← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 99

Sashe 28

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya jikin?
Ya fa
a murya
asa-
asa.
Nace,
Alhmdllh, ya mutan gidan?
Shiru yay bai amsaba, harma na fidda rai dan na mi
e kawo masa ruwa sai na tsinkayo muryarsa yana fadin,
Lafiyarsu lau, suna gaisheki
Murmushi kawai nayi na
an rissina na bashi ruwan dana
ebo.
Amsa yay idonsa akan
afata da nake
ingisawa, sai da yasha ruwanne sannan yace,
Ki duba ledan nan akwai magani saiki sake sha, insha ALLAH zai saki gaba
Kaina na jinjina masa ina godiya, na tambayesa abinci yace ya
oshi, abincin da yaci
azun ya tsare masa ciki.
Shiru nai ban sake cewa komaiba, inason masa magana ko zaiyi wanka nima na gwada na
an gayu amma inajin tsoro, hakan yasa nai
an da bakina har muka kwanta.
_________________________
Haka rayuwar wannan gida ta cigaba da tafiya mana, inda nake ganin sabbin salon
abi'u daga matan gidan, dan a hankali dai maman Ama kejan kausar jikinta, kullum kuma babu fashi sai sunba junansu labarin maganin mata da sukai amfani dashi da dare, harma da gwargwadon aikin da yayi akan mazansu, gefe kuma maman Ama na zuge Kausar akan Uwargidanta, dan tanada kishiya a wani gidan da ban.
Lokaci
ani saiga amintaka mai
arfi ta
ulle a tsakaninsu, inda kuma idan
aya na
aki yazama ina tare da
aya a waje kaji yana sukar
an uwansa da gulma.
Kamar yanda Yah Ahmad ya
e ni babu ruwana to haka naja kaina, iyakata dakin gama nace ALLAH ya
yauta kawai nabar miki wajen, koma kina cikin fa
ar nasan dabarar da zanyi na bar wajen.
Basa iya ri
e sirrinsu, kowacce cikin zayyanema
ar uwarta halin da take ciki suke, hatta da abinda sukaci da dare idan miji ya
an sayo saisun bama juna labari, wani lokacinma na lura da biyu akeyi saboda ni, sai kuma lamari yaso juya akala kan maman Ama, dan kuwa dai Kausar tafi za
ewa akan sayayya irinta
walam da na
ulashe da mijinta ke mata, dan da safe har sauran naman kaza ko tsire ko balangu ake kasowa a filet ni da maman Ama duk dan mugani, tun ranar farko Yah Ahmad ya takan birki akan amsa, dan haka na bama Kausar amsa da ni bama nacin nama kwata-kwata, sai ta koma bama Maman Ama kawai, itako maman Ama zata amsa taci amma hakan na sakata ba
in ciki, dan zakiga tanata fushi da kawomin sukar Kausar wai tana badawane dan ace ta fimu jin da
i wajen miji, nidai bancewa komai.
A kwana biyunnan kuma sai naga itama maman Ama ta fara
abi'ar kaso abu ta bamu wai a zuwan tsarabar kasuwa baban Ahmad yazo dashi, itama dai bana amsa saboda gudun
acin ran Yah Ahmad.

iri da muzu sai gulmarsu ta koma kaina, yayinda a gefe kuma suke kishi da juna, ni lamarin nasuma dariya ya koma bani, duk da sun gimeni amma idonsu na kaina, ni kuma bawani abu gareni na nunawa a garesu ba, tunma danazo gidan inaga sau uku nasan naci nama, biyu nama
aya kifi, suma duk na abincine da ake saye bai kuma wuce na
ari biyu.
Zuwan da yaran gidanmu ke yawan yine yake
aukemin kewa, muyita hirarmu a
aki, sai kuma sukace na fara musu wani abu na saidawa kamar alawar madara ko aya ko iloka da makamantansu.
Banyi musuba nace su bari idan Yah Ahmad ya dawo zan sanar masa, idan ya amince to zan ringa yi musu.
Tun daga wannan ranar na fara sana'ar abubuwan yara, dan kuwa Yah Ahmad koda na gaya masa sai bai musaba, ya bani dubu
aya da
ari biyar yace nayi jari, godiya nai masa sosai.
Abun har yayta bama Ahmad mamaki, domin kuwa yakan tuna Samina da ku
i ka
an kansata tayi fushi, idan ta tambayesa 3k ya bata 2500 aka tai ha
uri bashi dasu, to ranar kam sai tayi fushi dashi akan 500 da babu koda zata amsa 2500
in kuwa, sai idan ya cika mata
ari biyar
inne zasu dawo dai-dai.
Amma yau gashi ya bama Umm-Ruman 1500 kawai matsayin jari tanata masa godiya kamar ya bata 100k.
Yaji da
in hakan sosai, musamman ma da yaga ta bada himma akan sana'ar, dan kuwa gida ta aika dasu Ammi ta sai Gya
a da aya aka soya aka
ullo daga can,
annenta suka
auki wata sauran aka aiko mata nan gidan saboda yara masu shigowa.
Akan wannan sana'a ba
aramin dariya Kausar da maman Ama sukayiba, acewar Kausar ita yanzu ai bata da time
in wata sana'a, yaushe ma ta gama morar amarcinta da har zata takura tunaninta wajen wasu
ulle-
ulle.
Maman Ama kuwa tace ai ita bama zata iya sana'ar naira biyar ba, domin sana'ar yarace.
Rumana dai batace komaiba, sai ma murmushi da tai musu kamar yanda ta saba.
Duk kuma wannan abun da suke Ahmad na
aki kwance yana jiyosu, su kuma basuyi tunanin yana nanba, dan da takalmansa ya shige ciki bayan ya dawo sallar juma'a, lokacin da ya shigo duk suna cikin
akunansu.
Koda Rumana ta shigo
akin baice mata komaiba game da maganar, dan shima takaicin abinda Samina ta masa yau ne a gidansu ya sakashi zuwa ya kwanta.

______________________________
Bayan sallar isha'i Ahmad ya fita zuwa gidansu, dan tun dawowar da yay bayan sallar juma'a bai sake fitaba sai da zaiyi sallar magriba, daga nanne kuma bai komaba har akai isha'i ya wuto nan.

annensa dake cin abinci a
ofar Ayyah duk suka gaishesa.
Amsa musu yayi cikin rashin sakewa, hakanne ya sakasu fahimtar yana cikin damuwar abinda ya faru
azun har yanzun kenan.
Daga can
arshen tabarmar da suke zaune ya zauna, a haka Ayyah ta fito daga lungun Baba ta sameshi..
Da damuwa sosai a fuskarta tace,
an albarka dama kana nan?
Kansa ya
ago yana kallonta, ya girgizashi ka
an yana fa
in,
A'a Ayyah, ai tun tafiyar da nai
azun ban dawo ba, yanzu ma nazo wajen baba ne

To lafiya dai ko?
Lafiya lau Ayyah, magana kawai nakeson muyi, amma inaso ma ace kema kina wajen

Shike nan tashi muje ai yana ciki
Tashi yay tsaye, Ayyah na gaba yana biye har lungun baba dake zaune a
ofar
aki saman tabarma, kwanika na gefensa da alama abinci ya gama ci, dan hannu ma yake wankewa lokacin da suka shigo.
Zama sukai suka jirashi ya
arasa, ya ajiye butar yana fesar da ruwan bakinsa da ya kurkure, sannan ya jawo da baya ya zauna sosai.
Gaishesa Ahmad yayi, ya amsa cike da kulawa yana tambayarsa Rumana.

Tana lafiya baba, tace ma a gaisheku

Muna amsawa, amma lafiya na ganka haka kamar mai fama da ciwo?
Kan Ahmad a
asa yay murmushi, murya a sanyaye yace,
Lafiyata lau Baba, kawai dai yanayin garinne

Amadu yanayin gari kokuwa abinda ka kasa yakicema ranka?, bara na fa
a maka gaskiya, inhar baka cire yarinyar nan da halayenta a ranka ba bafa zaka zauna lafiya cikin salama ba, ka cire duk wani abun da ya faru ko yake faruwa a gidannan ka fuskanci matar da ALLAH yay maka za
i madadin son zuciyarka, Ahmadu idanfa kai saken da yarinyar nan Rumana ta farajin ciwon wannan shirmen naka har taso guje maka wlhy zakayi *GUDU DA WAIWAYE....*, kasan kuwa da ga karshe iyakarka mugun zato, amma baka da karfin
aukar mataki, ina saka maka idone kawai dan naga iya gudun ruwanka, to na lura bamai sanin zuru bane kai, yanzu abinda akace yarinyar nan ta maka yau a gaban saurayi da mutanen anguwa idan kai da mai zuciyane bai cancanci ka
auke kanka daga gareta ba har abada?........

Ayi ha
uri dai malam, ai kowa yasan yanzu hankalinsa baya a kan Samina, sai dai mu tayasa da addu'a kuma, kasan dama irin wannan fitarsa a rai sai dai a hankali

Kayya Ru
ayya, ke dai bar lamarin shirmen wannan
an naki, inda har bai saka abun a ransaba ai da yabar damuwa da lamarinta, ya kuma tashi ya nema ma kansa mafita ko
Ahmad da kansa ke a
asa yace,
Baba kuyi ha
uri ku gafarceni, yanzu ma haka nazone da wata mafitar, fatana dai ta zama mai amsuwa a gareku
Baba yace,
To babu laifi, muna saurarenka
Sai da Ahmad ya kuma luliya maganar a zuciya kafin yace,
Baba dan ALLAH inason a bani izini na bar garinnan

Kabar gari kuma? To zuwa ina kenan?

Duk inda ALLAH ya rubuto mani, inason fita nema ne kawai, bawai dan anmin gorin rashin arzi
iba, ba kuma dan ban godema ALLAH da sana'ar da ya baniba, hakan zaisa zuciyata mance komai dai insha ALLAHU
Baba dake jinjina ka sa yace,
i ta taka ba, amma dai abin dubi anan ita matar taka fa? Duk auren naku kwanansa nawa? da za'ace ka tafi wani waje ka barta, sai naga kamar akwai wauta
Shiru Ahmad yay, dan haka baba yace,
Jeka tsakar gida ka jiramu, amma ka turo mani Suwaiba
Ahmad ya amsa da to yana mi
ewa ya fita, da kansa ya le
akin gwaggo ya sanar mata kiran baba.
Batace dashi komaiba ta kashe redion da takeji ta tashi ta fito amsa kiran.
Koda tazo ta zauna Baba yay mata bayanin komai da Ahmad yazo dashi, bata ce komai ba a kai, dama sunsan bazata ce
inba, sai Ayyah ce ta bama baba amsa da
Niko malam sai naga kamar babu komai insha ALLAHU, musamman dai da itama Rumana tamuce, kuma itama barinsa garin zai kawo mata salama harya fuskanceta, sannan kuma bamusan alkairi. da ke cikin wannan tafiyaba da yaketa ambato, amma duk hukuncin da ka yanke akan hakan mu masu biyayyane akansa, dan abinda ka hango mu bazamu hangosa ba sam
Baba dake sauraren Ayyan ya sauke nannauyan numfashi, kafin yace,
Tunda har kun aminta da hakan kuma ai Alhmdllh, ni dai dama ba matsala bane, tun kuma maganar farko da kikaimin na sanar da su Iya, suma basuyi jayayyaba, sun dai ce na dakata har sai ya sake kawo maganar da kansa, to tunda yanzu ya sake maganar ai ina ganin sai kawai mu bisa da fatan alkairi ko?
Cikin fa
a murmushi Ayyah tace,
Hakane malam, mun kuma gode da wannan amincewa, sai aita tayamu da addu'a kuma
Chapter 28 · 0% Book details