← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 123

Sashe 51

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa daurewa Fatima tayi misalin karfe tara Samha na daki tare da Khadija ta shiga bedroom din Ummi, xaune ta tadda Ummi idonta sanye da glass tana aiki gaban computer, ta karasa ta xauna tace "Ummi..." Ummi ta juya tana kallonta tace "Ya aka yi?" Tace "Uhm wai da gaske gobe yaya Yusuf din xai iso?" Ummi ta ci gaba da abinda take tace "Ki kirasa ki ji mana" Shiru tayi bata ce komai ba don ba tambayar da ya kawo ta knn ba, Can dai tayi karfin halin cewa "Ummi me Samha take yi a nn ne wai?" Juyawa Ummi ta kuma yi ta kalleta tace "How is her staying here affecting you?" Yake tayi tace "Noo, Ummi it's surprising ne ta bar mijinta ta xo nan, i tot bata da lafiya ne ma" Ummi tace "Toh ba matsalar ki ba ne..." Daga haka Ummi ta ci gaba da abinda take, Fatima ta mike ta fita daga dakin cike da jin haushin abinda ummi tayi mata.

Dakin yayanta ta shige tayi kwanciyarta.

Da asuba Ummi ta shigo tada khadija tayi sllh, ga mamakinta sai taga sun ma tashi suna sllhn, tsaye tayi bakin kofa tana kallon Samha, a xuciyarta tace "Ikon Allah, amma wnn ai aikin baban giwa take..." Tausayinta sosai taji a ranta ta kuma dau kudirin xata dau time ta tambayeta her view about islam, is she interested, but ga dukkan alamu ma she is interested tunda har ta iya tashi da asuba tayi sllh, juyawa Ummi tayi ta fita.

Abuturrab na idar da sllh part din Ummi ya taho don jin ko xae je airport din kuma, "Na kira wayarsa bai je ba, je kayi abinda xaka yi idan ma ya iso sai ya dau taxi kawai" cewar Ummi kenan bayan ta fito, yace "Toh Mami" daga haka ya juya ya bar wajen.

Xama Abuturrab yyi a parlor ya rike kai bayan ya koma part dinsa, he never taught hukuncin da Ummi xata dauka kenan, me yasa take kkrin nisanta shi da Samha, sae yaji duk xaman gomben ma ya ishesa, damuwa yyi masa yawa, what happened the day before yesterday was just a mistake, sharrin shaidan.

Ya rasa gane whether he is regretting telling her or not, gaba daya yaji bai jin xai ma iya ci gaba da xama garin.

Samha na xaune daki tana kallon khadija dake karatun qur'ani sai dai gaba daya hankalinta bai gun, gaba daya tunaninta na gun Abuturrab is she missing him or what, hawaye taji na neman taruwa idonta, why is all this happening to her in just 2 month, kwanciya tayi a hankali ta juya kanta hawaye na sakko mata.

A ranan Abuturrab na xaune office ya jinginar da kansa jikin kujera wayarsa dake gabansa ya fara ring, dauka yayi yaga Hajiya Mariya ce ke kiransa, ya lumshe ido ya daga kiran ya kai kunne, cikin sanyin murya yyi mata sallama ta amsa daga daya bangaren, ya gaisheta tace "Abuu ko kira baxaka dinga yi ba, ya kuke?" Yace "Lafiya lau mum, ya gida?" Tace "Alhmdllh, ina Samhar?" Yace "Tana gida mum" tace "Kai kana ina?" Yace "Ina gun aiki Mum" tace "Aiki kuma, da wani qualification din" yayi murmushi yace "Uhn da na kai na Mumy..." Tace "Toh a ina ka samu aikin..." Bayanin Hajiya Hajarah ya shiga yi mata, Hajiya Mariya tace "Allah sarki, Allah ya mata albarka...

Yanxu kuma Abuu haka xaka ci gaba da rayuwa da wacce ba muharramar ka ba..." Yace "Mumy i told Hajiya everything jiya da safe, shine ta dauki Samhar ta komar da ita nata bangaren i really can't tell what she is up to...." Hajiya Mariya tace "Maa sha Allah naji dadin hakan gaskiya, am happy akwai babba tare da ku da xata dinga gaya maku gaskiya tana nuna maku, what she did is the right thing...." Abuturrab yace "But Mum, kar ta raba ni da ita wlh mum baki ji yanda naji da ta mayar da ita bangaren ta ba..." Hajiya Mariya tace "Keep quiet, hakan shine dai dai, ta burge ni wllh...

Idan ma conversion din ne gwara ita tayi converting dinta" kasa ce mata komai Abuturrab yayi, tace "Yea, sai mun yi waya" daga haka ta katse wayar ya ajiye ya rike kansa.

Samha na kitchen tare da khadija da mai aikinsu misalin karfe biyar saura suka ji fatima dake parlor da wata Billy, wanda da alamar ita ta kirata ta xo tana cewa "Welcome big bro..." Khadija ta ajiye yankan salad din da take yi da sauri ta fice daga kitchen din tana cewa "Oyoyo yayana" tsaye Samha tayi bakin kofa tana kallon yayan nasu dake kkrin cire takalmin kafarsa ganin kanwartasa ya mike ya wara ido ya rungumeta yace "Oyoyo lil sis..." Kankamesa khadija tayi tace "I missed you broo..." Yace "I missed you too, ina Ummina" khadija tace "Bata dawo ba..." Yace "Rabi'a fah?" Tace "Tana gidan Abbu..." Sau daya ya kalli Samha da tayi saurin sunkuyar da kai ya amsa gaisuwar Billy ya wuce bedroom dinsa.

Bayan Magrib Samha na kwance daki khadija ta shigo tace "Sis Samha ki fito mu ci abinci..." Samha ta kalleta tace "Ae daxu na ci abinci..." Khadija tace "Dinner fa ba lunch ba" murmushi Samha tayi tace "Toh ni dai na koshi...." Khadija tace "Ummi fa ce tace in kira ki" mikewa Samha tayi ta bi bayanta suka fito parlor, Dai dai lkcn da Abuturrab ya shigo parlorn, kanta a sunkuye ta karaso parlon, shi kam idonsa na kanta har ya shigo, khadija ta gaishesa ya amsa har lkcn idonsa na kan Samha, Fatima kuma idonta na kansa kamar xata cinye sa, ya xauna yace "Ga ni Mami..." Ummi tace "Abinci xaka ci dama, Samha kun gaisa kuwa?" Sai a snn ta dago kai ta kallesa, sai kasa daina kallonsa tayi, can tayi karfin halin cewa "Ina yini..." Ya kasa amsawa, Ummi tace "Ba ku ma gaisa da Yusuf ba Boy" daga haka ta kwalo ma Yusuf kira, Khadija tace "Ae bai shigo daga masallaci ba..." Bata rufe baki ba Yusuf ya shigo parlon da sallama, Abuturrab ya juya ya kallesa, karasowa yyi parlon yace "Ummi am jet hungry...".

Ummi tace "Ga abinci can dinning ai, bayan tafiyar ka Allah ya hada ni da wani son wanda ya take ka a rashin ji ma, ka gansa yana nn yana ban wahala shi ma..." Sosai ta ba Abuturrab dariya, khadija ta fashe da dariya ita ma, Samha kam murmushi tayi ta sunkuyar da kai, Yusuf ya wara ido yana kallon Abuturrab yace "Really Ummi..." Daga haka ya mika masa hannu murmushi dauke fuskarsa suka gaisa yace "I am barrister Yusuf Ahmad...." Abuturrab ya mayar masa da murmushin yace "I am Dr Aliyu Ahmad...." Yusuf yace "It's nyc meeting you..." Kai Abuturrab ya gyada masa har lkcn murmushi fuskarsa yace "Same..." Ummi na kallon Samha tace "Kun gaisa da shi dota?" Sai a snn Samha ta kallesa shima ya juya yana kallonta, a hankali tace "Ina yini?"
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
43.....

Yusuf da ke kallonta shi ma yace "Lafiya lau...." Daga haka Ummi ta mike tace "Ga dinner can a dinning, fatima u serve it..." Mikewa Abuturrab ma yyi yace "Mami na taho da abinci fahh" kallonsa Ummi tayi tace "Toh ae bn ce ka taho da abinci ba, ga abinci can nace a dinning" Daga haka ta nufi dinning din ganin Fatima bata da niyyar mikewa, da kanta tayi ma kowa serving abincin ta juya tana kallonsu, Yusuf ne ya fara nufar dinning din fatima ta bi bayansa, ya ja kujera ya xauna, Khadija ta kalli Samha tace "Mu je..." Mikewa Samha tayi ta bi bayanta suka tafi, Khadija ta ja mata kujerar da ke kallon na Yusuf, ta xauna, snn ta xauna gefenta, Ummi na kallon Abuturrab da ya ki tahowa tace "Toh ko sai na dauko ka..." Murmushi yayi ya taho dinning din ba don ya so ba, ya ja kujerar dake gefen na Fatima a hankali ya xauna, can ya kalli Ummi yace "Ke baxa ki ci ba Mami..." Ummi tace "A'a ku dai ku ci My boy..." Daga haka ta wuce daki, Yusuf kam kansa na kasa yana cin abincin gabansa sai dai lkci lkci ya kan dago ya kalli Samha dake opposite dinsa, wanda hakan yasa duk ta takura ta kasa cin abincin, Abuturrab ya dago ya kalleta, ganin ba dagowa xata yi ba yasa ya sunkuyar da kai ya shiga cin abincin gabansa, fatima kuma sai satan kallonsa take, Kamar ance Abuturrab ya kalli Yusuf ya ga idonsa a kan Samha, ji yayi abincin na neman dawo masa ya mike da sauri hade da rufe baki kamar me shirin amai, Fatima ta mike ita ma da sauri tana kallonsa, Yusuf ya tashi shi ma da mamaki yace "What happened...." Abuturrab na girgixa kai yace "Am...

Am not okay, i need to throw up...." Daga haka ya juya da sauri ya bar dining din, Samha ta bi sa da ido, ae bata san lkcn da ta mike ta bi bayansa ba, Yusuf ya bi su da ido, can ya kalli Khadija yace "Who's she?" Khadija tace "His wife..." Shiru yyi yana kallonta ko kiftawa bbu, Samha na fita taga har ya kusa balcony, ta bi bayansa da sauri, nan bakin kofa ta gansa durkushe sai kkrin amai yake ya kasa, ji yyi gaba daya cikinsa ya hautsine amma ya kasa amai, ga wani mugun bugu da xuciyarsa ke yi, ta durkusa gabansa ta rikosa hankali tashe tace "Me ya faru doctor, baka son abincin ne, ni da khadija fa muka yi..." Bai iya ya ce komai ba, jin hannunsa a shoulder dinsa yasa shi fara jin saukin abinda yake ji, ganin ya fara nutsuwa yasa tayi shiru tana kallonsa, a hankali ya dago idonsa da yayi jajir yana kallonta, sauke idonta kasa tayi, sai ji tayi ya rungumeta, tayi lamo jikinsa tana jin bugun xuciyarsa, duk yanda ya so bude baki yayi mata magana kasawa yayi, lkci daya hawaye ya kawo idonsa, ta dago a hankali ganin haka sai ta fashe da kuka, cikin sanyin murya yace "I love you Samha, i will be nothing without you...
Chapter 51 · 0% Book details