← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 123

Sashe 26

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta koma ta kwanta a hankali, can kuma ta mike xaune tayi tagumi, to ko taje ne, tunanin da take kenan, kawai ta mike ta kashe wutan dakinta ta bude kofa a hankali ta fita, blessing na parlor ta karasa kusa da ita tace "Blessing idan Abba ya kirani kice masa nayi bacci" Blessing tace "Toh" kamar munafuka ta fita gidan ta dau hanyar gidansu Abuturrab, a hankali ta tura gate ta shiga ta karasa balcony ta bude kofar parlor ta shiga, mikewa yayi yana kallonta ya nufeta yayi murmushi yace "Thanks dear!" Ta langwabar da kai tace "What's the call about?" Hannu ya sa a goshinta yaji xafi yace "Tun yaushe ne baki da lafiya?" A hankali tace "Since" ya kamo hannunta da damuwa yace "And you didn't tell me, wani maganin kike sha?" Janye hannunta tayi tace "How did you know my dad?" Murmushi yayi yace "Kin raina kitaba ta ne?" Bata ce komai ba, ya kama hannunta ya xaunar da ita kan kujera yace am coming, bin sa tayi da kallo ya shiga daki, can ya fito rike da stethoscope da thermometer, ya dawo kusa da ita ya xauna yana kallon kirjinta murya can kasa yace "how will i get to ur chest?" Ta masa wani kallo tace "What?" Murmushi yayi yace "Yeah, i want to use my stethoscope on u!" Tace "Toh bana so!" Wani kallo ya mata ya jawo ta kusa da shi ta xaro ido xata yi magana taji hannunsa a bayanta, a hankali ya xuge xip din ya sauke doguwar rigar kasa ya rage farin vest din jikinta, wani kallo take masa xata yi magana ya daura fingers dinsa guda biyu a lips dinta yana kallon cikin oily eyes dinta, daukar stethoscope din yayi ya makala a kunne, snn ya daga vest din a hankali ya manna daga kasan kirjinta, lumshe ido tayi, shi ko sai kallonta yake, can ya lumshe nasa idon ya cire instrument din ya ajiye ya sauke vest din, ya mayar mata da rigarta ya ja zip ya mike, sai a snn ta bude ido taga daki ya wuce, ba a dau lkci ba ya dawo da magunguna har da allura, tana ganin haka tace "Baxan karba allura ba" bai tanka taba ya xauna ya gama hada alluran snn yace "Kin shirya" bai jira tace komai ba ya mike yana kallonta yace "Am waiting" kamar xata yi kuka tace "Ni bana so nace" hade rai yayi ya dago ta, bata ankara ba sai ji tayi yana kkrin daga mata riga tace "Noooo" ya wani daure fuska yace "What?" Kamar xata yi kuka tace "Doctor there's nothing inside, just..." Dariya ta basa ya dake yace "Then???" Bata ce komai ba ta marairaice tana kallonsa, yace "Ohk Alryt!" Kama hannunta yayi ya isa gun switch din wutan ya kashe, duhu ya gauraye parlon, ya daga rigar gaba daya tace "Doctorrrr..." Dafa bango tayi ta runtse ido jikinta na rawa, har ta ji ya xare alluran, bata ankara ba taji ya rungumeta ta baya ya daura kansa a shoulder dinta murya can kasa "Get well soon wife" bude ido tayi da sauri, ya juyo da ita yana kallonta cikin duhun yace "Ki bar wahalar da ni Samha, stop pretending you don't know where i am heading, i know you know....." Rungumeta yayi cikin sanyin murya yace "I love you!" Ita dai bata iya tace komai ba, ya matse ta jikinsa yace "Kice abu mana dear, talk plsss" kamar mara lafiya yayi maganan, ta lumshe ido a hankali tana jin yanda xuciyarsa ke bugawa, harde hannunta yayi da na shi murya can kasa yace "Talk plss, say something Samha" ta rasa abinda xata ce, shafa bayanta ya fara yi a hankali ya kai bakinsa wuyanta, ta bude ido da sauri jin saukan numfashinsa a jikinta, lkci daya jikinta ya dau rawa da kyar tace "Doctor stop pls...." Cikin kasalalliyar murya yace "Talk! second love" Ta kuma runtse ido jin ya ki dauke lips dinsa a wuyanta, murya can kasa tace "I...

I...

I...

Love you tooo" wara ido yayi ya saketa yace "Da gaske baby??" Ja baya ta dinga yi kawai sai gani yyi ta juya a guje ta nufi kofa ta bude ta fice.

Washegari asabar da yamma Abuturrab ya iso gidan Mr David da da magungunan da xai ba Samantha jiya ta gudu, Mumy ya tarar xaune parlor tare da Mr David din bayan an masa izinin shigowa ya gaisheta ta dinga masa wani kallon mamaki, Mr David ya mike yace "Likitan da nake fadi maki kenan" daga haka yace ma Abuturrab ya taho sama, Abuturab ya bi bayansa suka wuce saman, yau ma bbu wani 6ata lkci ya gama basa medication din, ya tambayi samantha, Mr David yace ta tafi church, shiru Abuturrab yyi sai kuma yace "But da ta hakura har ta samu sauki" mika masa magungunanta yayi, yayi masa sallama ya fita, Sai da ya isa kofar fita sannan ya juya ya kalli Mahaifiyar Samantha ya ga kallonsa take yi, yace "Sae da safe Ma!" Wani kallo tayi masa ta mike fuu ta wuce sama, yayi murmushi ya fita, a bakin gate ya hadu da samantha, tana ganinsa ta koma baya da sauri, motarsa ya nufa ya tsaya ya rungume hannayensa yana kallonta har xata shiga gate sai kuma ta tsaya ta d'an saci kallonsa taga idonsa na kanta, kamar mai counting step ta nufi inda yake ta tsaya nesa da shi, tace "Good evening!" Yace "Da wucewa xa kiyi?" Kallonsa tayi suka hada ido tayi murmushi ta girgixa kai, ya lumshe ido yace "Come here" tace "Ba gani ba?" Ya harareta ya nuna mata gabansa, kamar xata yi kuka tace "Kaga daga church fa nake, am tired!

Am feeling dizzy" Yace "To tafi...." Shiru tayi tana kallonsa, can ta karaso gabansa a hankali tace "Gani" dago kanta yayi yana kallon kwayar idonta yace "Me yasa kika fita baki da lafiya?" Ta sauke idonta tace "I went to church, Mumy tace in je" Wani kallo yayi mata yace "To daga yau kar ki sake xuwa har sai kin samu lafiya...." Ta xaro ido, ya gyada kai yace "yes I mean it...." Tace "to ae addu'a ake min a can ma" ya tabe baki yace "Good sai kiyi ta xuwa...." Kallonsa ta tsaya yi, ya juya ya bude motarsa ya shiga ya tada, ta lumshe ido ta bude tace "Ohk ohk, baxan je ba kuma" hararanta yayi, tayi kamar xata yi kuka tace "I mean it baxan je ba...." Yace "Better!

Taho ki ji" karasawa tayi kusa da glass din motar tace "Mene?" Yace "Matso mana" matsowa tayi, dai dai kunnenta yace "Drugs dinki da prescription na gun Abba, you make sure you take all before going to bed, since you ran away yesterday....." Bata jira ya karasa ba ta juya da sauri don gaba daya ta mance da incident din jiya, ya rikota da sauri ya jawota yayi planting mata kiss a cute lips dinta, ta kwace kanta da gudu ta shiga gida.

Ranan litinin Samantha ta kare exams dinta na Waec, karfe uku driver ya je dauko ta a sch, kamar ko da yaushe a bakin layi ya ajiyeta ta karasa wai xai je kasuwa Mumy ta aikesa, tana isa dai dai gidansu Abuturrab ta ga motarsa a waje, ta tsaya tana kallon gate din ko me ta tuna kuma ta fasa shiga xata wuce aka bude gate, sai ga shi ya fito, wara ido yayi ganinta yace "Ina kuma xa ki?" Tace "Wucewa nake yi ai" yace "Uhm, i see yaushe xa ku gama waec din?" Tace "Mun gama" yace "Waow da gaske baby, but shine baki fada min ba?" Ta langwabar da kai tace "Gashi na gaya ma!" Yace "Alryt...

Plss ki xo anjima da yamma i have a surprise for you, yanxu xan tafi gun aiki ne i forgot my office key...." Tace "Baxa a bar ni in fito ba...." Xai yi magana aka bude gate sai ga Mami ta fito, gaba daya ya mance tace xai ajiyeta a hanya, kallo daya Mami tayi ma Samantha tace "Aliyu da ban fito ba wucewar ka xaka yi knn?" Ya shafa kai yace "Ohh Mami wllh mancewa nayi...." Samantha da ko ba a gaya mata ba ta gane mum dinsa ce ganin kamar da suka yi da Hajiya Mariya ta risina tace "Ina kwana..." Mami ta kalleta murmushi dauke fuskarta tace "Lafiya lau yan mata ya makaranta" murmushi kawai samantha tayi kanta a kasa tace "Sai anjima...." Daga haka ta juya ta wuce, Mami ta bude bayan mota ta shiga Abuturrab ya shiga motar shi ma ya tada, sai da yayi reverse Mami tace "Ina ka samo wnn kuma?" Ta madubi ya kalleta yace "A anguwar take, she's....

A frnd!" Mami tace "Amma ba musulma bace?" Shiru yayi na kusan minti hudu, cikin sanyin murya yace "Me kika ga Mami?" Mami dake danna waya tace "Me na gani a ina?" Yace "Da kika ce ba musulma bace" Mami da har ta mance xancen da suke tace "Ae musulinci ba boyayyen addini bne, duk inda kaga musulmi xaka gane....." Yace "But Mami uniform ne fa jikinta with Beret!" Tace "So?
Chapter 26 · 0% Book details