← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 123

Sashe 4

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ranan da daddare Abuturrab ya xauna misalin karfe goma a gun da ya tanadar as study room, ya bude textbook din da ta basa domin Duba xanen a jiki ya kwafa, tabe baki yyi ya rufe, lumshe ido yyi na kusan minti biyar yana nazarin diagram din heart a xuciyarsa, can ya bude ido ya dau well sharpened pencil din ya shiga xana Big Mammalian heart gwanin ban sha'awa ko wani curve ya basa hakkinsa, sosai Heart din ya xanu yyi kyau kamar drawing din Artist, cikin few minutes yayi labelling ko ina snn ya ajiye pen din ya lumshe ido yana nazarin skeleton, bude idon yyi ya bude wani page ya shiga rangada babban xanen Human Skeleton, ko wani k'ashi sai da ya tabbatar ya xana, ya gama tsaf snn yayi labelling ya gama ya rufe book din yana hamma ya mike ya shige bedroom ya fada kan gado sai bacci.

Washegari da xae fita aiki bae bari ya mance materials dinta ba in case ko xa su hadu, ya ajiye back seat snn ya bar gidan bayan ya shiga ya gaida Mumy, amma bai ganta ba ranan, da ya baro gun aiki ma haka ya dinga dube dube a hanya ko xai ganta amma har ya isa gida bai ganta ba.

Karfe takwas na dare ya shirya ya fita hankalinsa kwance ta gate dinsa bbu wanda ya sani bare yyi querying dinsa inda xa shi, gidansu Saudat ya nufa don yyi missing dinta tsakanin jiya da yau, yana isa ya kirata, ba a dau time ba ta fito sai dai kumbure kumbure kawae take, yyi murmushi yace "Why the pouting?" Ta hararesa tace "Ka manta bari na tsaye kayi ranan ka wuce?" Kamo hannunta yayi yace "Ohk Am sorry dear, how you doing?"ta turo baki tace "Am good" ya shafa kansa yace "So what's new?" Tace "Baxa ka shiga ciki ba?" Yace "Noo, an san kin fito ne?" Tace "Just my little sis" yace "Mum fah?" Tace "She's in her room" yace "Toh rakani mu je mu dawo yanxu" tace "No the other time I escorted you ka sa ana ta min wani kallo a club ni baxan je ba" ya wara ido yace "Wa yace maki can xan je?" Ta hararesa tace "Ban san ka bane" dariya yayi yace "Plss baby we are not staying long fa kawai rakani xa ki yi Akwae abinda xan karba ne" shiru ta d'an yi, sai kuma a hankali tace "Ohk, just thirty minutes before ayi noticing bana gida" hannun ta ya kamo yace "Ohk dear" daga haka ya tada motar ya dau hanyar club din nasu, duk da bin sa da Saudat take club kaffa kaffa take da kanta kuma bata sake ma kowa fuska, don tana mugun sonsa shi yasa bata iya kin yin abinda yake so, Saudat kyakkyawa ce ta ajin karshe, irin matan da samarin xamani ke so, Abuturrab bai yi amfani da wnn advantage din son da take masa ba ya cutar da ita, iyaka kawai ya rike mata hannu sae d'an peck, coz he always keep it at the back of his mind dat shi ma yana da k'anni mata, bai kuma son komai ya samu lovely sisters dinsa, hakan yasa yake yaki da duk wani yaudara na diya mace, kafin minti talatin din kuwa ya maida ta gida bayan sun shiga eatry ya cika ta da kayan ciye ciye, ba shi ya koma gida ba sai kusan sha daya sai a snn ya kuma farin cikin basa side dinsa da Abba yyi, ynxu bbu wanda xai ma san ya dawo bare yace daga ina yake, yana parking gaban gate din ya fito xai bude don bbu mai gadi a side din kuma bai ma bukata, yana bude gate ya dawo xai shiga motar ya hango Samantha da wata mata da baxata haura 40 ba, wai!

Da ganinta kaga rikakkiyar Christian, skirt ne jikinta shi bai kai kasa ba amma dogo ne sosai, sae wani bujejen riga da tasa tayi tuck in dinsa cikin rigar, kanta na sanye da irin hulan nan nasu na pastress, hannunta dauke da wani gundumemen Bible, dayan kuma na rike da hannun Samantha, da ganinsu kasan daga church suke, Samantha da ta gansa ita ma sai kallonsa take fuskarta dauke da murmushi har suka iso dai dai inda yake, satan kallon uwarta tayi taga hankalinta na gaba sai rera worship songs take, hannu ta daga masa a hankali alamar bye bye, ya sakar mata murmushi shi ma ya daga mata hannun, har suka wucesa bin su yake da kallo, doguwar riga ce jikinta sai rolling da tayi a kai, girgixa kai yayi ya shiga motarsa ya ja xuwa ciki yyi parking snn ya dawo ya rufe gate din, wanka yayi ya jima xaune yana karatun Qur'ani daga karshe ya mike ya shiga bedroom ya d'an yi xuke xukensa snn ya kwanta.

Washegari da ya kasance laraba ana idar da Sllhn Asuba a masallaci drawing din Samantha ya fado masa gashi tace ranan xata yi submitting kuma test dinsu ne, satan kallon Abbansa dake Azkar y
yi, don kusan ko da yaushe tare suke fitowa daga masallaci, kuma yasan ynxu sai ya bata rabin awa yana xaune, fuskewa yyi ya mike ya fice ya nufi gida, tsaye yyi a balcony yana tunanin ko dai ya bari kila idan xai fita aiki su hadu, sai kuma ya tuna jiya ma through out basu hadun ba, ya shiga gida ya dauka makullin motarsa ya fito ya bude motar ya dauki littafin da textbook din sai math set ya bude gate ya fice, tafiyar minti goma yayi ya iso dai dai gate dinsu, rasa yanda xai yi yyi, gashi har lkcn gari bai gama washewa ba, bai ma ga alamar an bude gate din nasu ba, leken cikin gidan ya shiga yi yaji daga bayansa an daka masa tsawa "Heyyy who you be, who you find?" Juyawa yyi da sauri yana kallon mutumin ko ba a gaya masa ba yasan mai gadin gidan ne, yace "Ehm, Samantha!" Mai gadin ya masa wani kallo yace "Wetin do Samantha?" Mika masa abubuwan hannunsa yayi yace "Give her plss" daga sama har kasa mai gadin ke kallonsa, Abuturrab ya kalli kansa, jallabiya ce milk colour jikinsa, karasowa mai gadin yyi yace "Who make I say?" Abuturrab yace "Aliyu!" mai gadin ya sa hannu ya karba Abuturrab ya juya ya bar wajen, karfe bakwai da kusan rabi yana kkrin rufe kofa Ilham ta karaso, ya juya yana kallonta yace "Pretty!" Tace "Ya Abu ko shigowa ka daina yi dama nasan kafi son haka" dariya yayi yace "Eh mana, baxa ku ma dinga gani ba bare ku dinga yangan bani abinci na" tace "Yaya pls ka ba Abba hakuri ka dawo cikin gida we are missing you" kamar xata yi kuka ta kare maganar, yace "Noo, I like it so much here" tace "Why?" Yace "Nothing" tabe baki tayi tace "Ae shikenan, kayi breakfast?" Yace "Yep, Peter ya kawo min" daga haka ya kama hannunta suka bar wajen yace "Za ki sani latti, ki sa kanki latti" tace "Ya turrab 5k plss" yace "I don't have cash, sai ltr" bai jima gun Mami ba ta fito ya hau motarsa xuwa gun aiki.

Da ya tashi dawowa da yamma daga gun aiki da gundumemen K'arensa ya dawo da cage tare da mutumin dake rike da Karen, cikin few minutes aka hada cage din karen mutumin ya fito da karen da bakinsa ke a daure ya turasa cage ya rufe snn ya kunce mouth cuff din dake bakinsa, nan karen ya hau haushi, Abuturrab yyi murmushi yace "Yesss!" Tap ya nufa ya bude ruwa yana wanke hannunsa sannan ya dawi yana kallon mutun yace "Yanxu ya xa ayi karen ya saba da ni?" Mutumin yace "In dai kai ne xaka dinga basa abinci ko da yaushe cikin lkci kankani xai saba da kai" Abuturrab yace "Ohk nagode" nn ya sallami mutumin ya basa kudin mota, yana tsaye yana kallon katon karen da ya fito da halshe sai hakki yake ya ji muryar Mami a bayansa, juyawa yayi da sauri da mamaki tace "Meye wnn kuma Abuturrab?" Wara ido yayi yana murmushi yace "Dog Mami!" Hade rai tayi sosai tace "Uwar me yake a gidan nan?" Ya marairaice yace "Mami gadi xai dinga min ni bana son mutum nafi son dabba!" Bude baki tayi tana kallonsa, can ta girgixa kai tace "Toh ba gidan nan ba kare xai maka gadi, sai ka jira idan ka koma gidan ka na kanka!" Yace "Nooo Plss Mami, bangarena ne nn fah!" Tace "Nace ka fitar min da wnn abun Aliyu" karasowa yyi kamar xai yi kuka ya mata side hug yace "No plss Mami, kinga fa ina jin kamar jiya barayi sun xo anguwar nn, pls ki bar min karen it will be a good watch man for me, bbu abinda masu gadin nn suka iya sai bacci...." Girgixa kai tayi ta juya ta fara tafiya tace "Ni dai bbu ruwana...." Murmushi yayi yace "Yes Mami" main gidan ta nufa ba tare da ta tanka sa ba.

Yana xaune misalin biyar kan farin kujera yana danne dannen wayarsa yaji kamar motsi jikin gate, ya daga kai da sauri, sai kuma ya mike ya nufi gate din ya bude, tsaye ya ganta kamar munafuka, tana ganinsa ta koma baya a tsorace, murmushi ya sakar mata murya can kasa yace "Samanth....." Sai kuma yyi shiru a hankali yace "Samha!" Wara ido tayi tana murmushi tace "Ashe kana nan, just came to say a big thank you!" Har da d'an risinawarta ta kare maganan, ya jingina jikin gate ya rungume hannayensa yana kallonsa yace "For what" turo baki tayi tace "For the beautiful drawing mana" Murmushi kawai yyi yana kallon hannunta dake dauke da Bible, mota ce ta shawo kwanan anguwar ta juya da sauri tana kallon direction din, ta xaro ido tace "Jesus!
Chapter 4 · 0% Book details