Sashe 115
Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Abuturrab ya langwabar da kansa bayan sun isa Atm yace "Mum kudin account dina is nt up to 500k fa, kuma...." Tace "Baka da damuwa sai in ranta maka idan ka samu ka mayar min da kayana" dariya yyi yace "Kai mum" tace "Ehh, xan dai bada tawa gudunmawar kayan jewelries" yace "Toh nagode mum" dubu dari biyu da hamsin kawai ya ciro a account dinsa, ita ma ta cire kudi me yawa bata dai gaya masa ko nawa bne suka shiga kasuwa, akwatuna masu kyau na xamani ta fara sa suka siya set guda, daga nn kuma suka shiga shagunan atamfofi ta siya manyan atamfa guda sha biyar snn ta siya masu d'an saukin kudi guda goma, ta siya lace masu tsada biyar, sai materials da abaya kala kala, mayafai, hijab, jakunkuna, takalma, kayan shafe shafe, turare, sabulai, kai duk abinda tasan ana xubawa a lefe har da su pray mat, alqur'an da carbi, sae jewelries da ta bata lkci wajen xabansu, Abuturrab dake xaune sai kallon ikon Allah yake yace "Mum kashe ni kike son yi kawai" kallonsa tayi tace "Wato ga yarinya ka samu a bnxa koh" dariya yyi yace "Wayyo mum a dai tausaya min, ni fa ne naki" tace "A'a mamar ka na can inda ka baro ta, wnn ce tawa a ynxu" ba su suka bar kasuwan ba sai kusan la'asar, sae da ta tabbatar bbu abinda ya rage bata siya ma Noor ba uwa ynxu xa ayi auren, sai da suka isa gida ta juya tana kallonsa tace "Kudin da xaka ban nayi lissafi 450k bnda kudin jewelries" xaro ido yyi yana kallonta, bata kuma kallon inda yake ba ta fita motar, ta kira mai gadi ya taimaka mata shiga da kaya ciki, Abuturrab ya fito motar yana murmushi a xuciyarsa yace "Lallai mum" Noor bata iya tace ma Hajiya Mariya dake ta nuna mata kayan tana jera su a akwati komai ba, duk jikinta yyi sanyi wanda hakan yasa bata san lkcn da hawaye ya shiga sakko mata ba, jin shirunta yyi yawa Hajiya Mariya ta dago tana kallonta, ganin kuka take tace "Ikon Allah, kuka kuma Samha" dawowa tayi kusa da ita tace "Kukan me kike daughter" rungumeta Noor tayi cikin muryar kuka tace "I love you mum, nagode Allah kara maki tsawon kwana" Hajiya Mariya tayi murmushi tace "Toh Amin my daughter, you take me as ur mother kin ji" karfe biyar da wani abu Hajiya Mariya tayi mata duk abinda tasan ya dace dai na gyaran jiki, ta kira mijinta ta rokesa alfarmar siya masu foodstuffs, ba a dau lkci ba driver ya shigo da buhun shinkafa biyu, carton din taliya uku, jarkan man gyada da manja manya, maggi, gishiri har da kwalayen indomie biyu, Abuturrab na shigowa tace "Toh ga gara nn Alhaji yyi mata nasan har ku bar duniya baxa ka mata gorin hakan ba wataran tunda ku din ba tabbas ne da ku ba, kayan daki kuma in shaa Allah idan kudi ya shigo min xan siya mata nata" dariya yyi sosai yace "Mum you are making me feel ashame, haba my mum" bata sauraresa ba ta kara gaba abunta, bayan magrib Hajiya Mariya ta rakasu can gidan nasu da aka yi furnishing tuni, duplex ne mai kyau da parlor sama da kasa sai dakuna huda ko wanne da bathroom, sannan babban kitchen, xa a iya cewa col ne ya gina masa gidan don kudinsa ba mai yawa bane a ginin gidan, Da yake abban nasa yasan halinsa shi yasa bai yrda ya tare gidan ba da dadewa sai masu gadi har uku dake rayuwa cikin gidan, Kuka Noor ta dinga yi da Hajiya Mariya xata wuce, Hajiya Mariya dake dariya tace "Ae sai yaran ki su maki dariya Samha, kar ki damu ko xuwa jibi Hauwa xata dawo ta dinga xama da ku sai in nemi wata mai aikin" tun barin Hajiya Mariya gidan Noor taki daina kukan da take, ita har xuciyarta take son matar, duk iya rarrashin da Abuturrab yyi mata kin saurarensa tayi, ya kyaleta ya maida hankalinsa kan boys dinsa dake kwance kan gado, ana kiran isha ya tafi masallaci da xai dawo ya dawo masu da take away da fresh milk, shi kadai ya ci don ko kallon abincin ita bata yi, yyi wankansa ya sauya xuwa pyjamas ya kashe wutan daki yyi kwanciyarsa kusa da yaran dake bacci, ta gaji don kanta bayan kusan awa daya ta mike ta shiga bathroom ta dauro alwala ta fito tayi sllh, tana idarwa ta canxa kayan jikinta xuwa rigar bacci don tayi wanka a can gidan, ta je can karshen gado tayi kwanciyarta ta juya masu baya, dawowa yyi kusa da ita ya jawo ta jikinsa murya can kasa yace "Oya ci gaba da kukan" turo baki tayi xata kwace kanta yace "Baki isa ba, ci gaba ina son rarrashin ki yanda ya kamata ne" cikin muryar shagwaba tace "Ni ka bar ni, bana soo..." Tsit tayi ta lumshe ido don bbu bata lkci ya fara rarrashin nata yanda ya kamata kuwa.
*Haske writers asso*
tnx for d prayers everyone.
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
101.....
*Haske writers asso*
tnx for d prayers everyone.
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
101.....