← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 123

Sashe 80

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Har ta shiga kitchen bata kalli inda suke ba, ta gama hada masa abinda yace ta xo ta wucesu, Khaleesat tace "Damn this, wnn arniyar ce xata xo tana daga mana kai a gidan yayanmu" Fatima ta dan bude ido tace "Arniya kuma?" Ilham ta tura cup din gabanta tace "Ehh mana christain" Fatima dake kallonsu da mamaki tace "Ban gane ba" Khaleesat tace "Ohk bai fadi maku Christian ce ita ba knn, she's a nonbeliever, kawai taje tayi tsafinta ta rabamu da yayanmu" kmr xata yi kuka ta kare maganan, Har lkcn kallonsu fatima take kmr bata yrda da abinda suke cewa ba, Khaleesat tace "Ae kafin in bar gidan nn sai na nakada mata duka wllh, kuma sai duk mun gaya ma Mami abinda muka gani" A tare Samha suka yi break din da Abuturrab duk da ta ki da farko, amma yana insisting ta xauna kusa da shi, suna gamawa yasa ta saka Hijab suka fita, sai da suka fara shiga gun small mum dinsa yace mata xa su je su dawo tayi masu Allah ya kiyaye snn ya fito ya dau makullin motarsa a bedroom, kallonsu su ilham suke yi har suka karaso cikin parlor, yyi ma fatima kallo daya ya kauda kai, yana kallon kanninsa yace "You girls shud wash all used plates, kuma ku gyara min dakina ku wanke bathroom" khaleesat tace "Yaya ina xa ka?" Yace "Ba dadewa xan yi ba" Ita dai Samha tana tsaye idonta a kan fingers dinta, Ido fatima ta kafa mata kmr me son gano abinda su ilham suka fadi mata, Khaleesat ta dauke kai tace "Toh shine baxa mu bi ka ba?" Yace "Ae ba yawo xan je ba, gun aiki xan fita, i will be back soon" Daga haka ya kama hannun samha suka nufi kofa, suna fita Khaleesat tace "Damn it, she is d one controlling him" Tun da suka shigo reception ake kallonsu, ya amsa gaisuwar nurses dake gun, Ita ma ta gaishesu duk suka amsa, daga haka ta bi bayansa, duk suka bi ta da ido, wata nurse tace "No wonder his eyes are not on women, his wife is a damsel" yar uwarta ta amsa da cewa "Yea she's beautiful shi yasa yake ma masu crushing dinsa kallon donkeys" wasu daga nurses din ne kawai suka yi dariya, office dinsa ya kai ta ya kunna mata Tv da A.c, ya isa gabanta yace "Enjoy ur self baby, idan kin gaji da xama ki kwanta, i think xamu shiga theatre ne" daga haka ya duka ya manna mata kiss a cheeks dinta yana murmushi ya ja hancinta ya juya ya fita, bai dde da fita ba ta mike ta isa kan bed din duba pregnant women ta kwanta tana kallon movie din da ake a tv, sai kusan karfe sha daya da rabi bacci ya dauketa, bata dde tana baccin ba taji ana shafa fuskarta, a hankali ta bude idonta ta gansa tsaye sanye da surgical clothing, da hula, ya sauke mask din fuskarsa hannunsa daya rike da baby a Shawl, mikewa xaune tayi tana kallon babyn hannunsa ta sauko daga kan bed din da sauri ta wara ido tace "Waow It's a baby!" Dariya ta basa yace "Yea you like babies?" ta gyada masa kai da sauri, mika mata babyn yayi ta rasa ynda xata yi ta karba, har rawa hannunta yake, kallonta yake cike da tausayi tunawa da yyi she's an only child, no siblings, kmr xata yi kuka tace "Ban san yanda xan rike ba doctor" jawota yyi jikinsa ya rungumeta tare da babyn, sai a snn ta iya wrapping babyn da hannunta ita ma tana lekan fuskar jaririn, ya kai bakinsa saitin kunnenta murya can kasa yace "Ke ma kina son ki haifi naki babyn?" Kallonsa tayi ba tare da tayi wani tunani ba tace "Ehh ina so" ya wara ido yace "Da gaske?" Jin ynda yyi maganan ta kuma kallonsa, ganin irin kallon da yake mata ta dauke kanta, ya daura daya hannunsa a flat tummy dinta yana murmushi yace "Soon xa ki haifi naki kema tunda kina so, yau da daddare xa mu samu namu babyn amma mace ni nake so wacce xata yi kama da ke" da sauri ta daga kai ta kallesa dai dai lkcn da aka bude kofar office din doctor Shariff ya shigo, ta sakar masa yaron ta ja gefe, Dr Shariff yace "Ohh ashe tare da madam ku ke Aliyu," Abuturrab yace "Ae kam, Cewa tayi yau sai ta bi ni, ba ynda na iya muka taho tare" yana murmushi ya kare maganan, Dr Shariff yyi dariya yace "Ohh toh sannun ki da xuwa madam, ya gidan?" kanta a kasa ta gaishesa ya amsa da fara'a yana sake welcoming dinta, nan ya dau abinda xae dauka a office din ya fita, Abuturrab ya kwantar da yaron ta karasa tana kallonsa tace "Bacci yake ne?" Yace "Noo he is nt sleeping" xata yi kiss dinsa ya dakatar da ita ya nuna mata lips dinsa yace "Instead ni ki min mana" murmushi tayi ta make kafada, ya ja cheeks dinta yace "i will be right back baby" har ya isa kofa ya juya yace "Kar fa kice xa ki daukesa baby baki iya ba" kallonsa take kmr xata yi kuka, ya danne dariyarsa ya dawo yace "Yes mana baby, idan mun haifi namu sai in koya maki ynda ake daukansu, kina son ki yar masu da jariri ne" yana dariya ya kare maganan, ta fashe da kuka, ya hadiya dariyarsa ya ja ta ya xaunar kan kujera snn ya dawo ya dau babyn ya iso gabanta ya sa mata shi a hannu ta karbesa da murna, yace "Toh kar ki tashi har in dawo" tace "Toh" daga haka ya fita yana murmushi, har ya dawo da wata nurse tana rike da yaron gam sai kallonsa take, da ganinta ka ga sabon shiga, yace "Sannu da aiki wife, kinyi kkri" karban jaririn yyi ya mika ma nurse din ya dau allura da xata yi masa ya bata snn ta fita, kmr xata yi kuka tace "I love babies" xaunawa yyi kusa da ita yace "Toh ba nace yau xamu samu namu ba" mikewa tayi da sauri ya rikota yana dariya yace "Ke fa kika ce kina son babies" tace "Ni na mutane nake so" yace "Uhm?

Toh ki fara shirin son naki" Sha biyu suka bar clinic din, ya biya eatery ya siyo take away don bai son tayi wahalan girki ga yan iskan ba ci xa su yi ba, yana gama parking ta bude motar ta fito rike da wasu daga ledojin, shi ma ya fito da sauran, da sallama ta shiga parlon wanda ita ma sai da hakan ya bata mamaki, Suna nn xaune ynda suka bar su, ga plates da cups da suka yi break a gun har lkcn kuma fatima na nn cikinsu, a hankali tace "Sannun ku" bbu wanda ya tanka ta ta wuce ciki, Abuturrab na shigowa ya ajiye ledan hannunsa da mamaki yace "What's all this, kuna nufin tun daxu baku tashi nn ba?" Khaleesat tace "Yaya hira...." Wani tsawan da ya tsorata su ya daka masu, fatima ta tabe baki ta mike ta dau gyalenta ta wuce sa ta fice daga parlon, ya wani daure fuska yace "Before the count of 3 bna son in ga ko wace parasite a nn" mikewa Khaleesat tayi tana murguda baki tace "Toh wai yaya...." Wani ihu ta saki ganin ya yo kanta ta nufi daki gun Small mum dinsu da gudu, Ilham ta bi bayanta har dakin ya bi su, duk suka yi bayan small mum din tasu a tsorace, a fusace yace "Mum wllh xan karya yaran nn a gidan nn idan basu shiga hankalinsu ba, they shud respect their selves idan ba haka ba in yi maganinsu" tabe baki tayi tace "Ni dai kar ku nakasa ni don Allah ku sake ni" yana kallon khaleesat yace "Fita ki kwashe kwanukan nn ki wanke yanxun nn" saukowa tayi daga kan gadon da sauri ta nufi kofan ta fita, yace "Ke kuma tashi ki share gidan gaba daya kiyi mopping, snn ku biyu ku shiga bedroom dina ku gyara ko wani ya kwanan maku a dakin" tashi ilham tayi ita ma tana rabe rabe ta fice da sauri, ya Karasa dakin ya xauna ya gaida Small mum dinsa ta amsa tace "Ina Samhan" xai yi magana sai ga ta ta shigo, ta isa gaban Hajiya Mariya ta durkusa tace "Sannu da gida mum" Hajiya mariya tace "Yauwa Samha har kun dawo" ta gyada mata kai, mikewa Abuturrab yyi ya fita, bedroom dinsa ya shiga yyi wanka ya sauya kayan jikinsa snn ya fito ya wuce daki, Kwance ya ganta yace "Kin gaji ko baby" cikinta ta nuna masa, ya xauna gefenta yace "What happen" a hankali tace "Ciwo yake min" yace "Ciwo kuma?" Ta gyada masa kai yace "Ta ina?" Ta nuna masa gefen cikin, ya sauke ajiyar xuciya yace "Alryt sorry dear, amma ai yana maki hakan koh" ta gyada masa kai, yace "Let me tell you what it is" ya matsa kusa da ita ya duka dai dai kunnenta.
*Haske writers asso*
[11/15, 8:09 PM] 0mmr Farouk:
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
74....
Chapter 80 · 0% Book details