Sashe 99
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wasa Oum tayi nesa da shi. Wani lokacin ko toilet ta shiga yana ofar bayi yana jiranta har saita kammala abinda take ta fito. Idan zataje wajen Abah kuwa a ranar girkinta sai fa da wayo da dabara idan ta tabbatar barcinsa yayi zurfi can cikin dare. Wani lokacin kuma dashi dole take tafiya ta kwantar da shi a falo ko in barcin nasa yay nisa ta maidosa cikin an uwansa. Akowane motsinsa shi dai Oum ce. Gashi da shegen iwa tun yana watanni biyar zuwa shida baya yarda da kowa sai Oum sai Fadeel idan yaso. Amma ko Abah da Mamy basu isa ta ashi ba ya hau ihu yana bin Oum da kallo yana kuka. Sanda ya cika shakara aya da wasu watanni kuwa idan ka takura sai ka aukesa cizo zakasha ta yanda dole ka saukesa ya koma wajen uwarsa. In ma anguwa suka fita bai yarda wani yako ta asa daga jikin Oum. Baba Sardauna ne ma ke an samun wannan alfarmar shima ana an yarda da shi saboda yana bashi irin chocolates in da yake so. A haka ya cika shekara hu u aka saka shi a makaranta kamar sauran an uwansa. Duk da su an sakasu tun suna da shekara uku-uku, shiko ulafucin uwa ya hanashi. A yanzun ma dai bada ala ake sha dan baya aunar zaman makarantar, yata kuka kenan da kiran Oum! Oum! Shi akaisa wajen Oum in sa. Shi gida zaije wajen Oumyn sa. Karatu ya iyi ya hana sauran yara yi. Duk wanda ya nuna kulawarsa da son rarrashinsa ya dan arama yaro cizo sai an rabasu da yar. Ganin haka yasa makarantar suka bada shawarar a ara masa lokaci ya ara wayo, dan inma ba hakaba bafa karatun zai yi ba. Dole su Oum suka yarda da hakan, amma tana arin masa a gida ita da Fadeel musamman na angaren addini. Gashi kuma da walwa Masha ALLAH. Sai da Ajwaad ya cika shekara bakwai a duniya sannan Mamy ta sake samun ciki, a lokacin yana zaman makaranta da yar dan yana a nursery 2 ma. A islamiyya kuwa Alhamdullah ya tashi da wazon karatu kamar sauran an uwansa biyu. A wannan karon abinda ya fara tadama Mamy hankali kamar Abah bai damu da cikinta ba kamar ukun can na farko, sai Oum ce ma ke dama-dama da ita da bata kulawa. Idan tai magana yace to mikuma ya rage shida keda uku rigis, ai sai fatan alkairi da addu'ar ALLAH ya sauketa lafiya. Wannan furuci nashi na cimata zuciya, amma haka take dannewa ta maida abin wasa. A haka ta shiga watan haihuwa, a kuma lokacin Abah ya fara musu gini dan yace wannan gidan ya musu ka an ga zuri'a suna tarawa. A wata juma'a Mamy ta sauka lafiya an biyu duk maza. Musalta muku irin farin cikin da wannan ahali suka shiga a wannan karon ma ata lokaci ne. Anyi shagalin suna kamar yanda akai na baya, duk da Mamy taso ace na wannan karon yafi na bayan armashi kodan biyu data santalo. Haka dai suna ya tashi lafiya yara sukaci sunan Hassan da Hussain. Dan tace bata son a canja mata suna a barsu da nasu. Duk da a wannan karon Mamy batace ta mallakama Oum su an biyu ba bata fasa yin hidima a gareta da jinjirayen ba kamar yanda ta saba. Dan har takai Ajwaad na nuna kishinsa a fili, sai dai suyita masa dariya kawai. Bayan yaye su an biyu da wata uku Hussain ya fara laulayin ha ora, ya dinga gudawa irin na ha ora mai wahalarwa. Abin ALLAH kwana biyu kacal a wannan halin UBANGIJI ya auke abinsa. Duk da rasuwar yaro ce ta girgiza wannan ahali, dan daga Oum har Mamy kuka rurus sai Abah ne ke lallashinsu, da yar suka ha ura suka sabarma kansu da rashinsa. Sai kuma tunda Hussain ya rasu shima Hassan lafiya ta masa aranci. UBANGIJI mai rahama da jin ai shima bai cika kwana arba'in ba yabi an uwansa. Ai neman zautuwa Mamy tayi, da yar ake tausarta. Sai dai kuma babu yanda ta iya da hukuncin ALLAH. Tun bayan rasa an biyu ko atan wata Mamy bata sake yi ba. Har suka tare asabon gidansu da a yanzu suke ciki wanda ke ma waftaka da nasu Maanal. Zuwa yanzu tsanar Oum Mamy keji mai zafi a ranta, amma a zahiri bazaka ta a fahimtar hakan ba, gefe ga uwarta da an uwanta dake zugata. Ba Oum kawai ba, hatta duk wanda Oum ke hu a da shi Mamy ta tsanesa. Dan haka bata ta a son Ammie da su Maanal ba. Amma koda wasan wasa bata ta a nunawa a koda fuskarta ba. Sai ma nunawa take kamar tanama Oum kawaici musamman akan tarayyar Maanal da Ajwaad dake a bayyane ga kowa. Ita ko Oum soyayya takema Mamy ta gaskiya da kuma zuciya aya, jin girmanta take da kimarta ta yanda zuciyarta koda hasashe bata ta a kallon munininta ba. Kai a yanzu koda Abah yazo yace da Oum ga munin Mamy to tabbas bazata amince ba. Ta bata matu ar yarda da gaskiya ta yanda bata ko jin wani ushin kishita a ranta. Kai sam bama ta mata kallon kishiya sai ar uwa. Hatta da sirrinta bata ta a canjawa daga yanda take sanar mata ba a sanda suna amintaka da awance. Komai bu ema Mamy take da zuciya aya ta nema shawara. Kuma a cikin an uwanta kaf babu wanda ya ta a kallon illar hakan dan suma yarda aya suka bama Mamy saboda unbin hallaci da yakana da dattakon data nuna ga Oum in. Lallai Mamy ta samu fada da soyayya tako ina daga zuri'ar Baffa Ishaq Darma. Yarda suke mata ta gaskiya, basa ta a banbantata a matsayin bare a cikinsu, basa ta a banbantata tsakaninta da Oum dake matsayin tasu. Kai sai suyi mata abu basu yima Oum ba musamman ma mahaifinta Dr Kasheem Kura. Dan shi yakance Mamy itace arsa. Oum kuwa ta Baba Sardauna ce. Itama a zahiri ta ri e dukkanin abinda zasu kalleta da wannan mutuncin, duk da zuciyarta cike take da shirin maido da anta gareta komai tsahon lokaci da rayuwa zata bata. Hakama duk damar data samu daga Abah da yarda bata gamsar da ita ba, kullum cikin sake harin ninkin baninkin inta take yi. Duk da kuwa ta wawashi kaso mafi girma daga soyayyar tasa. Dan tun fara girman su Fadeel Oum ta sake sallama mata Abah in kaso saba'in cikin ari, ita kuma yake ri e da talatin cike da kawaici da dattakonta. A yanzu ko tafiya Abah zai yi da ita ne. Idan wani abu ya taso kai tsaye Oum zatace yaje suyi da Mamy ita bazata iya yin nesa da yaranta ba. Tun abin na bama Abah haushi har ya ha ura ya sallama dan ya fahimci mai raba Fateema da an nan nata sai dai ALLAH. Musamman Autan ta uban alata da ulafucin uwa. Duk da Oum bata ta a fitowa ta sanar ma yaran ainahin mahaifiyarsu ba tana nuna musu girma da darajan Mamy a garesu. Kullum cikin cusa masu soyayyarta take a zukatan yaran cike da hikima. Tana awata musu girma da kimar Mamy a zukatansu. Tun abin baya tasiri a ransu harya fara. A hankali Fadeel da Fawzan suka an fahimci wani abu ka an bamai yawa ba. Sai dai hakan bai ta a canja musu Oum insu a matsayin da suke kallonta ba. Ita dai suka sani, ita kuma suke kallo da matsayi irin na uwa da mahaifiya. Amma suna girmama Mamy da bata hakkinta da mata soyayya kamar yanda Oum ta koyar da su take ma kan koyar da su in. Shi dai oga Ajwaad Auta Oum insa kawai ya sani. Shi uban kowama ya mutu har liman in dai za'a bar masa Oum insa. Farin cikinsa ce ita, sannan duniyarsace. Bai ha a soyayyarta data kowa ba a duniya... Wannan halin na Ajwaad na cima Mamy rai matu a, dan ALLAH ya jarabceta da soyayyar Ajwaad fiye da duk sauran yaranta. aunar yaron take har ashin zuciyarta. Ga shi kuma hankalinsa san baya a kanta yana akan ma iyarta ne. Shiyyasa take sake jin ninkuwar zafin Oum in matu a. Gashi ta fahimci itama Oum in tanama Ajwaad wata irin soyayya mai girman gaske. Hakan na nufin bayan Aliyu sun sake yin tarayya akan abu guda kenan. Wato soyayyar AJWAAD ALIYU ABUBAKAR DARMA... _MUN SAKE DAWOWA DAI CIKIN LABARIN RAYUWAR AJWAAD DA MAANAL DATA GABATA *GIRO:-* A Giro dai an aura auren Babu da amaryarsa Safarah. Safarah yarinya yawa mai busashen ido. Dan cikakkiyar ar tallace a tashoshin motoci na yankin auyen Giro da cikin Suru. Musamman a ranakun kasuwanni. Kai har cikin Kebbi idan ta kama suna zuwa kawo kayan sayarwa ita da awayenta. Gwaggo ta za ama Babu ita ne dan a cewarta itace dai-dai da Asiya. Anko sha biki, dan su Ammie sun sha kallo. Bajinta sosai Gwaggo tayi a bikin dan dabbobinta har goma ta saka a kasuwa. Bayan tarewar amarya a nan dai gidan akin dake a tsakanin Gwaggo da Ammie ango yasha bidiri. Dan Babu dai kura ne ba'a bashi ajiyar nama. Duk da ma dai abin bai masa armashi ba saboda samun Safarah ba'a cikakkiyar budurwa ba ita dai. Amma tsabar iya bariki na yarinyar nan da dudu shekarunta goma sha tara ne a duniya sai ta dinga zumbu a masa ihu da kururuwa ita a dole tana shan wahala. Wannan ihu ya tadama Ammie hankali, bawai akan kishi ba, duk da bazatace bata kishin mijin nata ba. A'a saboda su Shahidah ne. Dan takai yaran nan sai da suka farka a barci suma. Yayinda itama kanta Gwaggo data fito tsakar gida a wannan tsohon dare take faman kiran sunan Babu da garga insa akan wai yabi Safarah a hankali, ya dai san yarinyar arama ga mutuncinta ta kawo. Wannan abu shine ya taru ya saka Ammie kuka dan su Amaal nata jera mata tambaya akan ko mi ya samu amaryar haka. Sai dai bata kula yaran ba, daga arshe ma ta musu tsawa suka kwanta. A ranta dai tana sake godema ALLAH da su Abah suka wuce da Maanal. Dan tabbas ka