← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 123

Sashe 38

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Burabisko da miyar taushe da k'ashi Hansae tayi ta ajiye masu cikin langar tuwo da miya, Baffa dake xaune da yar radio a hannunsa yace "Bayin Allah da alama sun wahala, a dajin ma suka kwana" ana kiran Azahar Baffa ya tada Abuturrab yayi sllh, Hansae tace "Tafi ki tada ta ita ma tayi wanka tayi sllh" binta ta shiga ta tada Samantha tace "Ki tashi kiyi wanka sai kiyi sllh, Azahar yayi" Samantha ta mike xaune tana mitsika ido, can ta mike ta cire kayan jikinta ta daura xanin, ta kalli binta tace "ki ban mayafi don Allah" Binta ta nemo mata wani dankwali ta bata tace "Mu je in raka ki kewayen na kai maki ruwa" Abuturrab na xaune a tabarma tare da Alto yana shan fura da nonon da Hansai ta dama masu Samantha ta fito da Binta, kallonta ya dinga yi ita ko kallo daya tayi masa ta dauke kai Binta ta rakata har bayin snn ta dawo, Samantha na fitowa daga wankan Hansai tace "Ga buta can ki dauka kiyi alwala" shiru Samantha tayi bata ce komai ba, can ta kalli Abuturrab da idonsa ke kanta, ta girgixa kai a hankali tace "Bana yi" daga haka ta shige Bukkar Binta, wata yar top da xani binta ta bata ta sa, tana gama shiryawa binta tace "Ki fito ku ci abinci wae ke yake jira" Samantha ta mike suka fita a tare, Alto ya mike yace ta taho ta xauna, ta karasa ta xauna kan tabarmar, Fura Abuturrab ya mika mata ta karba ta ajiye, bata bari sun hada ido ba duk da irin kallon da yake mata, shi ya fara sa hannu cikin langar dake dauke da Burabisko da miya yayi bismilla ya fara ci, kasa sakewa Samantha tayi taki cin abincin sai fura da take sha a hankali Hansai tace "Ko xa ku shiga daga ciki naga kamar a takure take" Kamar Abuturrab jira yake yace "Toh" Hansai tace "Binta kai masu abincin daki" Binta ta je ta dau abincin ta shiga da shi bukkarta, Abuturrab ya mike yana kallon Samantha ita ma ta mike ta bi bayansa suka shiga Bukkar, suna shiga ya nuna mata kusa da shi ta xauna, ya dau cup din furan ya mika mata ta sa hannu ta karba yace "Finish it immediately ki ban cup din" ta yi d'an murmushi ta kai baki, kadan ta sha tace "Na koshi" ya hade rai yace "Sae fa kin shanye" girgixa kai tayi ya k
wace cup din hannunta ya matso kusa da ita ya rike kan ta ya kai cup din bakinta, bbu yanda ta iya haka ta dinga sha kamar xata yi kuka, sae da ya ga ya wuce rabi snn ya ajiye ya ce "oya sa hannu" lekan abinci tayi tace "What's that" Hannu yasa ya deba ya kai bakinta, ta bude bakin a hankali ya xuba mata, da kyar ta dinga taunawa tana kallonsa kmr me taunar magani, ya dake bai bari yayi dariyar dake cin sa ba, tana hadiyewa tace "Baxan iya ci ba Dr " Ya girgixa kai yace "No, but da dadi fah, there's no other food than this!" Ta fashe da kuka tace "Baxan iya ci ba..." Shiru yayi yana kallonta, can ya kamo hannunta cike da tausayi yace "Toh me xa ki ci" cikin rawar murya tace "Rice!"
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
30.....

Shiru yayi ya rasa abinda xai ce mata, can ya sa hannu cikin aljihinsa yaga har lkcn kudin da yayi withdraw na nan, ya rufe burabiskon ya mike yace "To taso mu je" a hankali ta mike ta bi bayansa suka fita, yana kallon Hansai da Alto da yare yace "Baffa xa mu d'an xaga rigar nn...." Alto tace "Toh har kun cinye abincin ne?" Yace "A'a idan mun dawo xa mu ci, furan ya ishe mu" Alto tace "Toh bari Binta ta xaga da ku, sai dai fa ba wani girma ne da kauyan namu ba" tana dariya ta kare maganar shi ma yayi dariya yace "Ni kuma hakan ya burgeni sosai babu hayaniya" Alto ya kwalo ma Binta kira ta fito yace tayi masu jagora xa su xagaye Rigar garki, tace "Toh" snn ta koma ciki, dama shigar fulani tayi dogon gashinta da ke kai wa har kusan gadon bayanta an tufke mata shi gida uku, ta dau sandar kiwonsu tana kallonsu Abuturrab da fillanci tace "Mu je" Samantha dai ko kallonta bata yi ba har suka fita, tana tsakiyarsu suke tafiyar ko wani Bukka suka wuce sai ta fadi masu na wanene duk da fillanci, kai kawai Abuturrab ke kada mata, can ta kalli samantha da yaren tace "Ke bakya magana, ya sunan ki" Samantha bata ce komai ba, Abuturrab yace "Sunanta Fatima amma ana kiranta da Samha" kallonsa Samantha tayi ya wara mata ido, Binta tace "Lah ashe sunan mu daya, to me yasa kanwar taka bata magana?" Ya buda hannu yace "Haka take" tace "To kai ya sunanka?" Yace "Aliyu" ta xaro ido "Suna mai girma" Hira Binta ta dinga masa tun yana amsa mata da uhm da eh da A'a har dai ya fara magana, Samantha dai tafiyarta kawai take bata ko kallesu ba, Binta tace "Ina son wataran ni ma inje birni" kamar xata yi kuka ta kare maganar, yayi yar dariya yace "Kar ki damu xamu xo mu dauke ki wataran..." Tace "To a ina xan xauna ni da ban san kowa a birni ba" Yace "Gidanmu mana" tayi murmushi tace "Allah yasa kar ku mance da ni" yana murmushin shi ma yace "In'sha Allah" kallon Samantha yayi da fillanci yace "Are you okay?" Bata ce komai ba bata kuma kallesa ba, tsayawa yayi yana kallonta Binta ma ta tsaya, ita ko ta ci gaba da tafiyarta, ya jawota da damuwa yace "Samha tell me what's wrong?" Ta mayar masa da fillanci tace "Just want to be left alone" shiru yayi yana kallonta, ta kwace hannunta ta ci gaba da tafiya, Binta ta kallesa a hankali tace "Kilan so take ku je gun Ammin ku" Murmushi ya k'irkira bai ce komai ba suka ci gaba da tafiya, can ya kalli Binta yace "Akwai inda ake sai da abubuwan ci a Rigar nan" tace "Ehh mana akwae yar kasuwa, ana tsayar da warar fulani, hura da nono, gyada kai har da nama da...." Ya katse ta yace "Shinkafa fah?" Ta ce "Akwai mana" yace "Toh muje xan siya mata shinkafa xata ci" Binta ta kalli Samantha da tayi gaba can tana tafiya tace "Bata cin Burabisko?" Kai kawai ya gyada mata, ya karasa da sauri gun Samantha ya kamo hannunta da turanci yace "What's all this dear?" Bata ce komai ba, ya ci gaba yace "Did i offend you in anyway" Binta dake kallonsu ta gefen ido ta ci gaba da tafiya, ganin baxa ta kulasa ba ya ci gaba da tafiya yana rike da hannunta, shinkafar dari uku ya siya da wani miya da ke basa kyankyani, ita kanta Samantha da ganin yanda take kallon abincin kasan bbu yanda ta iya ne, suna gama siya yace su koma gida, wnn karan su biyu ya bari suka yi gaba yana biye da su a baya.

Har suka isa gida bbu wanda yace komai cikinsu, Su Alto suka yi masu sannu da xuwa, ba laifi Samantha ta ci shinkafar sbda yunwar da take ji, ya tallabi cin dinsa yana kallonta har tace ta koshi, yayi murmushi yana gyada mata kai, murya can kasa yace "Kinsan me love?" Kallonsa tayi bata ce komai ba, a hankali yace "Idan ance ki tashi kiyi sllh ki dinga cewa toh" ta kafe sa da manyan idonta, can tace "Ban gane ba" ya lumshe ido ya bude cikin sanyin murya yace "I mean idan aka ce maki ga ruwan alwala ki ce to, ki dauka...." Wani kallo take masa tace "In yi me?" Yace "Kiyi alwalan ko baki iya ba!" Da mamaki ta dinga kallonsa, can ta girgixa kai tace "No!" Shiru yayi yana kallonta, can yace "Let me ask you, what's Good about Christianity?" Ta wani hade rai tace "What's Good about Islam?" Kamar jira yake yace "A lot, it's a religion of peace....

The true religion, Christianity is not a religion, it's just a way of life....

Ki bani inda aka ambaci Christianity a bible nima kuma xan baki inda aka ambaci Islam a bible...." Wani kallo ta dinga yi masa ya gigixa kai yace "If you know ur bible too well John 14;27 Jesus said 'Peace i leave with you, My peace i give to you, not as the world gives, and do not allow ur heart to trouble you' here Jesus made mentioned of the religion he practiced and let to his disciples (Followers) as (Shalom) and did you know the meaning of Shalom?" Har lkcn kallon tara saura qtr take masa, ya matso kusa da ita ya d'ago kanta yana kallon kwayar idonta yace "In kinsan Bible din ki sosai sanin ma'anar shalom baxai maki wahala ba...

Ashe kawae ke 'yar muna Christian ce" kwace fuskarta tayi tace "Shalom means Peace!" Murmushin da ya baiyyana dimples dinsa yayi yana kallonta yace "Good, And that's the meaning of Islam (peace!), Jesus ya gargadi mabiyansa (disciples) kan cewar kada su bi son xuciya, kada su bi ra'ayinsu, but unfortunately they all followed their heart desire and got their selves the name Christianity, a name not found in the bible, a name gotten from Paul the apostle, paul shine yayi naming dinsa Christianity for his selfish interest domin a da ai ba masoyin Jesus bane Paul, true or false?
Chapter 38 · 0% Book details