← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 123

Sashe 116

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zama irin ta masoya Abuturrab da Noor suka shiga yi, bai taba tunanin Noor xata ajiye komai ta fito masa da tsantsan so ba, ko kadan bata son bacin ransa kamar yanda shi ma bai son nata, bbu abinda ya sa ta kara samun kwanciyar hankali irin yanda Abbanta kan xo gidan nasu duk end of month ganin Arshaq da Ashraf da yanxu ke dosan shekara daya, yaran maa sha Allah bbu abinda suka mance na babansu, ga su da farin jini duk inda xa su sai an tanka su, ba don Hauwa dake gidan ba da ba xata iya rainon nasu ita kadai ba don matsalarsu na rigima yyi yawa, Mami kan xo lkci lkci ita ma ganin jikokin nata, wani lkcn kannin Abuturrab kan biyo ta har su kwana gidan amma fa sai ran da Col bai gari, Hajiya Mariya kam dama yaran har sun saba da ita ba a daukan lkci bata je gidan ba, su ma duk sati biyu ko uku su kan je su wuni a gidanta ran lahadi, duk ran Friday Abuturrab kan tura ma Mahaifinsa text din gaisuwa da barka da juma'ah bai taba fashin yin hakan ba, duk da shi ma bai taba masa reply ba, Anty Maryam ma taje gidan nasu sau daya amma bata kwana ba ta wuce, Abuturrab kan je gombe once in a while don gaida Ummi, Noor dai bata taba binsa ba sai dai su gaisa ta waya, Xumunci sosai suke yi da Umma don so tari ta kan je gaida su ta yini da su Arshaq, idan ma suka dade basu je ba, Ahmad kan je ganin takwararsa da matarsa Maryam dake kara koya ma Noor xamantakewar aure, har lkcn idan Noor ta tuna mahaifiyarta fushi take da ita hakan na hana mata walwala kusan kullum kuma sai tayi tunaninta, duk tsawon lkcn nn bata xauna haka ba sau daya Abuturrab yyi mata maganan islamiyya washegari kuma tasa ya kai ta, duk karfe goma take tafiya ta dawo karfe biyu, ita kuma Hauwa tayi rainon yara, ana haka har yaran suka cika shekara daya da watanni biyar nn kuma Hajiya Mariya ta xo ta daukesu tare da Hauwa don ita xata yaye su, duk sai Noor taji ba ddi, wanda hakan sai da ya sa mata xaxxabi, ganin ta ki dawowa normal har bayan sati biyu har abinci ma ta fara ignoring Abuturrab ya sa ta gaba don jin ko an taba ce mata xa a rabata da yaran ne, kasa ce mata komai yyi yana kallon kwayar idonta, lkci daya maganan Abbansa ya fado masa wanda hakan sai da yasa gabansa ya fadi, d'an murmushi ya kirkira yace "Ae shknn sai in je in samu mum in ce mata kince a karbo maki yaran ki" xaro ido tayi tace "Ni ai bn ce maka haka ba" yace "Toh me ke damun ki?" Ta bude masa hannu alamar bata sani ba, hancinta ya ja yace "Fadi gaskiya boys din ki kike tunani" bata ce masa komai ba ta koma tayi kwanciyarta, ya mike yace "On Saturday xa ta kawo su ae wife, ita ma xata je Malaysia ne" fita yyi dakin ya koma parlor ya xauna yyi shiru, can ya mike ya dau makullin mota ya koma dakinta yace mata yana xuwa snn ya fita, pharmacy ya nufa direct, ya siya injections da xai siya da drugs ya dawo gida, bacci ya sameta tana yi, ya kalli agogo ya xauna kusa da ita ya shiga tashinta, a hankali ta bude ido yace "Baki ci abinci ba har ynxu baby" ta girgixa kai tace "Am nt hungry" yace "No u re, tun safe tea kawai kika sha dear, gaya min me kike son ci?" Ta d'an yi shiru sai kuma tace "Tuwo xan ci" yace "Toh bari in siyo maki a eatry" daga haka ya mike ya fita, tuwo da miyar vegetable ya siyo mata yana xuba mata a plate ta sakko kasa, a hankali ta kauda kai, yace "What?" Da kyar tace "I think i want to throw up, ka rufe abincin, it's..." Rufe fuskar tayi gaba daya, ba musu ya dauke abincin ya rufe ya ajiye gefe yace "Toh me xa ki ci" ta mike xata koma kan gado tace "I told you am nt hungry" yace "Noo kin ga akwai xaxxabi jikin ki ki ci ko kadan ne sai in baki magani" tace "Baxan iya ci ba" yace "In kawo maki shayi?" Gyada masa kai tayi ya fita ya hado mata shayin, kadan ya lallabata ta sha snn ya dauko maganin da har ya ballar mata da cup din ruwa ya mika mata ta amsa ta sha, yace "Saura allura" da sauri tace "Bana so" yace "Guda daya fa dear" da kyar ta amince yyi mata alluran snn ta kwanta ya kwashi take away din tuwo da cups ya fita xuwa kitchen, yana fita bacci ya dauketa, a gida yyi la'asar don bai son barin ta ita kadai, karfe biyar saura ya rufe laptop din gabansa ya mike ya wuce dakinta, ganin bai ganta kwance ba ya kalli kofar bathroom dake a bude, ya karasa ciki da sauri, durkushe ya ganta a bathroom din cikin jini, ya dagota yace "Subhanallah what happened, me ya faru, kin ji ciwo ne" a rude yake tambayar ganin kallon da take masa sai da ya sha jinin jikinsa ya kasa cewa komai kuma, a hankali ta mike tsaye ta cire kayan jikinta, Yana tsaye ya kasa cewa komai har ta gama kintsa kanta ta fice bayin, sai a snn ya juya shima ya fita kwance ya ganta kan gado ya karasa a hankali yace "Sannu wife, u were bleeding....." Lumshe ido tayi bata ce komai, pain reliever ya dauko mata yace "Tashi ki karbi magani ki sha pls" bude ido tayi ya duka kusa da ita yace "Pls wife" mikewa xaune tayi ta karbi maganin ta sha, yace "Ina ke maki ciwo" kasan cikinta ta nuna masa yace "Allah xai sauwake kin ji" komawa tayi ta kwanta ya mike ya fita, duk jikinsa yyi sanyi, but he have no other alternative.

Kafin kwana biyu Noor ta warware kamar ba ita ba, a ranan Asabar Hajiya Mariya ta dawo mata da boys dinta, har ranta tayi murnan ganinsu amma bata nuna ba, Sai da Hajiya Mariya xata tafi ta tambayeta Anty Hawwa fa, Hajiya Mariya tace "Taje garin su amma sati biyu xata yi ta dawo" Noor tace "Allah ya dawo da ita lafiya" Abuturrab ne ya maida small mum din tasa gida.

Haka nn rayuwarsu ya ci gaba da kasancewa gwanin sha'awa, he was very careful kar Noor ta kara conceiving, Har Ashraf da Arshaq suka cika shekara biyu da rabi, a nan ya sa su a isla
mic schl mai hade da boko, sai a snn Noor tasan ashe Abuturrab ba baya ba a fannin addini kawai ya fi fito da boko fili ne, during weekend gaba daya lkcnsa na gun yaransa yana coaching din su don bai son su yi lacking komai na bangaren addini ynda baxai ji fargaban duk inda xa su shiga ba ko ba ynxu ba, don yasan baxai taba rabasu da dangin mahaifiyarsu ba, mugun tsoronsa yaran suke sbda strictness dinsa ita kuma a lkcn tana shirin fara Diploma a fannin Islamic studies, idan Noor na rera maka karatun qur'an ko tana karanto ma litattafen addini baka taba cewa she was once a Christian, hakan yasa Abuturrab ke alfahari da ita, a cikin kankanin lkci Arshaq da Ashraf suka fara larabci a shekararsu ta biyu a makarantar ga hadda dake kansu, Abbansu ya daina masu Hausa gaba daya sai dai Noor, in dai xai yi communicate da su sai dai Larabci ko Turanci, Mahaifin Noor ya maida gidansu wajen frequent xuwansa sbda jikokin nasa dake mugun sonsa shi ma kuma yake ji da su, ba don kowa yake xuwa gidan ba sai don su, yau ma kamar ko wace Friday Mr David ya xo gidan da yamma rike da chocolates dinsu, yan biyun na xaune gun da Abbansu ya tanadar masu don studies ko wannensu da qur'an a hannu, Noor kuma na kitchen tana girki, duk suka taso gaida kakan nasu, ya zauna kujera yana kallonsu ganin mood dinsu yace "What happen to my boys" Ashraf dai yyi shiru, Arshaq da har idonsa ya kawo ruwa yace "Abbu promise to cane us today" Noor ta fito kitchen ta gaida Abban nata tana murmushi, ya amsa ya maida hankalinsa kan yaran yace "Wht have you 2 done wrong" Ashraf ya juya yana kallon Ummun sa, Mr David ya kalleta yace "Me suka yi" yar dariya tayi tace "Abba k'arin hadda yyi masu tun jiya dan yana nyt duty sai suka ki yi, to yace idan ya dawo daga masallaci xasu bada haddan shine fa ka gansu haka" yace "Toh ke me yasa baxa ki masu ba" tace "Abba basa ji, kallonsu ya fara yawa kwanan nn" da turanci Arshaq yace "Grandpa ai kai ma ka iya ka yi mana" daga haka ya tafi ya dauko qur'an din yana mika masa, shiru Mr David yyi yana kallonsu bai kuma karbi Al-qur'an din ba, Ashraf yace "Pls grandpa, assist us" a hankali Noor ta juya ta koma kitchen, yaran biyu suka kuma hada baki gun cewa "Plss grandpa..."
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
102.....
Chapter 116 · 0% Book details