← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 123

Sashe 5

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbana ya dawo" kallon motar yayi da sauri sai kuma ya matsa daga gun gate din bata jira yace mata komai ba ta shige cikin gidan, wara ido yayi yana kallon motar har ya xo ya wuce snn ya shiga gidan ya rufe gate din, tsaye ya ganta tayi lamo jikin flower, tana ganin ya rufe gate din ta karaso da sauri tace "Ae ya tafi ko, let me leave" kallon gate din yayi yace "I don't think ya tafi fa, tare yake da wasu a motar kuma na ga sun tsaya" kamar xata yi kuka tace "Bbu wani hanyar doctor?" Girgixa Kai yayi yace "Only this....

Ga kujera ki xauna ki jira su wuce sai ki tafi," Da damuwa tace "Church fa xan tafi, I don't want to miss" shiru yyi yana kallonta, can ya juya ya dau wani kujerar yayi xamansa, bin bayansa tayi tana bin gidan da kallo ta xauna kujerar da ya nuna mata tace "Are you the only one leaving here?" Girgixa kai yayi ya nuna mata hanyar da main house din yake yace "My family members are there, my Mum, Dad and sweet siblings" mikewa tayi ta nufi inda ya nuna mata bata wani yi nisa ba ta hango kantamemen gidan daga nisa, dawowa tayi da sauri tace "Uhn!

Toh me yasa kai kake boys quatrs?" Murmushi yayi yace "Because I am a boy, an I prefer here" 'yar dariya tayi tace "Ohk that's true, xan wuce church yanxu" mikewa yayi yace "Bari in duba maki ko ya tafi" daga haka ya tafi gun gate ya bude ya leka, rufewa yyi da sauri ya dawo yace "Noo they are still there ki xauna kawai su wuce" bata fuska tayi tace "Lokacin Church na wucewa" bai tanka ta ba hakan yasa ta xauna, haushin k'are taji ta mike a firgice tana kallon direction din, ihu tayi suna ido hudu da katon karen ta juya xata gudu a rikice yyi saurin rikota da sauri, ta fashe da kuka tace "Noo bana son kare pls" xaunar da ita yyi kan kujera ya durkusa gabanta yana kallonta yace "But it's caged" Har lkcn jikinta rawa yake ta kasa cewa komai, dagota yyi ya shiga balcony da ita ya sa ta xauna ya duka gabanta yace "Ohk sorry Plss...." Hawaye ya sakko idonta tace "Ni xan tafi" mikewa yayi ita ma ta tashi, yace "Karen baya komai, it's very frndly" bata ko kalli inda karen yake ba ta nufi gate da saurinta, ya bi bayanta amma tuni ta fice, tsaye yyi bakin gate dinya rungume hannunsa ya bi ta da kallo ganin yanda take sauri, sai da ta tabbatar tayi nisa snn ta juya ta kallesa, d'aga masa hannu tayi, ya juya ya shige gate din yayi banging dinsa, kasa ci gaba da tafiya tayi sai kallon gate din take, can ta juya jiki ba kwari ta ci gaba da tafiya.
[7/19, 5:58 AM] 0mmer Farouk:
*Noorul Huda*
4......

Washegari da yamma misalin biyar da rabi Abuturrab na xaune karkashin artificial bishiyar dake dauke da fararen kujeru a karkashi hannunsa rike da Cigarette, dawowarsa kenan daga aiki yayi wanka ya d'an tsakuri abincinsa da ke ajiye a parlor snn ya fito ya xauna ya fara aikin xuke xukensa idonsa na kan k'aren dake ta fama da gundumemen naman da ya siyo masa a hanya, murmushi yayi ya mike ya shiga ciki sai ga shi ya fito da babban drawing board da materials din drawing dinsa, bude board din yyi ya tsayar ya dawo da farin kujera kusa da board din ya xauna dai dai yanda xai dinga ganin karen da kyau, ya fi minti biyar yana kallon karen hannunsa rike da well sharpened drawing pencil din hannunsa, daura hannun nasa yyi kan board din, a nutse ya shiga xana k'aren, ya kusa minti goma yana xana kai snn ya dawo jiki, yyi rabi yaji an tura gate a hankali ya juya da sauri, ido hudu suka yi da ita, ta wara ido kamar mara gaskiya ta k'asa tsaye gu daya tana jujjuya Bible din hannunta tace "Am...

Ina yini!" Murmushi yayi ya maida dubansa kan board din gabansa yace "Come in....." Kin shigowa tayi tana yi tana lekan karen dake cage tace "No, am going for service!" Ya kalleta yace "Ohk baxa a gaisa ba knn yau?" Murmushi tayi tace "Gashi na gaishe ka, and I can see you are busy drawing what I can't see from here!" Mikewa yayi ya karasa gabanta, tayi tsuru tsuru tana kallonsa, kallonta yayi daga sama har kasa, yau ma doguwar riga ce sea green jikinta, sai jan veil da ta daura a kanta, cikin idonta dake kyalli kmr ta tara hawaye ya kalla, ta juya da sauri xata bar gate din ya riko hannunta, juyowa tayi tana kallonsa, ya sakar mata murmushi yace "Yea, baxa ki ga abinda nake zanawa daga nan ba sai kin shigo" kallon karen tayi a tsorace tace "Noo, ni ina jin tsoron...." Jawota yayi xuwa cikin gidan ya rufe gate din, tace "Noo Plss...." Janta yyi har xuwa gun drawing board din sai buya take bayansa, ya dawo da ita gaba idonta ya sauka kan xanen, shiru tayi tana kallo ko kiftawa bbu, a hankali ta furta "Waoww....." Kallon karen dake cage tayi snn ta kalli na drawing din ta juya da sauri tana kallonsa tace "Doctor wa ya koya ma drawing haka, you are....

" Rungume hannayensa yayi yace "In koya maki ne ke ma?" Da sauri ta gyada kai, ya ja kujeran ya xauna ya dau pencil din ya ci gaba da xanen, durkusawa tayi a hankali kusa da shi ta dafa kafarsa tana kallon yanda yake xanen cike da kwarewa, muryar Khaleesat ya ji, ya juya da sauri sai kuma ya mike ya xaga ae ko ya hango ta ita da Ilham suna tahowa, dawowa yayi da sauri yana kallon Samantha tun kan yace komai ta mike a rikice tace "Your sister I guess?" Bai ce komai ba ya kama hannunta ya nufi kofar parlor ya bude ya sa ta shiga snn ya rufe ya dawo gun drawing din ya xauna ya ci gaba, Khaleesat da Ilham suka karaso, Ilham ta wara ido tace "Waow ya Abuu....

It's sooo beautiful!" Ta gefen ido ya kalleta yace "Thanks" Khaleesat ta durkusa kusa da shi tace "Yaya wai Anty Ramla tace kace xaka kawo wani karen main house, da gaske ne" ya hade rai yace "You two can see am busy...." Khaleesat tace "Don ma mun taho taya ka hira tunda bbu islamiyya yau?" Bai tanka ta ba, Ilham tace "Toh shknn since he's busy let go inside and....." Mikewa yayi da sauri kmr wanda aka mintsila yace "Go where?

Kar warce ta shigar min parlor....." Ilham ta bude ido da mamaki tace "Why?" Wani kallo ya watsa mata ya nuna mata hanyar inda suka fito, ganin bbu wasa tattare da shi yasa duk suka juya suka bar gun, ya bi su da kallo har suka bace, ya ajiye pencil din hannunsa, Samantha dake ta kallonsu ta window ta bude kofa ta fito, murmushi ta masa tace "Ur siblings are cute, they re fine...." Rungume hannuwansa yayi ya daga kafada, tace "Bye na tafi church!" Daga haka ta nufi gate ya bi ta da sauri yace "Wait!

Baxa ki jira in gama ki gani ba" tace "Lkci na wucewa xan je church ne fa" yace "Ohk I will be very fast sai ki wuce" shiru tayi ya wara mata ido yace "C'mon" karasowa tayi ya xauna ya ci gaba da drawing din ita kuma ta durkusa kusa da shi, sai da aka yi wani minti talatin kafin ya gama xanen, ta xuba ma board din ido tana kallon katon karen dake ta dambe da k'ashi, can ta lumshe ido a hankali tace "Waow, you are so talented" murmushi yayi yana nodding kai yace "Thank you....

Samanth..

Uhm Samha!" Xaro ido tayi tace "Am not Samha but Samantha!" Ya daga kafada yace "Ohk all same...." Hamma yayi yana stretching din hannunsa yace "Am exhausted, No am hungry rather" tace "Baka ci abinci ba?" Langwabar da kai yayi yace "It's finished...." Shiru tayi sai kuma tace "toh me xaka ci?" Ya juya manyan Eye balls dinsa yace "May be black tea, da yaji kayan kamshi" ta tallabi kuncinta tace "Toh wa xai ma, ko xaka shiga gida ka gaya ma Mumy" ya d'an marairaice yace "She won't, yanxu dinner take yi na sani" a hankali tace "Toh ni in maka?" Yayi shiru sai kuma yace "Yess Plss" mikewa tayi tace "Toh xo ka nuna min kitchen din da komai...." Mikewa yayi yace "Yauwa thanks frnd, shiga ki jira inje can cikin gida in dauko lipton din da scent ingredients" dariya tayi tace "Ohk ohk" yayi murmushi ya juya ya nufi can cikin gida ita kuma ta shiga parlonsa, ba a dau lkci ba ya dawo rike da su a wani bowl, ta mike daga xaunen da take ta karba ya rakata kitchen din, yana tsaye daga bakin kofa ta gama dafa ruwan lipton din da ya dume gidan da kamshi, ta juye masa a flask din da ya nuna mata ya karaso kitchen din yana murmushi yace "Waow thanks frnd!" Murmushin ita ma tayi yayi mata stretching din long fair hand dinsa me dauke da kwantancen bakin gashi, a hankali tayi stretching din nata ya karba yayi shaking dinta, yana kallon kwayar idonta.
Chapter 5 · 0% Book details