← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 99

Sashe 18

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

an kayan da Ammin Rumana ta fara tarawa na auren Rumana
in aka fiddo ake
an wankewa, dukda bana kirki bane zasu taimaketa ko yaya dai.
Duk bikinnan da akeyi fa Samina na gidan, saboda ta nuna abinma bai dametaba komanta yinsa take kai tsaye a gadarance a gidan, hakama Mama gaje, har dariya takema Ammi akan ha
in auren Rumana da Ahmad, wai saji sa gani, nan za'a ringa
ullar tuwo a kwano ana wucewa dashi gidan Rumana, dan sunsan dai Ahmad bashi da abinda zai ri
e Rumana.
Babu wanda ya kulata akan zancen, dan kowa kwllon wawuya yake matama yanzu, daga ita har
ar tata.
Gefe kuma ga munafukan
oye irinsu Umma (Sailuba uwargidan baba Iliyasu, aminiyar Mama gaje a gidan idan baku mantaba) dan tana
aya daga cikin mai tunzura mama gaje da Samina akan auren Ahmad, bayan itama akwai sangamemiyar budurwa a gabanta Salima, dan sa'arsu Rumana
ince, tarema suka tashi su uku tamkar tagwaye, Umm-Rumana, Fa'iza
anwar Ahmad, sai Salima
Ayyah da bataga giccin Ahmad ba tunda aka dawo
aurin aurene abin ya dameta, dan haka ta aika a duba matashi ko yana
ofar gida wajen abokansa.
Koda Abu yaje ya tambayi su Rabilu sai sukace aisu tunda aka dawo daga
aurin aurenma basu sake ganinsaba, sun zata yana cikin gida yana wani abun.
Babu shiri Ayyah ta fito zuwa
akinsu Ahmad, saita iskeshi yanata rawar
ari a bargo, hankalinta ya tashi sosai, tasaka Abu ya kira mata Baba Hamza.
Tunda baba yaga halin da Ahmad yake ciki sai tausayinsa ya kamasa, sunata jera masa sannu shi da Ayyah, a
oye ba tare da kowa ya saniba Mudanseer ya kira wani mai aikin asibiti anan kusa dasu ya duba Ahmad
Bai
oye musuba ya sanar musu damuwace tai masa yawa, shine harta haddasa masa zazza
i, dan baya samun isashshen barci ma, ga malleria kuma a gefe itama.
Magunguna ya basa, yace yaci abinci sannan yasha ya kwanta danya samu isashshen barci.
Har Ayyah ta kawo masa fura yasha da
yar, zata bashi maganin baba ya dakatar da ita akan ta barshi ba yanzuba, tunda likitan yace akwai na barci su
aga
afa zuwa anjima, dan Malam yace yau za'a kai Rumana, to kenan bayasha magani yay barci a nanba kuma, bayan an kaita sai yasha yatafi can ya kwanta.
Dole Ayyah tabi wannan umarni na mijinta, suka bar Ahmad, sai dai ruwan
umi da aka kawo masa yay alwala yay sallar magriba da isha duk a
aki, lokacinne kuma Ayyah ta sawo Gwaggo gaba a
oye tazo ta duba Ahmad
Sannu tai masa sau
aya ta
auke kanta sai kace bata damuba, nanko ranta sai suya yake da halin da yaronta ke ciki, amma kawaici ya hana agani koda a fuskartane.
Kusan
arfe tara aka mika Rumana da tasha kuka tamkar hawayenta zasu
are
akinta, tasha nasiha a wajen iyayenta da dangin mahaifiyarta, malam ya bata
yautar da ko ita batasan minene a cikiba, hakama Iya ta bata.
Duk wanda yaga yanda take kuka saita bashi tausayi.
Haka suka mikata, basu wani jimaba suka barota tana cigaba da shar
ar kukanta.
Tunda Ayyah taga
an kai amarya sun wuce tazo ta tada Ahmad, da
yar ya iya tashi ya watsa ruwan zafi da Ayyah ta
umama masa, Abu yakai masa bayi, bai wani jimaba ya fito, jallabiya kawai ya bukaci a basa ya saka, dan haka Mudan ya fesheta da turare sannan ya bashi.
Baice komaiba ya saka, Ayyah tai zaman lalla
ashi yasha magani, da
yar yasha kuwa yana tsuke fuska da yamutseta, harda yun
urin amai saboda tsanar da yayma magani.
Suka dai samu ya ha
iye duka da kyar.
Nasiha Ayyah ta sake masa da baba, kafin Mudanseer ya rakoshi inda Sufyan ke jiransa da mashin.
Shine ya
aukesa ya kaisa gida, kafin suje sai rawar sanyi yake, yanata sake
udundune hannunsa a
irji, ga jiri na
ibarsa sabida rashin
warin jiki.
Dole Sufyan ya taimaka masa har cikin gida, yay sallama a
ofar
akin Umm-Rumana da har lokacin take zaune tana kuka ta amsa.
Izinin shiga Sufyan ya nema, ta bashi sannan ya shiga ri
e da Ahmad cikin
akin.
Babu shiri ta mike tana kallonsu a firgice, dan sam batasan Yah Ahmad baida lafiya ba, da taimakon Sufyan Ahmad ya kwanta saman gadon, Sufyan ya mikama Rumana ledar maganin Ahmad da kazar da suka saya musu da lemon
awo sai kankana.

Amarya kiyi hakuri, angonki ya shigo miki ba yanda kowanne ango ke shigoma amryaba, bashi da lafiyane, muna fatan zaki kula mana dashi nanda kwanaki ka
an ya dawo mana Ahmad
insa jarumi mai yawan juriya da kowa ya sani, ALLAH ya baku zaman lafiya da zuri'a
ayyaba, ya kara muku hakuri da fahimtar juna, ya dasa muku soyayyar juna a zukatanku mai karfi daban mamaki da kwatance ga ma'abota soyayya
Itadai kanta a kasa tana hawaye bata iya bashi amsaba, ya juya ya fita yana fa
in ta rufe
ofar shi ya wuce.
Sama-sama Ahmad ke jin Sufyan harya fice, daga bayama barci mai
arfi yay awon gaba dashi.
Har lokacin Rumana na tsaye tana hawaye, sai da taji tsayuwar ta gundireta ne ta ajiye ledojin hannunta ta nufi
ofar ta rufe addu'a
auke da bakinta kamar yanda mahaifiyarta ta koyar da ita.
Zama tayi kawai ta zuba masa ido tsawon lokaci, tausayinsa na sake ratsa zuciyarta.
Itama kantane ke mata azabar ciwo, dan haka ta lalla
a taja bargon dake saman gadon ta lullubama Ahmad data lura yana rawar
ari, tana sakawa kuwa taga yajashi har saman kansa ya sake kudundunewa da
yau, ajiyar zuciya ta sauke tausayinsa na sake kamata.
Tsawon lokaci tana wajen har ta farajin saukar numfashinsa ya canja alamar barcinsa yay nisa sosai.
Tasan dolene a tausayama Yah Ahmad, dan halin da yake ciki abin dubawane, akwai tashin hankali abinda ka girma dashi a zuciyarka yazama shine sanadin rusa dukkan farin cikinka a dare guda.
Sabuwar tabarmar dake a
akin ta dauka ta shinfi
asan ledar da aka saka a
akin ta kwanta ba tareda ta saka koda zaniba, sai filo data
auka kawai a gado saboda bata iya kwanciya babu shi.
Gyalen jikinta ta rufa dashi dukda bashi da wani kauri sosai.
A haka taci gaba da kukanta har itama barcin yay nasarar saceta, ga kanta yana sara mata sosai da ciwo.
_______________________________
A wannan darenma Samina da Ma'aruff sunsha hirarsu ta masoya, inda mafi yawan firar duk ta karkata wajen tsara yanda shagalin bikinsu zai kasance.
Da
i tamkar zai narkar da ita, sai wani lumshe ido take tana dafe
irji da washe ha
ora, har yanda take bu
atar lefenta ya kasance da kalar akwatunan da takeso da kayan gidan dazai zuba mata duk sai da ya tambayeta, sai events na garari na nunawa a gidajen tv da social media shima duksun tsara abinsu.
Cikin shagwa
a take shaida masa yafayi ta turo manyansa, dan ita yanzu dukta tsani komai na gidansu, sotake ta kara gaba tabarsa kodan
an bani na iya.
Daga can Ma'aruff yay murmushi yana fa
in,
Karki damu gimbiyar mata, ni kaina na kagara na jiki a jikina lafe, ina baki gangariyar soyayya da babu sirkin ruwa a cikinta, burina kawai mallakarki tunda kinki bani damar hakan tun a yanzu, kince sai munyi aure, niko nayi biyayya na ha
ura har a
aura a kawomin ke babie

Oh ni kana bani kunya, gara dai kayi ha
uri harnazo, dan saboda na faranta makane ma nai duk abinda ya dace kar wancan shashashan ya sameni, dan ka
an daga aikinsa ya kwata cikin
arfi, niko kai ka
ai nake burin cikama al
awarin kawo maka budurcina har gida

Nagode ta wajena, shiyyasa nake
ara jin sonki na
aruwa a raina a kowacce da
a, dolene nazo na samu su baba ayi komai da wuri, insha ALLAHU nanda karshen wata kina nan kwance a
irjina
Yanda yay maganar da wani irin salone yasaka tsigar jikin Samina tashi, ta sauke nannauyan numfashi daya sake haukatar da Ma'aruff daga can, hakan yasashi kuma manne karuwarsa dake barci a jikinsa, dan saida ya gama holewarsa ne ma ya kira Samina

Sai da Safe
Samina ta fa
a a sanyaye saboda kasalar da ya sakar mata da kalamansa.
Shima da
Uhmm
kawai ya iya amsa mata ya yanke wayar yana sake maida karuwarsa a network.
Haka Samina tai barci da
unbin begen abokin hakittarta, dolene ma tai yadda zatai ai aurensu da Ma'aruff a nan kusa, koba komai ta samu nauyin shekaru dake gallabarta ya fita. A shekarun da suka shu
e Ahmad kawai take iya suffantawa da wannan yanayin, amma zuwa yanzu sam ba haka bane.
Wani gefe na zuciyarta yace yanama can yana hutawa da kanwarki amaryarsa kuma Rumana.
Baki ta ta
e tana jan tsaki, sai kuma
ayan gefen zuciyarta ke shaida mata sam Ahmad bazaiyi hakanba, dan tafi kowa sanin halinsa idan ka
ebe iyayensa, dan ko
an uwansa tafisu sanin wanene Ahmad akan abinda yake so, tasan kafin Rumana ta samu gane kan Ahmad za'a yara, dan soyayyarta ta riga ta masa
ullin ya
on wake a gona, kafin zuciyarsa ta fara kallon Rumana matsayin mace sai anyi babban dagama...............
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
_**ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*(11)*
............Kiran sallar farko Ahmad ya farka, zazza
in ya sauka masa, sai dai akwai ciwon kai ka
an-ka
an, sai nauyin jiki da yakeji.
Chapter 18 · 0% Book details