← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 123

Sashe 21

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mary wacce kuke kira da Maryam ita ce mahaifiyarsa, Mary macece baiwar Allah me kamun kai kowa a Bethlehem ya shaida hakan, tana kuma da wanda xata aura wato Joseph wanda ya kasance Carpenter, ranan tana xaune ita kadai daki sai ta ga wani haske daga waje, haske sosai wanda sai da ta rufe idanuwanta, Mala'ika Gabriel kenan ya xo mata da sakon cewar xata haihu ba tare da aure ba, abun ya bata mamaki sosai, kafin tace komai har ya bace nan ta fara naxari sai dai bata fadi ma kowa ba har Joseph da xata aura, wasa wasa taga da gaske ciki gareta, wanda hakan yasa 'yan gari suka fara maganganu kanta, ko ina gulmarta ake wasu na cewa da ma lullubin karya take a ko da yaushe, tayi kkrin ganar da su cewar ita bata taba sanin namiji ba amma nobody was willing to believe her, sae Joseph da bai gujeta ba, bayan an dau lkci xaman kasar ya gagaresu sbda mutane wanda hakan yasa Joseph yasa su bar garin, a hanya nakuda ya kamata Joseph ya shigar da ita gun ajiye dawakai wato horse stable a nan ta haifi Jesus Christ the son of God!" Abuturrab dake ta kallonta cike da tausayi ya dakatar da ita da sauri jin furucin ta na karshe yace "Madam He's not the son of God but rather his messenger" kallonsa ta tsaya yi sae kuma tayi murmushi tace "Yeah, believe din Muslims knn, but we believe he's the son of God" hade rai yayi yace "Ina gaya maki magana kina ce min ba haka ba, Allah bai haifa ba ba a haifesa ba, h
e's one and one alone, Jesus is his messenger!" Shiru tayi tana kallonsa can ta girgixa kai tace "For God so love the world, that he gave his only begotten son that who so ever believeth in him shall not perish but have everlasting life, this is a verse from the holy bible don me xaka ce jesus isn't the son of God?" Wani kallo ya dinga mata can yace "Then ur bible is deceiving you" hade rai tayi sosai tace "How dare you? why will you say that?" Mikewa take son yi a fusace ya fixgota ya xaunar da ita yace "Luke 3:38 said; Adam was the son of God, Gen 6:2 also said all men are son of God, Jeremiah 31:9 said David is the begotten son of God, Psalm 2:7 said who ever ia righteous is the son of God, Romans 8:14 says Jesus is the ONLY begotten son of God, which are we to believe??

There is a lot of confusion in ur bible, nan ance mana Jesus kadae ne son of God, an dawo an lissafo mutane da dama an kirasu da son's of God su ma, why?

How's that???

Ashe kenan ba Jesus kadai ne son of God din ba ma," Kallonsa take ko kiftawa babu, ya tabe baki yace "Ci gaba" Sauke idonta tayi a hankali tace "Am going home" daga haka ta fara kokarin mikewa yace "Baki isa ba you are not leaving here until u finish ur forged story" wani kallo tayi masa sai kuma ta fashe da kuka tace "It's not forged" tabe baki yayi yace "Then ki ci gaba since you didn't defend my question" ta goge hawayen idonta a hankali tace "Three wise men ne suka yi announcing haihuwar Jesus the Messiah.....

Snn comet from the sky ne yayi leading dinsu har manger inda aka haifi Christ....." Dakatar da ita yyi yace "Yeah yeah... jump all this...." Cikin sanyin murya tace "Allah ya ba ma Christ baiwa da dama yana kuma da disciples 12 wato mabiya har sha biyu, first miracle din da jesus yayi on earth shine na tada matattace, Lazarus ya mutu yan uwansa na ta koke koke Jesus ya je tomb dinsa ya tado sa ya fara rayuwa kuma, ya warkar da mutane dayawa don ya kasance mutum me tausayi, akwai wani biki da suka je da mahaifiyarsa Mary, wine ya kare gun bikin, nan Mary ta nemosa tana tambayarsa ya xa ayi, nan yasa aka ciccika masa ruwa a pots ya maida su wine gaba daya, shine kadai mutum da ya taba tafiya a kan ruwa da kafafuwansa, ya taba ciyar da dubban mutane da bread guda biyar da kifi biyar yayi miracle suka cika baskets fiye da dari....

John the Baptist shi yyi baptizing Jesus....." Jin ana kiran sllh la'asar ya dakatar da ita yace "Alryt xan je sllh idan na dawo sae ki karasa, nima kuma sai in baki nawa tarihin islamically then you compare and contrast" a hankali tace "Ohk...." Rufe sauran abincin da ya rage yayi, tace "Ka koshi?" Bai tanka ta ba bai kuma kalleta ba, bayan yan mintuna ta mike xata wuce ya mayar da ita ya zaunar, hade rai tayi tace "Wucewa xan yi" bai ce komai ba kuma bai saketa ba, bayan wasu minutes din ya saketa yana kallonta yace "Idan ana kiran sllh ba a magana" buda ido tayi tace "da gaske?" Mikewa yayi yace "Yesss" mikewa tayi ita ma yace "Baxa ki jira in dawo ba kuma?" Hade rai tayi tace "Kai xaka sllh, ni kuma baxan je church ba, me yasa kai ma baka fasa xuwa sllhn ba" kallonta kawai yake, can ya juya yayi ficewarsa, kamar xata yi kuka ta bi sa da kallo, samun kanta tayi da kasa fita, a hankali ta koma ta xauna.

Sosai yayi mamakin ganinta da ya dawo daga masallaci amma bai nuna ba, ya xauna kusa da ita yace "Oya karasa in fara nawa!" Ta sauke idonta ta ci gaba da basa tarihin, tun daga kalubalen da jesus ya fara samu gun nonbelievers, da encounter dinsa da paul the apostle, da yanda paul ya dawo Christianity, irin sharrin da nonbelievers suka yi masa, da last dinner dinsa da disciples dinsa, da yanda soldiers suka xo suka yi arresting dinsa, aka saka masa crown din k'aya a kai, aka ja sa tare da cross dinsa xuwa Golgotha ana cin xarafinsa, da yanda aka saka shi tsakanin barayi biyu, yanda aka daura sa cross din aka buga masa kutsoshi a hannu kallonta Abuturrab yake da mamaki ganin hawaye idonta, ya danne dariyarsa yana kallonta da tausayin rashin sani wanda aka ce ya fi dare duhu, cikin sanyin murya tace "Jesus Wept!!!

And his last words where; Ohh father, forgive them because they don't know what they are doing!" and that was how jesus Christ died for our sins, he was crucified on the cross in Calvary, he was slain" ta karashe tana goge hawayen idonta, yana mata wani kallo yace "Ohh da gaske ya mutu ashe?

Kuma sbda xunuban mu? he died on the cross for all our sins?" Ta kallesa tace "Yess!

But he rose up after 3 dayz and his father took him to heaven...." Da mamaki yace "But....

But Why then do we still have to go to hell and pay for them again, don me wasun mu xa su je wuta bayan sbda xunuban mu ya mutu?

Wato sau biyu kenan xa ayi judge dinmu....

Toh sacrifice din da jesus yayi sbda xunuban mu bai isa ba knn har sae an sake mana hukunci?

Ina ce don xunuban mu ya yarda ya mutu, to in haka ne kenan he did not die for our sins tunda har hukunci pa na jiranmu ranan gobe kiyama, idan kuma ba haka ba ki fahimtar da ni yanda xan gane, kuma ni dai nasan it wasn't Jesus Pbuh that was Crucified or slain....

Another error from your Bible" yana kai wa nan ya wani hade rai wanda hakan yasa ta kasa cewa komai tana kallonsa ko kiftawa bbu, ya wara ido yace "Kinyi shiru?" Ta dauke kanta, ya kamo hannunta yace "Ki ganar da ni mana Samha" ta xame hannunta a hankali tace "I don't know too, all my Bible told me was that he died on the cross and rose from his tomb after 3 dayz and was taken to heaven bayan wannan ban san komai ba" innocently tayi maganan, murmushi yayi yace "Toh shknn, are you ready in fara baki nawa tarihin?" Bata ce komai ba ta sauke idonta kasa, ya lumshe ido yace "Alryt, His mother is Maryam Bint Imran, the daughter of Hannah......" Shiru yayi yana kallonta, ta d'ago a hankali jin shirun, murya can kasa tace "Ci gaba" yayi murmushi yace "Ohk...."
*Haske Writers asso*
Astaghfirullaahal Adheemal lathee la ilaaha illaa huwal hayyul qayyumu, wa atoobu ilayhi!!

Allah knows best.
*Noorul Huda*
17.....
Chapter 21 · 0% Book details