← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 123

Sashe 8

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kwaso books din" mikewa tayi, tayi yanda yace ta ajiye su a kasa, ya sauko ya rage volume din Tv din, ya bude physics book din yana kallo, shafa beard dinsa yayi ya lumshe ido ya bude yace "Ohk, listen attentively" tace "Toh" a nutse ya shiga mata solving din questions din yana mata bayani, ya maimaita ya kai sau biyar har sai da tace ta gane, yayi forming questions uku ya bata tayi ta karba tana kallo, ya mayar da hankalinsa kan kallon da yake, tana gamawa ta kallesa tace "Am through" karba yyi yana dubawa, can ya gyada kai yace "Then do ur assignment now" tace "Toh" snn ta fara assignment din, ko da ta gama tare suke yi biology din har suka gama, ta kalli agogo taga goma ya kusa ta kallesa kafin tace komai yace "Lokaci ya riga ya wuce, just read ur note...." Xaro ido tayi tana kallonsa tace "Ohk to xan tafi gida" yace "Mum xata tambayeki why you came back early" shiru tayi bata ce komai ba, yace "So it's better ki jira time yyi sai ki wuce" ita dai bata ce komai ba, yyi kwanciyarsa kan 3 sitter ya canxa station, wani American film ake yi tayi tagumi ita ma tana kallon movie din, gajiya tayi ta bude essential bio dinta tana kallo, kmr ance ta dago kai ta kalli Tv abinda ta gani yasa ta kallesa da sauri, lumshe ya ga idonsa, bata kuma kallon Tvn ba ta mike da sauri tayi hanyar kitchen, plates din da suka yi breakfast ta shiga wankewa tana gamawa ta gyara kitchen din snn ta fito da sweeper da mop har lkcn rufe ta ga idonsa sai ta ga kamar bacci ma yake, gyaran parlon ta fara yi da yake bbu wani kura cikin few minutes ta gama gyaran ta mayar da komai inda yake ta dawo ta kalli agogo ta ga sha daya ya kusa, one sitter ta xauna ta canxa station xuwa Bollywood, bata yi minti goma tana kallon ba ta jinginar da kanta jikin kujera sai bacci, bude ido Abuturrab yayi ta dalilin wayarsa da ya ji yana ring a bedroom ya mike xaune yana kallonta ganin yanda ta takure kan kujeran tana bacci, mikewa yayi ya karasa kusa da ita ya durkusa, long lashes dinta kawai yake kallo ko kiftawa bbu can ya sauka idonsa kan dogon hancinta kafin d'an karamin bakinta, hannunsa ya daura kan fingers dinta ta bude ido da sauri, ya mike yace "You are not comfortable xo ki kwanta a can" xata yi magana ya kama hannunta ta mike ya nufi kan kujeran da ya tashi daga yasa ta kwanta snn ya wuce bedroom, missed call din Abokinsa Mujaheed ya gani ya shiga kiransa back, bugu uku Jaheed ya daga, daga daya bangaren yace "Ina ka shiga man?" Abuturrab yace "Was having a Nap at the parlor, ya aka yi?" Jaheed yace "Alryt gani tahowa....." Da sauri Abuturrab ya katse sa ta hanyar cewa "Yanxu fa xan fito office ku hadu a can" Jaheed yace "It's urgent....." Abuturrab ya kalli agogo yace "Ni na ma shirya fa, fitowa kawai xan yi" Jaheed ya d'an yi tsaki ya katse wayar, Tabe baki Abuturrab yayi xai shiga toilet ya ji ana danna bell, fitowa yayi da sauri, ga mamakinsa ko motsi Samantha bata yi ba, baccinta kawai take, kofa ya nufa a leka waje yaga Mami tsaye, xaro ido yyi ya juya da sauri ya isa gun Samantha tashinta ya shiga yi ta bude ido a hankali tana kallonsa, sai kuma ta mike xaune tana kalle kalle dai dai lkcn da Mami ta kuma danne bell tace "Abuu?" Mikewa Samantha tayi a tsorace tana kallonsa da kyar tace "Ur Mum?" Bai ce komai ba ya kama hannunta ya wuce bedroom dinsa da ita tana shiga ya rufe kofar snn ya fito ya koma gun Kofar ya bude, sai ka rantse daga bacci ya tashi yanda yyi da fuska, Mami tace "Bacci kake?" Gyada Kai kawai yayi, tace "Ohk sorry, ka xo ku gaisa da Yakumbo ta xo" shiru yyi yana kallonta sai kuma ya hade rai yace "Mami maimakon kice na fita aiki?" Mami tace "Go and freshen up ka fito ku gaisa nace, bana son magana" daga haka ta juya ta bar gun tana kallon karen dake cage abinsa, girgixa kai tayi tayi gaba.

Abuturrab yayi tsaki ya juya ya koma bedroom dinsa, durkushe ya ganta bakin kofa ya buda ido yace "Me kike a nan kuma?" Kallonsa tayi bata ce komai ba, yayi murmushi ya nuna mata gefen gado yace "Kiyi xaman ki, or are you afraid, she's gone already?" Mikewa tsaye tayi ta girgixa kai tace "A'a xan wuce gida karfe sha biyu muke dawowa daga lesson din" kallon agogo yayi sai kuma yace "Alryt, me xaki yi a gida yanxu idan kika koma?" Tace "Idan Mumy bata nan xan yi girki, that's all, da yamma kuma in tafi catechism" ya rungume hannayensa yace "Uhn ashe kin iya girki" xaro ido tayi tace "Kai!" Sai kuma tayi murmushi ta dauke kai, yace "Ohk idan ke kika yi girkin ki xubo min xan ci" ta kallesa da sauri tace "Da gaske?" Ya gyada mata Kai, tace "Ohk xan kawo maka" daga haka ta juya tace "Bye na tafi" yace "in raka ki?" Girgixa Kai tayi tace "Noo, thank very much" daga masa hannu tayi ya bi ta da ido har ta fita daga dakin, murmushi yayi ya sauke hannayensa ya shiga toilet, wanka ya kuma yi ya fito ya shirya cikin kananun kaya ya fito xuwa main House, da sallama ya shiga parlon, Yakumbo dake xaune tare da Mami ta bi sa da ido har ya karaso parlon, xaunawa yayi a kasan lallausan carpet din dake malale tsakar parlon ya gaisheta, ta tabe baki tace "Lafiya lau, ya aiki?" Ya shafa kai yace "Alhmdllh" Tace "Wato dai har gobe baxa kayi xumunci ba ko Aliyu, nan nan yayanka ya dawo daga Germany bayan shekaru masu yawa amma ka kasa xuwa inda yake ka gaishesa" Abuturrab ya d'an hade rai yace "Umma na kirasa fa...." Tace "Rufen baki, kira nace ko xuwa can" dauke kai yyi, Mami dai bata ce komai ba, Yakumbo tace "Ba dai ka da kamarsu a duniya wllh, idan ka so ka rike su da mutunci su ne iyayenka gobe" Mikewa Abuturrab yayi ya nufi kofa, ta bude baki tace "Ohh ga shegiya na magana koh?" Ko juyowa bai yi ba har ya fice, ta kalli Mami tace "Hajarah anya tarbiyar arxiki kika ma Aliyu kuwa, yo ashe idan Ahmad na masa magana xai iya tashi ya wuce" Mami bata ce komai ba ta mike ta bi bayansa, har ya kusa part dinsa ta gansa tace "Aliyu" juyowa yayi yana kallonta ta karasa tace "Are you stupid ake maka magana xaka tashi ka wuce" yace "Haba Mami ni me yasa matar nn baxata kyaleni bane a rayuwar nn, komai nayi tace bai yi ba, ni gaskiya darajar Abba yasa nake daga mata kafa....." Tsawa Mami tayi masa tace "Koma dai meye yayar Mahaifin ka ce, and you have to respect her the way you will respect ur father...." Bai kuma cewa komai ba ya dauke Kai, tace "Maxa ka koma ka bata hakuri kar in saba maka" da kyar yace "Ohk Mami, amma sallah xanje yi masa
llaci yanxu" bata ce komai ba ya nufi gate, ta girgixa Kai ta juya ta koma gidan, ko da Abuturrab ya dawo daga masallaci sai da ya ga dama ya shiga gidan bbu yabo bbu fallasa ya bata hakuri ya fice daga parlon, karfe hudu yana shirin fita gun aiki aka danna bell a parlor.

Haske writers asso
*Noorul Huda*
6.....
Chapter 8 · 0% Book details