← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 123

Sashe 96

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A yau litinin Samha ta xamo daya daga cikinmu bayan an yi duk abinda musulunci ya tanadar kafin yin hakan, wato dai ta amshi kalmar shahada, yanda Umma tayi farin ciki a wannan rana sai ka rantse ta hada abu da ita ne, shi kansa mai gidan ta Alhaji Ibrahim da abokansa biyu sai yaransa maxa gaba daya sun yi farin ciki da lamarin suka kuma yi mata fatan alkhairi suka kuma yi mata addu'ar Allah yasa ta dauwama a islam, shawarwarin da ya kamata suka bata suka kuma yi mata nuni da sai ta kauda kai a duk abinda xata gani gun yan uwanta nan gaba, sauran kuma suka bar ma Hajiya Halima, nan ita ma ta bata nata shawarar, sun jima sosai a parlon da umma bayan barin su maigidanta, ita dai Samha na xaune kanta a kasa, har lkcn ta rasa dalilin kukan da take, Umma tace "Bana son kukan nan daughter, ain't you happy?" Tana share hawayenta a hankali tace "I am" Umma tace "Good, kar ki sake xubda hawayenki, Allahu na tare da ke, kuma shine gatan ki xai kuma ji6anci duk al'amuran ki" kai Samha ta gyada mata, Umma tace "Kina da sunan da kike son a dinga kiran ki da shi ne?" Kallonta Samha tayi sai kuma ta girgixa kai, Umma tayi murmushi tace "Alryt we will call you *Noor* meaning *Light* kina so?" Murmushi Samha tayi a hankali tace "Toh Umma" tace "Kina xuwa Antenatal ne a can gombe?" Kai ta gyada mata ba tare da ta dago ba, Umma tace "Alryt, tafi ki je ki huta, koh gobe sai Maryam ta raka ki asibiti" Mikewa tayi tace "Nagode Mum" daga haka ta wuce daki, a bedroom Umma ta xaunar da yaranta gaba daya da surkanta biyu ta fadi masu matsayin Samha ta kuma basu takaitattacen labarin da Samha ta bata jiya, duk sun ji tausayinta sosai, nan Umma tace "Ke Sumayya tunda kina gida always sai ki dinga lura da ita kina putting din ta through, tun daga kan alwalarta da sallah, kiyi kkrin dinga nuna mata do's nd don't's din islam, snn kiyi kkrin dinga koya mata addu'o'i, har ma da karatun qur'an, i notice she's not totally an illiterate in islam, kema sai ki samu lada gun Allah in kika yi xuciyar ki daya" Sumayya tace "Toh Umma" Umma ta kalli Maryam da Rukayya tace "Ku kuma ta fannin auratayya nake son kuyi putting dinta through" su ma suka amsa, nan tace ma 'ya yan nata duk Noor xa su dinga kiranta da.

A hankali Abuturrab ya bude idonsa ya saukar saman dakin, sosai yake jin nauyin idanuwan nasa, kare ma inda yake kwance kallo ya shiga yi a hankali yaga bedroom din kamar na Abbansa, idonsa ya sauka kan alluran dake vein dinsa, kallon ledan ruwan yyi lkci daya ya mike xaune xai tuge yaji muryar Abbansa, "Don't you try that!" Juyawa yyi da sauri suka hada ido, lkci daya abubuwa suka dinga dawo masa, rike kansa yyi jin wani tukukin da xuciyarsa ke yi yace "Nooo" Abba ya karaso da sauri yyi gripping shoulders dinsa yace "Are you okay" ya daura kansa jikin Abbansa cikin rawan murya yace "She's gone Abba...." Mami ce ta shigo dakin tare da Hajiya Mariya jin muryarsa, Hajiya Mariya ta karasa da sauri ta dago sa tace "Aliyu...." Bude ido yyi yana ganinta ya rungumeta cikin raunin murya yace "Mum don Allah don annabi kice mata ta dawo" da damuwa Hajiya Mariya tace "Then ka nutsu tukun son, ba fa inda ta je tana gida dama...." Saketa yyi da sauri yace "Da gaske Mum" bai jira cewarta ba ya yunkura xai mike tsaye tana kkrin mayar da shi amma tuni ya tashi, wani mugun bugu xuciyarsa yyi, ya dafa gun da hannu biyu, Mami ta rude tace "Innalillahi, Col ka kira likitan don Allah" tare suka yi kasa da Hajiya Mariya don kasa tsaye yyi, Strictly Abba yace "If anything shud happen to my son.....

Wllh duk sai kunyi mamaki na, i will make sure you two pay for this, yanda ku ka munafurce ni ku ka boyesa da yarinyar for all this while haka xaku nemota ku kawo masa ita ynzu idan ba haka ba......" A tsawace yace "kowa ma sai ciwon xuciya ya kamasa" Wani harara Mariya ta watsa masa ta gefen ido a fusace tace "Don Allah mu wuce asibiti yaya, ki kira masu gadi su taimaka mana a sa shi a mota" fita Mami tayi tana hawaye taje kiran soldiers din waje.

Suna xaune a ward din da aka basu su kadai, Ramlah na xaune kusa da shi sai hawaye take haka ma Khaleesat, Ilham kam na gefen Mami ita ma kukan take, Mami dai ta xuba uban tagumi idonta a kansa ganin mugun ramar da yyi, bacci yake amma da gani kasan na dole ne, hawaye ne ya xubo idonta jin abinda likitocin suka gaya mata, Aliyunta da ciwon xuciya kuma, wnn wace irin kaddara ce, sallamar Hajiya Mariya da Ummi ne ya katse mata tunaninta, suka shigo ward din Shariff na biye da su a baya, Mami ta d'an yi murmushi tace "Sannu da isowa Hajiya" Ummi dake ta kallon Aliyu ta karaso a sanyaye bakin gadon ta tsaya ta daura hannu forehead dinsa, Shariff ma tsaye yyi yana kallonsa, Mami tayi karfin halin cewa "Ina yinin mu Hajiya" Ummi ta kalleta, sai ta ji tausayinta har cikin ranta, ta kasa amsa gaisuwar, kujera ta samu ta xauna, ta rike kai, can ta dago ta kalli Hajiya Mariya dake tsaye ita ma, tace "Hajiya ina gidan iyayen yarinyar yake kika ce?" Hajiya Mariya tace "Anguwarsu daya da yaya ai" Tace "Toh ko mu je can" Ita dai Mami bata ce komai ba, Ummi ta tuna ai sun yi exchanging number da Anty Maryam, tace "Ai ina ma da number Aunt dinta ta kaduna, musulma ce ita, bari a kira ko can tayi" daga haka ta shiga kiran Anty Maryam, tana dagawa bayan sun gaisa Ummi ta rasa ynda xata yi tambayar, can dai tace "Maryam, tambayarki xanyi don Allah ko Samha taje gun ki?" Anty Maryam dake xaune sai da ta mike tsaye tace "Wajena kuma?" Ummi tace "Tun jiya ba mu ganta ba Maryam" Salati Anty Maryam ta saki tace "Ba a ganta ba kuma Hajiya??? nima ba ta xo nan ba wllh, meke faruwa ne" rasa abun cewa Ummi tayi can dai ta katse wayar.
Chapter 96 · 0% Book details