← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 99

Sashe 27

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Barshi zan zuba kawai
Yay maganar yana bu
e kular abincin.
Dole Rumana ta koma ta kwanta, Ahmad kuma ya zubama kansa a binci a filet
in da Umm-Ruman ta ajiye.
Sai ya samu kansa da yawan kallonta, ka
adan idonsa sai ya kai gareta.
Rumana kuwa barcin wahala ne yay gaba da ita ba tare da ta shiryama hakanba.
Maman Ama dataji shiru sai ta kama gyaran murya, da fa
in,
Sannu amarya kinji
Ahmad duk yana jinta, amma sai yay kunnen uwar shegu da ita, jin an
i bata amsa taja
afafunta ta koma
aki.
Koda na farka bayan la'asar kaina kawai na gani a
akin, babu kayan da ya yanka, sai kular da abinci kawai ke ciki da kofin ruwa, filet da
aramin kofi da yay amfani dasu ma can na hangosu ya saka a robar da nake tara wanke-wanke.
Sakkowa nai daga gadon, dukda har yanzu ina
anjin zafin amma ba kamar
azunba, takarda dana gani sa
ale a hannun kofin ruwan na zare ina warwarewa.
_Idan kin tashi kici abinci, ga maganinan kisha kuma._
Iya abinda kawai aka rubuta kenan a jiki, nai murmushi kawai, a raina nace da mijin Novel ne bazaije ko inaba saina tashi, ya bani abincin da kansa da maganin,
ilama har wanka zai mini.
Ayyana hakan da nayine ya saka ni tuna yaya Samina, sai nayi saurin fa
ALLAH ka ciremin wannan ragon tunanin a raina, dan kuwa suma marubutan suna saka wani abunne kawai dan nisha
i, wani abun kuma dan
ara ilimi da gyaran zaman takewar aure, amma ga irinsu yaya Samina nan mai makon su duba abu mai muhimmanci su
auka a ciki sai suka
aura rayuwarsu bisa mara muhimmancin, na tuna randa naji tana fa
ama mama gaje itafa auren irin mijin Novels shine burinta, kuma sai ta cikashi, maimakon naji mama gaje ta kwa
eta sai cewa tai shi mijin novel
in yaya yake ne? Samina!.
Ina jiyosu Yaya Samina na bata labari tiryan-tiryan na wani littafi da take karantawa suna dariya.
Na girgiza kaina kawai ina murmushi, daurewa nai na fita
auro alwala.
Maman Ama dake jan ruwa a rijiya ta kalleni, sai naga kamar fuskarta babu fara'a, amma sai ban kawo komaiba, sai dai kuma maganar da tayice ta sakani kallonta.

Oh ni Amarya sai yanzu aka tashi?
Murmushi na mata,
Wlhy kuwa Maman Ama bansan barci ya kwasheniba, ashe har anyi sallar la'asar

Ina kuwa zaki sani, daga gyaran ciwo an koma soyayya, ni shiyyasama na fito na baku waje, dan naga kun manta dani a
akin. dama su maza idan kana amarya ai jinka suke kamar
wai a cokali, sai an fara haihuwa
aya biyu sai labari ya canja salo
ta
are maganar da
yalewa da dariya tana cigaba da fa
in,
Muma fa duk anmana mafiyin ma wannan tarairayar, shiyyasa da ake muku yanzu sai muga abun kamar maimaici
Murmushi kawai na sake iya yi mata, nace,
ALLAH sarki
kawai nai wucewata bayi.
Duk da Maman Ama ta girmeni, kuma rayuwar gidanmu ba irin haka bace, ba kuma wasu
awayene daniba bayan su Fa'iza na fahimci alamar jin haushin kulawar da Yah Ahmad ya nuna a kaina cikin maganar maman Ama, sai kuma yanzune zuciyata ta sake gane yawan tsogumi da maman Ama keyi akan amaryar gidan, dan taga mijinta na bata kulawa, to ALLAH ya
yauta, ashe shiyyasa yaya Ahmad yaymin garga
azun.
A bayin ma nayo alwala ta dankar na tsaya wajen nazo na gittata tana
ibar ruwa da yin wakar barmani choge.
Wuceta nai kamarma na manta da ita a wajen na koma
aki.
Koda na idar da salla duk yanda yace nayi haka nayi, bayan nasha maganin na gyara
akin sosai dan
azun bawani gyara mai kyau nai masaba saboda yah Ahmad, turaren wuta na tsinke na kunna a
akin, na
iba ruwa naje waje nai wanke-wanke.
Ina cikin yine Amaryarmu ta fito rakkiyar mijinta da alama fita zaiyi, sunyi gayunsu abin sha'awa, har soro ta rakashi sannan ta dawo.
Inda nake ta nufo, hakan yasa nai mata murmushi, ba wata babba bace itama, da alama dai irin sakin wawan nanne, baka da
e da auren farkoba a sakeka.
Ta zauna saman rijiyar tana fa
in,
Kuyi ha
uri bamuyi gaisuwa da kowaba a gidannan irinta sanayya
Cikin fa
a murmushi nace,
Ayya ai babu komai, keda kikazo jiya da dare, ai ya kamata amiki uziri
Sosai tai dariya, sannan muka gaisa, tace,
Ni sunana Kausar, kefa?
Nace,
Kausar suna mai da
i, ni kuma Umm-Rumana

Woow Nice name
ta fa
a cike da iyayi.
Ni dariyama ta bani, dan haka na dara ka
an, sai ga Maman Ama dake wanka ta fito tsilim tana cewa,
Mi ake tattaunawa haka amaren gidanmu?
Mu duka kallonta mukayi muna cigaba da dariyarmu, ni dai bata samu amsa a wajena ba, sai Kausar ce ta bata amsar.
Yanda Maman Ama ta nuna son Kausar sai abin ya bani amamaki, wato dai matarnan kwararriyar
ar barikice, koda ta shiga
aki kayan
walliyar waje ta
ebo ta dawo dasu, ta zauna a kujera
ar tsugguno, a haka aka cigaba da hira, wadda su biyune keyi, iyakata dariya kawai, saboda firar ta koma akan abinda yafi
arfin girma na ne.
Har Kausar na fadin miyasa ni banson cewa komai?.
Nanma dariyar kawai nayi, sai maman Ama ke cewa
Ai indai amaryace haka take, inaga batason bamu nata sirrin
Nace,
Maman Ama ni wane sirri gareni, ai sai dai ku manyan yayye
Da haka na mi
e ina share ruwan wajen, kausar tai dariya tana bani amsa da cewar,
Kema kin shiga layin manyan ai tunda har aka kawoki
akin miji
Maman Ama tai saurin cafe zancen
Kema dai
ya fa
a Kausar, koda yake itafa
ar gatace, angon nata rainonta yakeyi har yanzu, kusan sati uku kenan da aure kuma
Kausar tace,
Tab, dama har a wannan zamanin akwai waliyan maza irin wa
annan da suka rage? Ballema saurayi da kamar ji suke su
wata tun a waje?

Aiko dai gashi an samu a gidanmu kausar, nima dai ina jinjina
arinsa, mu
an zamanin shekaru kusan takwas ma ba'a
aga mana
afaba balle na yanzun?, randa aka kawoni gidan da muka fara zama ALLAH tun farkon dare baban Ahmad yana gida, kamar jira yake
an kawoni su wuce ya hau sassafata
Dariya suka kwashe da ita, ni dai na
auki ruwan wankana na nufi ban
aki ba tare dana ce dasu uffanba.
Ina jiyosu suna cigaba da hirarsu wadda ni kunyama take sani dukda bana a kusa dasu, dan Maman Ama tiryan-tiryan take zayyanoma Kausar daren farkonta, itama tana fa
a mata nata suna kwasar dariya.
A haka nazo na shige
akina ina
ingisa kafata mai ciwo.
Ban sake fitaba duk da ina cigaba da jiyo hirar tasu kuwa, wadda naga tayi zurfi sosai dan har maman Ama tafara kiran ta shiga
ari lokaci yaja bata dora abincin dare ba.
Kausar take cemata
Kai dama zakiyi abinci kika biyemin, tashi ki
ora kam gaskiya dan mu saimun gama cin amarci, Amarya dai tunda ta shige tai bulum a
Dariyar maman Ama na jiyo tana bata amsa da
yaga da yawa indai amarya ce, sam bata gajiya da
umshe kanta a
aki kamar wata maijego

Zata barine, har yanzu da sauranta ne ai
cewar Kausar.
Ni dai ko tari banyiba balle susan yaya nake.
______________________________

angaren Samina kuwa a hankali Ma'aruff ya fara cin galaba a kanta, yanzu kam babu fashi duk randa yazo hira wajenta saiya moreta da Romance, tun tanajin tsoro har itama idonta ya fara bushewa saboda jin da
in hakan da takeyi, dan zuciyarta ta yarda da Ma'aruff
ari bisa
ari akan bazai cuta mata ba, a ganinta tunda aure zasuyi kuma ai babu wani abu, da yaje yayi da wata kamar yanda ya fa
a gara yayi da ita tunda kowa yasan akwai maganar aure a kansu.
Ku
i kuwa da sayayya ya kara haukacewa da yi mata, hakan ya
ara saka izza da dagawa a zuciyar mama gaje da Saminar kanta, kullum cikin yima Ammin su Rumana da su Ayyah habaici ake, haka zasuyita ciye-ciyen kayan da
i gaban su Ammin Rumana, amma ko guntu ba'ai musu tayi.
Duk abinda ke faruwa baba Yusha'u ya sani, ya ta
a ma Samina fa
a sau
aya akan shiga motar Ma'aruff, amma sai malam Rabi'u mahaifinsu yace karya
ara ya sakama Samina da uwarta ido kawai. Saboda a randa yay maganar tujara sosai Mama gaje ta zubar a gidan, har su malam
in sai da ta zaga babu kunya babu jin tsoron ALLAH.
Komai kuwa a kunnen Ahmad dake gidan yazo gaida su Ayyah ya faru,
ala bai ceba akan zancen, daga
arshema ya baro gidan kawai.
Zuwa yanzu takai karatun Samina ya fara walagigi, dan bata da burin daya wuce Ma'aruff yazo ya
auketa a mota su more rayuwarsu da shan minti, hakan yafiye mata zaman aji muhimmanci.
Kowa ya kawo ido ya zira mata, yayarta Bintu da iya kishiyar kakarta Inna mari ne kawai ke fa
ama Saminar gaskiya, sai dai sam batama saurarensu, saboda a yanzu duk mai fa
a mata gaskiyar kallonsa take ma
iyinta, mai ba
inciki da cigabanta kai tsaye.
Gefe kuma zugar su Nafy akan haduwar Ma'aruff na sake tunzurata da zuzutata a
aunarsa.............
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*(17)*
..............Harna fito alwalar magriba basu tashi a wannan hira ba, dan maman Ama ma tana kicin ne tana girkin dare.
Ni dai nai alwalata na shige
aki ina tsokanar Amatullah dake barbazamin duwatsu a
ofar
aki tana wasa.
Basu tashi ba sai gab da isha'i, shima mijin kausar ne ya shigo, sai lokacin naji wai tana fadin ta shafa'a batai sallar magriba ba.
Ni dariyama ta bani, shiyyasa na
an murmusa ina cigaba da azkar
ina.
Yah Ahmad bai dawo gidanba sai goman dare, na tashi daga kwanciyar da nai ina amsa masa sallamar sa, ledar hannunsa ya ajiye idonsa a kaina.
Chapter 27 · 0% Book details