← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 123

Sashe 74

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ta gama sanya kaya kafin ya shigo dakin, ta wani daure fuska ta kwanta hade da juya masa baya, gefenta ya xauna yace "Ba gashi you re much better ba yanxu da kika yi wanka" bata juyo ba kuma bata ce komai ba, ya mike yace "Mami brought you something, let me check what's it" daga haka ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo rike da warmer din da plate da cokali a hannunsa, ya ajiye k'asa yana kallonta yace "pepper soup, it's Yummy...." Ya bude warmer din yana kallonta, bai jira tace komai ba ya dibar mata pepper soup din kayan ciki ya mike yana rike da plate din ya xauna gefenta yace "Here it is" ta girgixa kai tace "Baxan ci ba" ya buda ido yace "Why?" Ta dauke kai tace "Na koshi" yace "Noo pls ki ci ko kadan ne, Mami ce fa ta aiko maki, kila ma ita tayi maki da kanta" daga haka ya ajiye plate din ya dagota, haka ya dinga bata tana wani yamutse fuska, ya kai daya baki yace "But it's sweet fa baby" bata ce komai ba, ya dinga forcing dinta ta ci me dan yawa snn ya kyaleta, sauka tayi daga kan gadon yace "Ina xa ki" nn ma bata ce komai ba ta wuce bathroom ya bi ta da kallo kafin yyi murmushi, brush ya ji tana yi, ya rufe sauran naman ya ajiye gefe, tana fitowa ta kwanta, ya matsa kusa da ita murya can kasa yace "Naga kafar ya kusa daina ciwo gaba daya koh?" Bata ce komai ba sai rufe idonta da tayi, yyi murmushi ya mike ya fitar da warmer din, sai da yyi wanka yayi shirin kwanciya kafin ya koma dakin ya tarar har tayi bacci, kashe wuta yyi ya kara A.c ya kwanta kusa da ita ya kai hannunsa fuskarta, farkawa tayi ta mike xaune da sauri, tana ganinsa ta fara kkrin sauka kan gadon ya rikota, ta fashe da kuka tace "Noo plss" jawota yyi ya kwantar da ita yace "Ni ba abinda xan maki fah baby kiyi baccin ki...." Ta kuma mikewa cikin rawan murya tace "Ni ba bacci nake ji ba" ya d'an yi murmushi yace "Do you want to sleep alone?" Kai ta gyada masa, yace "Alryt dear," daga haka ya sauka kan gadon yace "Toh kwanta" a hankali ta koma ta kwanta, ya rufa mata duvet, ya daura lips dinsa kan nata murya can ciki yace "I love you wife" light kiss yayi mata yace "Sleep tight baby" daga haka ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita ya rufe mata kofar.

Washegari wajen karfe bakwai ta tashi, ji tayi gaba daya bbu inda ke mata ciwo, ta sauka a hankali kan gadon ta nufi bathroom.

Karfe bakwai da wani abu ta fito parlor ta gansa kwance yana bacci a 3 seater, kallon takardun dake kan center table a gabansa take kafin ta karasa ta dauka, kallo daya tayi ma uban rubutun da yyi ta hade gaba daya ta yaga in to three ta ajiye masa nan kan table din ta juya ta koma daki, ringing din wayarsa ne ya tada sa, ya jawo wayar a hankali yana kallon screen din ya ga Small mum dinsa ce, mikewa xaune yayi ya daga ya kai kunne, amsa sallamarta yyi yace "Mum!" Tace "an tashi lfya?" Ya gaisheta ta amsa tace "Kai baka kiran mutane Aliyu" ya shafa kai yace "Kiyi hakuri sweet mum, sometimes ina tunanin kiran is nt safe" tace "Alryt, ina ku ke a gombe?" Shiru ya d'an yi sai kuma yace "Na'am" tace "You heard me right Aliyu" murmushi yyi yace "Mum xuwa xa kiyi?" Tace "Ko kar in xo?" Ya wara ido yace "Noo, mum you re welcm....

Yaushe xa ki xo plss?" Tace "Gobe Saturday in'sha Allah" yace "Waoww, Allah ya kai mu mum, but please kiyi persuading Mami ta bar su ilham ku xo tare, am really missing them" tace "I think ur dad is around" shiru yyi bai ce komai ba, tace "Amma kayi mata flashing, idan ta kira sai ka tambayeta ka ji me xata ce" yace "Toh mum i will do that right away" tace "Alryt" yace "Let me send u the address ynxu" sallama suka yi, yyi texting mata address snn yayi ma Mami flashing, Mami dake bedroom dinta tare da su Ilham ta dau wayarta tana kallo, duk da ba saving din number tayi ba tasan wanda yyi flashing din, kira tayi ta kai kunne, yana dagawa tace "Aliyu" yace "Ina kwana Mami" tace "Lfya lau, ya kuke?" Tuni su Ramla suka dawo kusa da ita gaba daya ko wacce na son a bata waya, daga daya bangaren yace "Mami pls pls kiyi convincing Abba ya bar su Ilham su taho tare da Mum..." Kamar xae mata kuka yyi maganan, tace "Makarantar fa Ali?" Yace "Mami bai fi su yi sati daya kawai ba fa" shiru tayi...

Yace "Plss Mami" tace "Toh bari in ji yanda xae ce" da sauri yace "Amma Mami ina xa ki ce masa za su?" Tace "Gidanku!" Murmushi yyi yana shafa kansa yace "When shud i be expecting ur call Mami" tace "Sai mun yi magana da shi" yace "Toh nagode Mami" tace "Ina matar taka?" Ya kalli agogo ganin tara ya wuce yace "Tana gida" tace "Kai kana ina?" Yace "Emm na fito gun aiki" tace "Alryt" daga haka suka yi sallama dai dai lkcn da idonsa ya sauka kan takardun kan table, mikewa yyi da sauri ya daukesu yana kallo da mamaki, can ya kalli hanyar bedroom ya kuma kallon takardun, bedroom din ya nufa ya bude dakinta, gyaran gun kayanta ya sameta tana yi, ya karasa cikin dakin yace "Why did you tear this Samha?" Bata ko kallesa ba tace "Why did i tear what??" Shiru yyi yana kallonta, jin bai ce komai ba ta juya ta kallesa, kallonta taga yana yi ta turo baki ta ci gaba da abinda take yi, yace "Kin san meye wnn din kika yaga?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Yea, ko ba assignment ba" ya girgixa kai yace "Noo, it's research da Mami ta bani in yi, nd i have being doing this tun shekaranjiya a office, i completed it around 3am this morning nd you've ruined everything" juyawa tayi ta kalli takardun, ya juya ya bar dakin ta bi sa da ido, a hankali ta juya ta ci gaba da abinda take yi, tana gamawa ta fita daga dakin, kitchen ta wuce ta kunna gas ta daura ruwan lipton ta xuba kayan kamshi snn ta fara feraye Irish, cikin minti talatin ta gama hada breakfast ta kai parlor ta ajiye, bedroom dinsa ta nufa ta tura kofa a hankali ta shiga, tsaye ta gansa ya gama shiryawa cikin fararen shadda, ya dau makullin mota da takardun ya juya suka hada ido, ta hade rai tace "Toh ni ban san it's useful ba ai, am sorry" yace "It's ohk" daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo, can ta bi bayansa, har ya kai kofar fita tace "Baxa ka yi breakfast ba?" Ya bude kofar yace "Ki ci nawa da naki" daga haka ya fita.

Karfe sha daya Mami ta samu Abba a part dinsa, ta xauna tana kallonsa tace "Col, Mariya xata je yola gobe, ina son ta je da su Ramla su gaisa da gwaggwo da yan uwana, rabonsu da can kusan shekara bakwai" idonsa na kan takardan hannunsa yace "Boko da islamiyyan fah?" Tace "Ae yau friday, bai fi su yi kwana uku ba, ran Monday ko talata xa su dawo" ya girgixa kai yace "Noo, it's better a bar shi lkcn hutu Madam" tace "Amma ae baka cewa sae lkcn hutu xa su gun yan uwanka col, duk lkcn da kayi ra'ayi kke cewa su shirya su je, kayi adalci mana Yallabai, sorry to say, yan uwa fa ba su fi yan uwa ba" sai a snn ya kalleta yace "Su nawa xa su bi ta?" Tace "Su duka" wani kallo yyi mata yace "Kin taba ganin inda aka tura yara gaba daya lkci daya suyi tafiya, kinga ki bar ni in ci gaba da ji da rashin Ali...." Ta buda ido tace "Toh fah!

Rashin sa na damun ka kenan?" Yace "Did you knw what an only son means?" Ta d'an yi murmushi tace "I never thought u were missing him, har ina mamakin duk bond din ka da Aliyu ka iya watanni da dama ba shi tare da kai, bana manta lkcn da yake karatu waje, kusan duk karshen wata biyu ana kan hanyar xuwa gun only son" wani kallo ya watsa mata yace "Are you teasing me?" Tace "Why will i.... nasan duk inda Abuturrab yake he is also missing home, just that he knws d kind of dad he has, am pretty sure he is afraid of coming back, baxae taba dawowa ba kwana kusa na sani" ya mike ya kuma jefa mata wani kallo yace "Ki fadi alkhairi ko kiyi shiru" daga haka ya nufi kofa, ta bi sa da ido tana murmushi, can ta mike da sauri tace "Col ya maganar tafiyar su Ramlan" yace "yarana baxa su bi hanya gaba dayansu ba, sai dai daya ta bi ta" ta girgixa kai tace "Ba wannan xancen, sai dai Ilham da Khaleesat su bi ta ita Ramla ta hakura" bai tanka ta ba ya fice.
Chapter 74 · 0% Book details