← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 123

Sashe 100

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bayan minti goma aka fito ma da su, Umma ta karbi daya, Maryam dake ta murmushi ta karbe dayan dake ta ihu, Kallon yaran Umma ke tayi ganin girmansu, ita kuwa Maryam tana ganin yaran tasan lallai mahaifinsu ma ba baya ba wajen kyau, tun da aka fito da Noor take baccin wahala, Su Abba da yaransa maza dama tuni suka koma gida ganin ta sauka lafiya har sun ga yaran, Sumayya da Sadiya suka taho asibitin da kayan shayi sai kallon fararen yaran Sumayya take, ta kalli Sadiya tace "They r so cute kamar larabawa sis" Sadiya tayi murmushi tace "Wllh kuwa" sai bayan isha Noor ta farka nan da nan Umma ta hada mata shayi ta bata, da kyar ta dinga shan shayin har ta shanye, Umma tace "Sannu Noor, baki tambayi yaran ki" sunkuyar da kai tayi bata ce komai ba, Anty Maryam tayi murmushi ta dauki yaron dake kwance a gadon yara, farida ma ta dauko dayan suka nufota, gaba daya yaran suka ajiye mata a jiki, kallonsu kawai Noor take ganin su wasu kanana don bata saba ganin jarirai ba, banda dogon hancinta da ya fi na babansu bbu abinda suka dauko nata, sak Aliyu kamanninsu har hasken, irinsu kuma ake kira da identical Twins tsabar basu da bambanci, Farida ta nuna mata dayan da aka sa ma xare a hannu tace "Kinga Hassan ga Hussaini" bata san lkcn da murmushi yyi escaping lips dinta ba sae dai kuma ta kasa daukan yaran sbda kunyar Umma duk da ba ma iya daukansu xata yi ba, Umma tayi dariya tace "Amma gaskiya basu yi kama da ke ba sai dai Aliyu" rufe fuskarta tayi, Maryam tayi dariya haka ma farida, Sadiya tace "Xan so in ga Aliyun nn ni kam" Noor bata iya ta bude fuskarta ba sbda kunya, Umma tace "Toh kin dai san gidansu Aliyu a nan kanon koh?" Shiru Noor tayi bata ce komai ba, Umma tayi murmushi tace "Kya ma bude baki yarinya" A nan asibitin Umma tayi ma yaran wanka tunda kwana xa su yi, da kanta ta kai Noor bayi ta taimaka mata ta dauraye jikinta da ruwan xafi kafin su je gida.

Washegari misalin tara aka sallamesu, suna isa gida wanka mai lafiya tayi ma Noor snn tayi ma jariran da suka cika gidan da ihu don tun jiya bbu abinda aka bari aka basu a asibitin sai ynxu da suka dawo gida, Noor na xaune tana kallon ynda Umma ke shiryasu, gani take kmr da an taba su xa su iya karyewa, nan ko su Umma ganin girman yaran suke sosai, da yake ita bata saba ganin jarirai ba bata san girmansu da rashinsa ba.

Umma na gama shiryasu sai ga Abba ya shigo nan ya kuma yi ma Noor da ta kasa dago kanta barka, ya dau yaran gaba daya yayi masu addu'a snn ya fita, Ahmad da su Usman ma suka shigo suka mata barka suka ma yaran addu'a su ma suka fita, Anty Maryam ce ta shigo da warmer din pepper soup na kayan ciki ta ajiye dakin tana cewa "Sannu mai jego" murmushi kawai Noor tayi, Umma ta dau hassan ta daura ma Noor a kan kafa ganin da gaske bata iya daukan jariri ba dan tun a asibiti bbu wanda ta dauka sai dai tayi ta kallonsu, Umma tace "Toh fito da maman in ga ko xai karba" Noor ta kasa yin abinda Umma tace sbda kunya, Maryam ta bude mata zip din rigar jikinta, da kyar ta yrda tayi hakan don kunya take ji, ita tunda take ko Mumynta bata yrda ta ga tsaraicinta da girmanta ba banda Abban twins dinta sai Umma ynxu, Umma na xaune kusa da ita har ta ga babyn ya fara shan abincin snn tayi murmushi tace "You now feel the joy of Motherhood dear, Allah ya raya maki su a bisa tafarkin Islam" Noor bata iya ta dago kanta ba, bayan minti uku Umma tasa ta mayar da shi daya side din, sai da ta tabbatar abincin ya isa babyn snn ta dau d'an uwansa shi ma tasa ta bashi, bayan ta gama da babies din ta kwantar da su gefe, da kanta ta xuba mata naman kayan ciki da Maryam ta kawo mata ta dauka ta bata, tana gama ci ta sha magungunanta da aka bata a asibiti snn ta kwanta.

Da yamma misalin biyar Ahmad ya shigo dakin tare da Maryam, bayan sun gaisa ya dau Hassan yana kallon Hussain yace "They re really identical, in ji an banbance maku su a asibiti" Umma tace "Hassan din ne a hannunka" yace "Maa sha Allah" kallon Noor yyi yace "Maman biyu bani number mai gidan ki" shiru tayi tana kallonsa, can a hankali tace "Bani da Number sa" Umma tace "Baki da numbersa kuma Noor, you've punished him a lot dear nasan duk inda yake yanxu baya da kwanciyar hankali" kamar xata yi kuka tace "Umma wllh bani da numbersa da gaske" Ahmad yace "Toh kin san gidansu ai koh?" A hankali ta gyada kai, yace "Toh bani address" bata ce komai ba har sae da Maryam tace "Ki bada Noor" kallon Umma tayi tace "Xan rubuta a takarda" aka dauko mata takarda da pen ta rubuta ta mika ma Maryam ta karba ta ba mai gidanta, babyn hannunsa ya kwantar yace "Ya sunan mai gidan naki?" Noor ta sunkuyar da kai tace "Doctor Aliyu" Umma tace "Oh likita ne" Noor tace "Uhm" Ahmad yace "Alryt to, bari in je" sallama yyi masu ya fita.
Chapter 100 · 0% Book details