← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 99

Sashe 21

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wai Salima yaushe kika koma hakane? To ALLAH ya gyara lamarinki da wuri, kema dai na kula auren kikeso
Fa'iza tai saurin fa
in,
Mi takeci na baka na zuba, Wlhy Malam yace muma mu kawo mazan aure, wai muna gama jarabawa aure za'ai mana, abinda Yaya Samina tayi ya tada hankalin kowa, bazasu sake yarda
ansu suyi zurfi a karatuba sai dai idan mijinka naso ya kaika da kanshi
Cikin marairaice murya Rumana tace,
Kuma godema ALLAH kuda gashi zaku
arasa, ni kam nasan ai nayi kenan

Karkice haka wlhy, tunda Yah Ahmad nason karatu zai barki ki
arasa, ALLAH dai yasa kar bebin mu yay shigar sauri kawai
Hararta Umm-Rumana tayi.
Suka sanya mata dariya.
Daga nan suka koma hirar Samina, tare da iskance-iskancen data tsuro dasu a gidan a safiyar yau.
Rumana tace,
ALLAH ya
yauta to, ALLAH ya shiryeta
Amin dai, su Fa'iza suka fa
a a tare.
Su Fa'iza na gidan har Sadiya da Na'ima
anwar Rumana suka kawo abincin rana da
an tarkacen kwanika da aka
ara saima Umm-Rumana, harda
aramin risho da abin gawayi, sai Abu dake biye dasu da
atuwar jakkar Ahmad ta kaya da tarkacensa.
Sannu Rumana tai musu, suma suka zauna aka
alle hira, Abu nata zuba musu shirme suna kwasar dariya, yaran anguwa kuma nata shigowa jefi-jefi ganin
akin amarya, harma da mata ma
wafta
an gutsiri tsoma, dan yanda auren ya kasance duk ya shiga kunnensu.
_________________________
Ahmad kuwa koda ya fita dauriya kawai yakeyi, dan bayajin
arfin jikinsa sam, ga zuciyarsa har yanzu a cunkushe take, kansa kuma bai daina masa ciwo ba.
A majalisar abokansa ya fara yada zango, ya zauna suka gaisa yana sake musu godiya, sukuma suna tambayarsa jikinsa da amarya.
Yaja kusan minti talatin a wajensu kafin ya mi
e ya
arasa gidansu, sashen su Malam ya fara shiga suka gaisa, Malam nata saka masa albarka, hakama tsoffin da aka bari
an shema su hu
u da Iya, ya
an da
e anan ma, ya fito yana murmushin
arfin hali na tsokanarsa da sukeyi irin dai wasan jika da kaka.
Sashen Baba Ilyasu ya shiga, ya gaida matansa sannan ya fito zuwa Sashen su Rumana.
A tsakar gida ya iske Ammi da Mama gaje, kowa na hidimarsa, ya risina ya gaidasu tamkar yanda ya saba, Ammi ce kawai ta amsa masa cikin jin nauyinsa da batayi da, Mama gaje kuwa
aki ta shige bata amsashiba.
Bai damuba ya mi
e ya fito abinsa.
Ya shiga sashensu,
an biki duk sun kama gabansu, sai
anwar gwaggo kawai data rage bata wuceba inna Asma'u.
Da Ayyah ya fara cin karo a tsakar gida suna
arin kwance zare a
afar
aya daga agwaginsa ita da Mudan.
Ya
arasa gabansu yana fa
in,
Ayyah miya sameta ne?

Wlhy
an albarka zarene ya sar
afarta, gashi nama lura kamar
afar tata ciwo take tun jiya wajen taron nan, to ALLAH baisa nasamu kamata ba suka fice sai yanzu abun ya fa
omin arai, shine nashiga nemanta sai kuma na ganta jikin kejin kajincan a takure kamar wadda aka
aure, ashe zarene ya dabai baye
afar

To, bai dai ji mata ciwo ba ko?

Eh bai jiba, amma Yaya ina ganin gara a saidasu kawai, kwanan nan naji ana maganar agwagi suna fama da murgwi, na gidan malam kalla sai mutuwa suke suma
. Madan dake maganar ya fa
a idonsa akan Ahmad.
Ahmad yace,
To Mudan saika cigita mai sayen muga idan zasu
anyi daraja, amma abar guda biyu, dan nagama wata fara mai yarfin ba
i kamar
wai takeyi
Ayyah tace,
Ai naga kamarma fa ta fara
yasa da safenan indai
ar budurwar nance...
Kafin Ahmad ya bada amsa Inna Asma'u ta fito daga
akin Gwaggo ri
e da kayan wankin Gwaggon.

A'a, ango
an gidan Ayyah ne a gidan? Jiki yayi sau
i kenan?
Maida hankali gareta Ahmad yayi, ya taka zuwa inda take yana risinawa ya gaisheta, ta amsa cike da kulawa tana tambayarsa jikinsa.
Ya amsa da cewar da sau

To Alhmdllh, ai haka muke son ji, Ina
iyar tamu amaryar
amshi?
Kansa ya kuma sunkuyarwa ya amsa da cewar,
Tana lafiya itama
Daga haka ya mi
e ya shiga
akin Gwaggo.
Tana zaune Zainab dur
ushe gabanta tana cire mata abu a ha
ori, sai yarfa hannu take tana kukan shagwa
a na autanci.
Zama yay yana kallonsu, Gwaggo da sallamarsa kawai ta amsa ta bige hannun Zainab dake ri
e nata,
Idan bazaki tsaya ba tashi kiban waje, ji iskanci saikace ina cire miki rai

ALLAH Gwaggo da Zafi fa
Zainab tai magana tana share hawaye.

To jeki kicire da kanki mana

Yi ha
uri to zan tsaya ALLAH kuwa
Zainab ta bama Gwaggo amsa.
Ahmad dake kallonsu baice komaiba ya lumshe idanu yana cewa
Ina kwana?
Amsawa Gwaggo tayi kamar yanda ta saba masa, sai dai ta tambayi yaya jikinsa da Rumana?.
Yaji da
i sosai, ya amsa mata murya a raunane.
Ita dai sharesa tayi, duk da kuwa
unbin tausayinsa da ga shi har Rumanar nacin ranta.
Shiru babu wanda ya sake tankama wani, har Gwaggo ta gama cirema Zainab ha
orin makka data sa ya ma
ale ya
i fita, tashi yay ya fito da ga
akin yaje
akin Ayyah suka gaisa itama.
Sai jero masa tambayoyi take akan jikinsa, yay murmushi saboda ganin yanda damuwa ke kwance a fuskarta, kwanciya yay a gadonta dan wani sabon zazza
i yakeji.
Ayyah dake kallonsa ta
ora hannunta saman goshinsa tana fa
in,
an albarka wani zazza
inne fa? Anya kasha magungunanka?
A hankali yace,
Nasha Ayyah, bani bargo sanyi nakeji
Babu musu ta
akko Bargo ta rufa masa, ahaka barci yay awon gaba dashi.
Sai da aka kira sallar zuhur Ayyah ta tashesa dan yayi salla, yay alwala ya fito shi da Mudanseer, a soron gidan sukaci karo da Samina taci kwalliya zata fita, kallo
aya yaymata ya
auke idonsa, hakan yasa taja siririn tsaki.
Kasa jurewa Mudan yayi yay saurin kallonta yana cewa,
K da ubanwa kike?
Baki ta ta
e tana tauna cingam yay
ara
as tai fari da idanu,
Da wanda ya tsargu man....
Bata kai
arsheba ya sauke mata mari, zai
ara na biyu Ahmad daya juyo ya kallesu ya dakatar dashi da fa
in,
Kai wuce muje mana
Samina kuwa sai ta fashe da kuka dafe da kunci, da gudu ta juya cikin gida tana kwalama mama gaje kira.
Ahmad sun dawo salla suka iske marin da Mudan yayma Samina ya zama Hayaniya a gidan, dan kuwa mama gaje hannun Samina ta kamo har sashen su Ahmad akan bazata yarda ba, wai Ahmad yasa Mudan ya daki Samina.
Gwaggo uffan bata ceba, sai Inna Asma'u ce ta tanka, sai ko Ayyah data idar da salla itama ta fito ta taya inna Asma'u, nanko abu ya zama hayaniya Mama gaje nata daddatsa magana wa jama'ar gidan, har Malam da Iya bata bariba, Ammin Rumana kam ai tafi kowa shan Zagi da su Ayyah.
Ahmad ya ra
a ta gefensu ya shige
akin Ayyah ya sake kwanciyarsa, ko kallon
aya a cikinsu baiyiba.
Hakan da yayi ba
aramin ciwo yayma mama Gaje da Samina ba, dan sunso ya tanka su hau kansa.
Mudanseer kam cayay inhar Samina bata bar sashenba wlhy dukan mutuwa zai laka
a mata, abinda ya
ara rura hayaniyar kenan, Gashi su baba basa nan, sai da Iya ta shigo tai magana su Ayyah sukai shiru, Mama Gage kam ai kamar tunzurata akayi, taita zuba tsiya har sai da ta gaji tai shiru dan kanta............
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*(13)*
..............Koda Ayyah ta shigo
aki nasiha tai tayima Ahmad akan wannan sabon lamari da ya shigo musu cikin gida.
Ahmad dake jin zazza
i yace,
Karki damu Ayyah, ni wlhy abunsu bai damuna, dan ALLAH kuma kubar biye musu, shima Mudan
in zan masa magana yabar shiga harkarta, tunda bata da kunya, duk yanda yake tunanin da da yanzu akwai banbanci

Humm su dai suka banbanta da son zuciyarsu
an albarka, indai duniya ce kuma gasu gata nan, wanda ma bai zoba jiransa takeyi, wanda kuma duk yasai rariya yasan zata zubda ruwa, ni lalacewar wannan aurenma tsakaninka da yarinyarnan alkairine, dan kuwa na lura duk halin uwarsu ta kwashe, kuzo ku haihu kanaji kana gani
anku su tashi ba tarbiyya, yanzu kuwa ALLAH yay maka sauyin alkairi, gidannan kaf babu mai cewa ga halin Umm-Rumana na banza, hakama uwarta, duk fitinar Gaje tayi ta barta, tunda ita dai ba tanka mata zataiba saboda ha
uri da kawaicin da ALLAH yay mata, dan haka ka kwantar da hankalinka akan yarinyarnan, insha ALLAHU wataran sai kace gwamma da akai hakan
Idon Ahmad a lumshe duk yana jiyo nasihar Ayyahn sa, wannan itace shawarar da kowa ke bashi, tare da fa
in gamma da akai, shidai jinsu kawai yakeyi, dan bazasu gane yanda Samina ta mallake dukkan zuciyarsa bane, yasan kozai shekara kwatanta musu irin mugun sonta da yayma zuciyarsa dabai bayi ba fahimta zasuyiba, gaskiya so bai masa adalciba, da yasan a haka wannan soyayyar tasu zata
are da ya ro
i ALLAH mutuwa kafin wannan lokacin, kawai dauriya ya keyi, dan mutane karsu kallesa mara zuciya ne kawai, amma ko yanzu Samina ta yarda zata zauna dashi zai saki Umm-Rumana ya sake auren Saminar.
Humm, tur
ashi Ahmad, lallai zuciya batai maka adalciba kam.
_________________________
Chapter 21 · 0% Book details