← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 123

Sashe 57

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe takwas da yan mintuna Ummi na xaune daki gaban computer sai dai gaba daya hankalinta bai kai, sosai su Abuturrab suka tsaya mata don bata san halin da xa su je su shiga ba kuma, jawo wayarta tayi for the 5th time within that period ta sake dialing numbersa amma switch off ta dafe kai, bude kofar dakinta aka yi ta dago da sauri Yusuf ya karaso ya xauna kujera yana kallonta yace "Sannu da aiki Ummi" ba tare da ta kallesa ba idonsa a kan screen din computer tace "Yauwa" Ya d'an yi murmushi yace "Ummi kar fa ki sa ma kanki damuwa, dama ni ina ganin Aliyu nasan ba shi da gaskiya, as in the way he does his things ma xaka gane hakan, baka taba gane abinda ke ransa na lura, he can be a silent killer, at the first place na tambayeki hadinsa da Samha kika ki gaya min, daga bincikena tun a jiya na gano Samha ba matarsa bace, though bance xaman banxa suke ba, amma daga duk alamu rabo ta da iyayenta yayi may be for his selfish interest, tun daga lkcn da kika ce min bai ji na fara gano wasu abubuwan....

But Ummi me yasa kika boye min kilan da hakan da ya faru ynxu bai faru ba, i would have kept an eye...." Kallonsa Ummi tayi a karo na farko tace "Bana son xancen Yusuf" mikewa yayi yace "Aiit, buh am gonna fish him out idan Allah ya yarda" daga haka ya fita.

Anty Maryam na xaune tsakar gida a ranan tana wanke kwanukan da suka ci abinci amma hankalinta na ga tunanin decision din da suka yanke da mai gidanta na aura ma Aliyu Yar d'an uwanta, bude kofar soro aka yi ta juya da sauri taga Rachael ce da Sarah, Duk da ba wuta tsakar gidan sai hasken wata hakan bai hanata ganin yanda Rachael ta daure fuska ba tana tahowa kamar xata tashi sama, Anty Maryam ta dauke kai tana murmushi ta ci gaba da wanke wankenta, sarah ce kadai tayi mata sannu da gida suka shige parlor, Anty Maryam ta mike ta dau abinci ta kai masu ta fito, ko da ta gama wanke wanken xamanta tayi tsakar gida tana sake saken yanda al'amarin gobe xai kasance, can ta mike ta shiga dakin mai gidanta ta xauna tana kallonsa tace "Abbansu Asiya ya kake ganin xa ayi gobe ne wai" Yace "Gun mai gari xa mu je a daura auren sai su tafi duk inda xa su, matukar xai iya kula da ita, na kuma ga yana sonta sosai don da ganinsa kasan ba karamin mutum bane." Da damuwa tace "To fa bata amshi musulunci ba har ynxu" yayi murmushi yace "Ba yar ki bace kin san yanda xa ki bi da ita ai, sai dai kuma kada a tilastata don in har aka yi haka tana iya komawa gidan jiya tun da ba da son ranta ba....

Ko kin mance yanda muka yi da ke Maryam" ganin dariyar da yyi ta hade rai tace "A'a ni baka aureni a Christian ba ni musulma ce a lkcn ma" yace "Amma a lkcn abubuwan da kike yi meye banbancin ki da Christians din, ba fa gori nake maki ba rabin rai kawae dai magana ce" ta tabe baki tace "Ae don ina gun yayana ne lkcn Kuma mahaifiyar Samantha ce matsayin uwata...." Yace "Toh kar ki ji komai ni nasan da kanta xata yi sha'awar addininmu ba sai an mata dole ba, at the first ma da bata son musulunci baxata yarda da musulmi ba har su gudu tare ta bar iyayenta" Anty Maryam tace "Haka ne, kuma kaga lkcn da take xuwa hutu nan bata kin yi duk abinda na sa ta tun daga kan sllh har xuwa tafiya islamiyya da su Asiya" yace "Toh kin ga" Mikewa tayi tace "Bari in je can parlor" daga haka ta fita.

Washegari da ya kasance friday da safe Abuturrab ya fito ya nemi d'an boutique ya siya kaya da kudin dake hannunsa, daga haka ya nufi Atm machine don cire kudi, takaici ne ya ishesa don Atm machine din da ya gani bai fi biyu ba kuma duk ba kudi, kallon agogon hannunsa yayi yaga tara bata yi ba, kawai yayi deciding ya wuce cikin kaduna kawae, sai da ya koma hotel ya shirya snn ya dau hanya, yana isa ya kunna wayarsa tunawa da yyi sun yi exchanging number da mijin Anty Maryam, yana cire kudin ya shiga tunanin me xai siya kuma kafin ya koma wayarsa ya shiga ring Sadeeq ya gani jikin Screen din, har ya fara tunanin waye kuma sadeeq kawai ya tuna gayen da suka hau mota tare tun daga gombe, dagawa yyi, nan suka gaisa da fara'a Abuturrab yace "Kasan jiya fa can maraba muka wuce amma yanxu ina cikin kaduna na xo cire kudi..." Sadeeq yace "Au haba, a ina kake yanxun?" Abuturrab ya kalli gun yace "Ina bypass" Sadeeq yace "Haba to ka karaso nan gidanmu mana kafin ka koma" Abuturrab ya kalli agogo sai dai bai son Sadeeq ya ga kamar yyi shun dinsa, yace "Funny you, ni da nake sauri" Sadeeq yace "Sai in kai ka har maraban da motata" Abuturrab yyi jim don bai son exposing secret dinsa ma kowa kuma, can dai yace "Haba don xan xo gidan ku sai ince sai ka mayar dani, bari in taho sharp sharp in koma ba sai ka yi wahalan kai ni ba" Sadeeq yace "Alryt" address ya tura ma Abuturrab da yake yasan garin xuwa gidan bai yi masa wahala ba sai dai ba dai nisa ba don sai kallon agogo yake, babban anguwa ce ta masu abun hannu, Sadeeq ya fito daga wani kantamemen gida mai dauke da gate biyu kai da ganin gidan kasan naira ya xauna, nan suka gaisa sadeeq na dariya yace "Ashe dai xaka gane..." Abuturrab yace "Haba dai ai ba wani wahala" daga haka suka shiga gidan sadeeq ya kai sa har babban parlon gidan, Abuturrab na xama ya ji gabansa na faduwa ya rasa dalili, Sadeeq na kallon kanwarsa da ta fito yace "Kiyi setting mana breakfast a bedroom dina" tace "Toh" sannan ta gaida Abuturrab ta koma kitchen, Sadeeq yace "This is our home, you feel free frnd" Abuturrab yayi murmushin karfin hali yace "Sure" Ana bude kofar parlor ya waiga da sauri kamar jira yake, bai san lkcn da ya mike tsaye yana kallon mutumin dake kallonsa shi ma a bakin kofar ba, Sadeeq ma ya mike yace "He is my Dad...." Abuturrab ya kallesa ya kirkiri murmushi yace "Ohh alryt" juyawa Mutumin yyi ya fita, nan hankalin Abuturrab yayi mugun tashi, ya dake ya koma ya xauna, Sadeeq dake ta studying dinsa yace "Any problem Aliyu?" Wara ido yayi yace "Ohh nothing Sadeeq" ba a dau lkci ba mutumin ya dawo parlor, sai a snn Abuturrab ya gaida shi kansa a kasa, mutumin ya amsa yayi wucewarsa Sama, mikewa Abuturrab yyi yana kallon Sadeeq yace "Let me answer a call in dawo" daga haka yayi waje da sauri, wani mugun faduwa gabansa yyi ganin mutanen da bai gani ba lkcn da xa su shigo tsaye bakin gate wato dai soldiers in uniform, dakewa yayi ya karasa xuciyarsa na bugawa ganin kallon da soldiers din ke masa kawai ya juya ya koma ciki da sauri yana furta innalillahi a xuciyarsa, Yana shiga parlorn ya isa gun Sadeeq da sauri, Sadeeq ya mike da sauri ganin tashin hankali bayyane fuskarsa yace "Aliyu lafiya" Abuturrab yace "Nooo, help me out now plss!! ur dad....

Abokin Abba na ne" Sadeeq dake kallonsa da mamaki yace "Then?" Abuturrab ya kamo hannunsa yace "Don Allah make a way out for me nayi ma Abbana babban laifi i left home for months, nasan kilan yanxu ya ma kirasa wllh....

Plss" tsit Abuturrab yayi ganin Col Ishaq yana saukowa stairs, da sauri sadeeq yace "Haba to meye baxa ka hau sama mu yi break ba sai a nan frnd, plss mu tafi bedroom dina, it will be more convenient there."
*Haske writers asso*
Afuwan for the delay
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
51.....

Abuturrab ya gyada kai yana kirkiran murmushi yace "Toh... toh mu tafi dakin" Ta gefen mahaifin Sadeeq suka wuce xuwa dakin Sadeeq din, Sadeeq ya sa ma kofar key yace "Shitt, ohh God, i caused everything" Abuturrab kam xaunawa yayi kan gado ya rike kai, Sadeeq ya nufi Balcony din dakin da sauri yana kallon kasa ya girgixa kai ganin prickled Object dake watse a kasa wanda sbda shi aka xuba su, dawowa daki yyi yana tunanin hanyar da xa su bi su bar gidan don yasan duk Abbansa ya sa an toshe hanyoyin da yake bi, can ya dafe Abuturrab yace "Chill guy sai dai idan ba sojoji suka haife mu ba, we will surely find a way out, look... bana daukar last a irin haka fa, ni nan da kake gani ko kama kafata baka yi ba gun rashin ji, don haka in sha Allah sai mun fita" Abuturrab ya kallesa sai yyi murmushi yace "Yea kuma haka ne, buh we have to be very fast frnd" Sadeeq ya isa kusa da kofarsa ya bude a hankali tsaye ya ga Dad dinsa corridor din, pretending yyi yace "Abba you are here dama" Dad dinsa bai tanka sa ba, sadeeq ya shiga bedroom din mum dinsa, Kanwarsa Sumayya ce ke dakin tana gyara, yace "Sumy Umma fah?" Sumayya tace "Tana kitchen," shiru yyi sai kuma ya bude balcony din Ummantasa yana leken kasa, can ya dawo ya fara bude drawers dinta yana bincike, Sumy ta ja ta tsaya tana kallonsa da mamaki, ya kusa minti biyar kafin ya dago ganin kallon da take masa ya jawota a hankali yace "Pls Sumy am in trouble ki taimake ni" da mamaki tace "Me kuma kayi" murya can kasa yace "Ni da frnd dina wllh.
Chapter 57 · 0% Book details