← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 99

Sashe 93

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

an sanda babu man kai suka yarda
, suka kuwa kwashi
afafunsu sai gidan Inna mari bisa kwatancen da Mudan yay musu.
Koda suka isa gidan Maman Ma'aruff taci karo da Inna mari bayan sunyi sallama ta fito dan taga wanene sai cewa tai
Yauwa yalla
ai ga kakarta nan, ku ha
a da ita
Inna mari na tambayar ba'asi aka cukuykuyeta zuwa cikin motar
an sanda, sannan suka kutsa kai suka tattaro Mama gaje dake tsakar gida zaune zataci abinci, iya kuwa ta fita sayo waken
osanta na gobe.
Itama dai kwasarta sukai sai cikin mota, duk da ro
on da take musu da tambaya sun
i saurarenta.
Babu tausayi babu imani mahaifin Mufida yasa aka jibgi su Inna mari duk da tsufanta, sai da sukai musu lilis sannan suka barsu.
Iya na dawowa
an anguwa suka sanar mata abinda ya faru, nan take ta rikice tahau kuka, ta saka aka kira mata
arta a waya ta sanar mata komai, hankalinta tashe tazo gidan ita da mijinta, haka suka bazama neman station
in da aka kai su mama gaje tare da
anin mama gajen shima isa, amma basu samuba har dare, dole suka dawo gida.
Washe garima haka sun fita bin stations suna tambaya, amma duk inda sukaje sai ace ba nanbane, har inda aka kai su inna mari sunje amma ance ba nan bane, a kwana na hu
u sukaga abin yafi
arfinsu sukaje suka fa
a gidansu Ahmad.
Shi Mudan ma ya manta da anyi abun, dan bai sanarma kowaba, koda suka dawo daga Shema, sai randa su Iya sukazo.
Kai tsaye Baba Yusha'u yace shikam babu ruwansa, dan baida ala
a dasu yanzu kam.
Baba Hamza ne ya tsawatar masa akan wannan furuci, ta ya zaice baida ala
a da mama gaje bayan gasu binta, dole Baba Yusha'u yay shiru.
ALLAH sarki Baba Hamza, haka ya tasa
eyar Madan gaba akan suje su bincika suma, su Iya kuma suje gida su huta, amma sai sukace karya damu suje taren kawai.
Da farko Mudan yaso yin yawo da hankalinsu, to amma da ya tuna dashi za'asha wahalar, ga kuma dinkuna jibge a shago suna jiransa ga zuwa makaranta sai kai tsaye ya rakasu station
in da yake da tabbacin su Mama gaje nacan, amma a zuwan dai bashi da tabbas dan kar baba yaci
aniyarsa.
Suna isa kuwa suka iske maman Ma'aruff a wajen.
Su baba sunsha wahala kafin a basu su inna Mari, dan sai da ya saka Mudan ya kira Ahmad a waya suka ha
ashi da d.p.o din wajen, baisan mi Ahmad
in ya fa
a ma d.p.o
inba ya yarda, kuma da yake shi baba tare sukazo a wancan lokacin da aka rufe Samina akan fa
ansu da Basy sai d.p.o
in ya sake aminta da maganar da sukai da Ahmad, nan take ya bada belin su Mama gaje.
Hankalin su Baba ya tashi ganin yanda aka fiddo su Inna mari, jiyay
walla sun cika masa idanu, harya kasa ha
uri sai dai yayma dpo
orafin irin wannan duka da sukaima mata haka, matanma tsoffi kamar wa
annan, musamman ma Inna Mari.
Dpo yayta bama Baba ha
uri akan wlhy shi bayanan komai ya faru, hasalima baisan halin da su Inna Mari sukeba sai yanzu, yay taima
ansandan da sukai abin fa
a tamkar zai cinyesu
anyu.
Su dai su baba sun kwashi su mama gaje zuwa asibiti kamar yanda Mudan ya bada shawara, dan tausayi suka koma bashi, harma yay dana sanin bai tura
an sandan can gidanba.
A asibiti sosai su Inna mari sukaji ciwu
ka, gashi duk sun galabaita, dole dai aka basu gado, tare da taimakon gaggawa, komai Mudan ne ya biya na asibitin, dan sai da aljihunsa yay kankat harya ha
a da cin bashi.
An kwantar dasu tsahon kwana uku kafin a basu sallama.
Daga Mama gaje har inna mari sunsha kuka bisa wannan tashin hankali, dan tun daga wannan lokacinma dai Inna mari lafiya ta gagareta, sai da ta kaita da kwanciya cutar ajali, haka zataita rusar kuka da sambatu, tare da kiran sunan Samina ta yafe mata, sai dai ina Samina batajinta, hasalima tana
aya daga cikin wa
anda Saminar tafi tsana a yanzun a duniya.
Takai kusan watanni uku tana jiyya ALLAH yay mata rasuwa.
Wannan mutuwa ce ta kuma susuta mama gaje, lamarin da ake tunani na ta
uwar hankali ya sake bayyana a gareta, dan itama haka kawai saita kama surutai, kokuma tai zaune jugum ba im ba im-im, saita ha
a kwana biyu bataima wani magana ba, komai sai dai tayita binsa da idanu.
A lokacin Ahmad har waya yasa aka bata yay mata gaisuwa, sai dai ko Umm-Ruman bai sanarma rasuwarba, dan tana fama da laulayin cikin Abu-Talib lokacin.

angaren su Ma'aruff kuwa sai komai ya koma yay lif, dan mahaifin Mufida ya fahimci bazasu sami abinda sukeso ga Ma'ruff ta wannan hanyarba, dole ya tirsasa Mufida ta koma lalla
a Ma'aruff.
Sai dai lalla
awar sam batai amfaniba, dan shan giyar da yake ta kuma
aci sosai, Har takai hantarsa ta ta
u ba tare da kowa ya saniba, a tsaitsaye ya fara ciwo tamkar wasa, tun yana
aukar lamarib ba komaiba har abun ya kaisa ga kwanciya, dukda mufida tasan baida lafiya ta
i fa
ama mamansa ta kuma
i taimakonsa zuwa asibiti, saima takurama rayuwarsa da tai da batun
akko takardun nan.
Jikin Ma'aruff yayi matu
aryin tsamari, har takai ranar ya gaza a yin komai yana
aki kwance rijib, yanaji wayarsa na ring tunda farar safiya amma ya kasa
auka ya duba wanene mai kiran, gashi sam baiji koda motsin Afrah ba a gidan balle na Mufida.
Hawaye masu zafi suka gangaro masa a kumatu, inda zai iya da tuni ya
auki wayarnan ya kira Mominsu ya shaida mata halin da yake ciki ko zai damu taimako daga garesu.
Har kusan azhar babu motsin Mufida, hakanne ya tabbatar masa bama ta gidan, koma bata kwana a cikinsaba, dan tun jiya da magriba dama yaji kamar motsin fitarta, daga nan bai sake jinta ba, to duk zatonsa kodan yayi barci da wurine harta dawo bai saniba, sai dai zuwa yanzukam yaji a ransama bata dawo ba tun jiyan.
Jiyo knocking
ofar da ake da
arfine ya katse masa tunaninsa, dagaji dai ba bugune na lafiya ba, gashi duk yanda yaso tashi ya gaza hakan, kuma yana tunanin Mufida kullesa tayi....
Bai kai
arshen tunaninsaba ya jiyo maganar mai gadi sama-sama yana fa
i musu anya kuwa yana nan?.
Sai kuma ya jiyo maganar Mominsu kamar tana kuka, ya rimtse idanunsa zuciyarsa na sake salon bugu, dan kuwa dai tabbas yaji a jikinsa babu lafiya......
Maganar
anwarsa data zagayo ta bayan Window
akinsace ta sakashi jin sassauci, ta shiga sallallami ganinsa kwance a gado da alamar yana cikin mawuyacin haline, da gudu tabar wajen tana
wala kiran sunan mominsu da tabbatar musu yana ciki kwance.
Nan take suka fara
arin
alle
ifar, cikin amincin ALLAH suka sami nasara da taimakon baba mai gadi.

Yanda suka shigo suka iske Ma'aruff ya kuma birkita dukkanin tunaninsu, suka shiga share hawaye da jera masa tambayoyi, sai dai bai iya basu amsar ko guda
ayaba shima, sai binsu da kallon tsoro yake ganinsu duk da raunuka a jiki an li
e da bandeji.
Babu maganar jan dogon zance sukai
arin cewa a kaisa asibiti, duk da sunsan basu da ko sisin kwabo tare dasu, amma suna tunanin shi
ila a samu wani abu a accaunt
insa tunda da alama su Mufida basu ta
a komai na nan gidanba.
Ramar da yayice ta saka suka iya
akkosa su uku ba tare da sunji wani uban nauyiba sam, suna shirin sakashi a motane wata motar tai hon, hakan yasa Momi cewa maigadi yaje ya bu
e gate yaga wanene?.
Babu jimawa sai ga baba maigadi ya dawo a ki
ime, momi ta shiga tambayarsa ko lafiya?.
Yace,
Hajiya wlhy wai wasune sukazo suke maganar nan gidansu ne
Cikin matu
ar razani
annen Ma'aruff da Mominsu sukace,
Gidansu kuma?!

Wlhy kuwa hajiya, gasu nanma zasu shigo......
Babu wanda ya iya cewa uffan a cikinsu har mutanen suka
araso, sai wani cika suke da batsewa.
Su dai su Momi sun zuba musu idanu kawai.

aya a cikinsu ne ya fara bayani ko gaisuwa babu balle lura da halin da Ma'aruff yake ciki baiyiba,
Hajiya mune wa
anda suka sayi gidannan, kuma hajiyar da suka sayar mana sun tabbatar mana kafin muzo kun tashi, amma kuma sai gashi mun iske sa
anin hakan
Baki bu
e duk suke kallonsu, cikin
annen Ma'aruff
aya ta samu baki fa
in,
Hajiya kuma? Wace hajiyace ta saida muku gidan bayan ga mai gidan nan shi baisan anyiba?
Kallon juna sukai suma,
aya yace,
Bamu gane mi kuke nufiba?, to mudai Hajiya mufida sunanta, kuma ita da Mahaifinta suka kawomu mukaga gidan sati uku da suka shige, tun a ranar muka biyasu rabin ku
in, jiya kuma muka cikasa biyasu sauran suka bamu takardun gida yau
innan da safe
Baya kawai momi tai ta yanke jiki ta fa
i a sume, nan take hayaniya ta kaure.
Ma'aruff ya amshi takardun da
yar ya duba, tabbas takardun gidanne, to amma a garin yaya sukaje hannun su Mufida bayan yasan suna gidan momi?.
Bai samu amsaba saboda tashin hankalin da suke ciki, masu gida kuwa sallama sukai musu suka tafi akan sun basu nanda sati guda su kwashe komansu su basu gidansu suna bukata.
Babu wanda yabi ta kansu, dan suna a ru
anin da baki bazai iya furtawaba sam.
Chapter 93 · 0% Book details