since they r doin nothing, beside u re nt feeling fine" tace "A'a xan yi da kai na, am now okay" juyawa yyi ya fita ya koma gun kannin nasa yace "Alryt kallon ya isa haka ku tashi ku shiga ku girka dinner" Khaleesat ta xaro ido tace "Dinner kuma yaya?" Yace "Yes ko breakfast kika ji nace?" Bata ce komai ba ta dauke kai, yace "Ko baxa ku tashi ba?" Ilham ta bata fuska tace "Toh mu ba mu san me xa a dafa ba fa" yace "Ku shiga ku dafa duk abinda kuka ga ya dace" hade rai yyi ganin sun ki tashi yace "You girls shud'nt push me into laying my hands on any of you before leaving this house" ba shiri duk suka mike, ya nufi kitchen suka bi bayansa khaleesat har da hawayenta, yana shiga kitchen din ya janyo Samha suka fita, kallon mamaki take masa tace "Meye haka doctor?" Yace "Nace baxa ki yi girkin ba nurse" daga haka ya ja ta ya komar da ita daki.

Tagumi Rachael tayi tana kallon priest din dake xaune gabanta, Vivian dai sai gyara gyaran zama take don ta gaji da xaman, sun fi awa daya zaune gaban priest din har lkcn bai ce komai ba, priest din ya d'ago kai daga karshe ya nisa yace "Rachael!" Mahaifiyar Samha ta gyara xama da sauri tace "Na'am Father" ya girgixa kai yace " 'yar ki xata dawo, sai dai ba ita kadai ba" Rachael na kikkifta ido tace "Tohhh...

Ita da wa Father" yace "ita da jikokin ki" kallon Sarah tayi a rikice tace "God forbid!" Nan da nn idonta ya kawo ruwa cikin raunin murya tace "Jikoki kuma Father??" Yace "Kwarai kuwa" ta fashe da kuka sosai tace "Blood of jesus, Ai ni nasan na shiga uku na lalace, amma yaushe kaga dawowan nata father?" Yace "Wannan kuma sai mu bar ma Jehovah sani" Ta kuma rushewa da kuka tace "Father ya xan yi da raina, wnn 'ya ita knn gare ni, ni kadai nasan abinda nake ji rashin Rebecca, nayi kwanciyar asibiti ya fi a kirga, to 'ya yan ubanwa xata taho min da..." Ta kuma rusa wani uban kukan tace "Amma Jehovah ya isa tsakanina da musulmin nn, ya cuce ni ya cuceni" Vivian dai tagumi kawai tayi bata ce komai ba, Priest din ya girgixa kai yace "Am giving u assurance yarinyar ki xata dawo gare ki sai dai xa a dau lkci me tsawo kuma Allah bai nuna min lkcn ba, sai dai ina son ki sani cewa akwai sa hannun yan uwan mijin ki a lamarin nn, wasun su kuma sun san inda take" Rachael ta share hawayenta da sauri tana xaro ido tace "yan uwan mijina kuma father?" Ya gyada mata kai yace "Kwarai kuwa" Tace "Heyyy! father yan uwansa uku ne ke raye ae yanxu....

Daga Sarah sai wata Maryam dake kaduna sai yayarsu dake Ghana to waye cikinsu xae cuce ni haka, nasan Sarah baxata cuceni ba" sai ta kuma fashewa da wani sabon kukan tace "Sae dai algungumar musulman nn Maryam, kai ni na ma san ita ce, amma Allah ya isar mani tun a duniya" Sarah tace "Ki kwantar da hankalin ki sister, in har Maryam ce sai tayi regretting action dinta, ni dama tun da naji musulma ce matar nn kwata kwata ta fice min a rai, in har tasan whereabout din Samantha ta bari muke ta garari sai na yi mata abinda har ta bar duniya baxa ta mance ba" Rachael na share hawayen fuskarta tace "Man of God wani aiki nake son ka min don Allah" ya gyada kai yace "Fadi me kike so" ta kara gyara xama ta tsuke fuska a nutse tace "So nake ka min addu'a wanda xai sa Samantha tayi da ta sanin bin musulmi, so nake kasa shi musulmin ya mayar da rayuwarta so miserable, so nake kasa ya walakantata karshen wlknci infact he shud just make life worst nd miserable for her" tana huci ta kare maganan, Priest din na jinjina kai yace "Wnn abu me sauki ne ai" Tace "Sai dai fa kar ayi wanda xai sa in rasa 'ya ta, kawai dai a d'an wujijjigata ne ta dawo gida, snn wnn jikan da kace xa a taho min da kayi duk abinda xaka yi kar ya iso duniya" Daga haka ta bude jakarta ta fiddo kudi me yawa ta ajiye masa tana godiya, Vivian tace "Toh shi dan iskan a haka za a bar shi?" Rachael tayi murmushin mugunta tace "Jira 'ya ta ta dawo gare ni ki ga abinda shi kuma xan masa" daga haka ta mike tsaye suka sallami priest din suka fita.

Da daddare Abuturrab na xaune tare da Small mum dinsa a daki tace "Gobe fa xa mu koma Haiydar" ya kalleta yace "Gobe kuma mum?" Tace "In sha Allah" ya marairace mata yace "But i thought sati xa ku yi ae" ta hararesa tace "So kke col ya dau hanyar yobe don dauko yaransa koh?" Murmushi yyi yace "Toh mum su koma su sai ke kiyi sati daya" ta kuma hararansa tace "Aikin sai in bar maka knn" ya bata fuska yace "Mum to sai yaushe kuma?" Tace "Ranan da kaje kano" murmushi ya kuma yi bai ce komai ba, can yace "toh amma da yamma xa ku tafi ko mum?" Tace "Sai mu isa da yaushe?" Yace "Sai in biya maku flight mum" tace "Noo, da safe xa mu wuce Aliyu, kar ka damu xan dawo wani lkcn" bai kuma cewa komai ba, sae dai yaji har ya fara missing din mum din tasa da sisters dinsa, sun jima suna hira daga bisanni yyi mata sai da safe kusan karfe sha biyu, bedroom dinsa ya bude ya ga sisters dinsa har sun yi bacci ya rufe masu kofa ya wuce daki, ita ma Samha har tayi bacci, ya kashe wutan dakin ya kunna Ac ya cire jallabiyan jikinsa ya isa kan gadon ya xauna gefenta yana shafa fuskarta, a hankali ta bude ido ya duka dab da ita yace "Haka muka yi da ke?" Kmr xata yi kuka tace "Doctor bacci naki ji" kwanciya yyi gefenta yace "Toh yi baccin ki wife" juya masa baya tayi ya jawota jikinsa a hankali.

Da asuba yana dawowa masallaci ya tarar har ta tashi ya xauna gefen gado yace "Baby yau fa su mum xa su wuce" tace "Yau kuma" ya gyada mata kai, ta langwabar da kai tace "So early?" Mikewa yyi yace "Yea, just a day leave ta dauka a gun aiki" karfe tara mum ta gama shiryawa bayan sun yi breakfast, su ilham ma duk sun gama shiryawa, Samha ta bi Abuturrab bedroom tace "Doctor ni bn san me xan ba su ilham ba" ya juya ya kalleta, sai kuma yyi murmushi yace "don't worry i will give them on ur behalf baby, laifina ne bana baki kudi koh?" Tace "Toh idan ka ban kudi me xan yi da shi?" Yace "Ga irin abinda xa kiyi da shi nn ai" bata ce komai ba ya ja hancinta yana murmushi yace "Toh mu je mu kai su park" ko da suka fito parlor khaleesat ce kadai tana sa jewelries dinta, yace "Ina mum?" Tace "Ta je part din su fatima" yace "Ohk" bayan kusan minti sha biyar Ummi suka taho tare da Hajiya Mariya, sai kusan karfe goma suka bar gidan bayan ta ba Samha turarruka masu yawa da ta hado mata har da na wuta, ta kuma yi mata nasiha sosai ta bata shawarwari, suna isa park Hajiya Mariya tace "Aliyu kayan ka na booth na mance ban fada maka ba wllh" yace "Toh mum" shi ya biya masu kudin mota duk da ynda Hajiya Mariya ta dinga hanasa, ya ba kanninsa dubu goma bayan sun karba yace "Samha tace a baku" kallonta suka yi gaba daya, khaleesat ta dauke kai hade da kyabe baki, Hajiya Mariya ta ja Samha ta bude jakarta ta ciro box din dankunne ta mika mata tace "Gashi daughter ki sa a kunnen ki, sae na dawo wani lkcn kin ji" sunkuyar da kai Samha tayi lkci daya hawaye ya cika idonta ta dan risina ta karba cikin sanyin murya tace "Nagode mum" Hajiya Mariya tayi murmushi ta dago kanta tace "Kuka kuma Samha" girgixa mata kai Samha tayi tana kkrin mayar da hawayen, Abuturrab dake tsaye tare da su Ilham ya juya ya kallesu yyi murmushi ya dauke kai, Khaleesat da har ta fara hawaye tace "Yayanmu yaushe xaka dawo gida plss" Ya kama hannunta yace "Soon sweet sis, ku gaida min da Ramla sosai kuce mata i missed her a lot" Ilham ta fashe da kuka ya wara ido yace "Kee a park din kuma" jawota yyi ya rungumeta yace "Kar ku damu sisters, soon xan dawo gida kun ji" A haka mota ta cika Hajiya Mariya ta fara shiga snn Khaleesat dake hawaye, yana rike da hannun Ilham ta shiga motar don kin sakesa tayi, yyi pecking hannun nata yace "I will miss you all sisters" daga haka ya xame hannunsa, sai kallonsu mutanen cikin motar suke, Ya daga ma Small mum dinsa hannu snn ya juya ya bar gun, banda kuka bbu abinda Samha ma take, motar na fara tafiya ta daga ma su Ilham hannu, Yayansu suka kalla kafin su daga mata hannun su ma, murmushi yyi ya bi motar da ido har suka fita park din kafin ya juya ya bude front seat yana kallon Samha yace "Toh kukan ya isa haka shiga mu tafi" tana shiga motar ya rufe ya xaga ya shiga maxaunin driver.
Chapter 81 · 0% Book details