Sashe 30
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
amazing young lady . Sai kuma ya shiga tafa mata. Suma sauran tafa matan suka farayi suna mai kallon boss in nasu da har yanzu bai tanka ba baima maida hankalinsa a kansu ba yanata duba magazine insa hankali kwance. Ganin dai bashi da niyyar kulasu suka ha ura suka daina. Sun bata takarda da kayan aiki tai zanen agogo a take anan, zanen da yay mugun basu mamaki da aryatar dasu. Daga haka File suka tura mata da mata bayanin zata cike tai singing a take anan. Bata musa ba taja file in gabanta. Ta an dudduba abinda ke cikinsa kafin ta shiga gudanar da dukkan abinda suka bu ata zuciyarta na mata wani irin sanyi alau dan kuwa dai sun tabbatar mata da aukarta aiki ne. Acan asan ranta kuwa tana mamakin nasu tsarin. Daga interview a take a wajen kuma babu batun kaje ka jira sai a tabbatar maka da an aukeka aiki. Haka dai ta gama cike komai tana zancen zucinta ta basu. Bayan sun dudduba suka mi ama ogan nasu da sai a yanzu ya ajiye magazine in ya fara duba file A karo na farko oga kwata-kwata da yay kamar bashi nan a wajen ya ago kansa bayan kammala duba komai na file in, cikin wani irin dakewar murya ya jeho mata tasa tambayar data tilastata kallonsa. A yanzu ba bugun zuciya kawai taji ba, zuciyar tatace gaba aya zata iya cewa ta tarwatse a dalilin kallon ido cikin ido da sukaima juna. Suma, aukewar numfashi, ko gushewar hankali ko tsatstsagewar zuciya batasan yanda zata kira yanayin data tsinta kanta a wannan lokacin ba ma......... _Tofa jama'a mi kuma ke shirin faruwa anan?. CEO na Mawaad Company da Maanal? Kumuje zuwa wasan na ainahi ma yanzun ne zai fara a duka angarorin in sha ALLAHU ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ........Fin mintuna biyu sunama juna kallon tsakkiyar idanu babu ko yaftawa, yayinda sauran sukai kasare suma suna kallonsu da mamaki. Da wani irin shegen salo CEO in nasu ya juya mayan oily ayes insa masu matu ar haske kamar madara dake cikin ha en siririn farin gilashi tas tare da kauda fuskarsa gefe yana mai furzar da wani irin huci. Sai kuma ya sake dawo da idanun nasa a kanta cike da barazana da isa da basarwa ya furta, Miss Maanal! Answer my question Duk da cikin nutsuwa da sassanyar murya yay furucin, sai Maanal ta dinga jin kalaman aya bayan aya suna mata wani irin amsa kuwwa da tartsatsi a cikin kunne, acan kuma sama ololuwa. Ga wani irin sanyi yana saukar mata a ga an jiki da asusuwanta tamkar yanayin yammaci ko safiya a lokacin tsananin hunturu irin na arshem Janairu in nan. You are not serious Miss Maanal . Ya fa a cikin gizago da nutsatstsen sauti mai cike da aji yana mai an buga desk in da yatsunsa biyu. Firgigit Maanal ta dawo a hayyacinta tamkar wadda aka farkar da ga barci. Sai dai har yanzu sanyin nan na cigaba da ratsata tun daga saman kai har yatsun afafu. Sam bata san ta yanda akai ta bu e lips inta cikin dakiya da tarin nutsuwa ta bashi amsar tambayar tasa ba. Har lokacin kuma idanunsu na a cikin na juna. A karo na biyu shine ya sake kauda kansa. Sai kuma ya an yamutse fuska da aureta yana maida hankalinsa a kan sauran da sukai jugum-jugum suna kallon ikon ALLAH. Duk da kuwa wannan ba sabon abu bane a wajensu. ammata da yawa a cikin Companyn nan sun jima da mutuwa akan boss in nasu. Hakama masu shigowa domin bussines suka shiga fiye da irin yanayin da Maanal ta tsinta kanta a yanzu. Bakuma wai dan ogan nasu yafi sauran maza bane, badan yafi kowa yau da iya ado bane, badan yafi kowa dukiya da cikar kamala bane. Kawai dai ALLAH ya bashi farin jini da wani irin kwarjini da ko su kansu mazan yana cika musu waje duk da kasancewarsa yaro matashi da bai wuce 30+ ba a duniya. Boss insu nada wasu qualities da mata da yawa ke bu ata a tattare da mazan zamani na wannan arni. Duk da dakewarsa da kamewa da asaita hakan bai hana ammata kawo masa hari ta kowacce kusurwa ba. Koda yake ku i fa babu abinda basa saka matan wannan zamanin, kai Bama mata ba kowafa a wannan arnin ya koma girmama matsayin bawa da abinda ke a hannunsa ne kawai. Sai kana motsi akeyi da kai, sai ka zama wani ake girmamaka da son ra arka. Da zarar baka dasu ko sun bar hannunka sai kaga kowa ma ya janye jikinsa an zubar da kai a kwandon shara saboda dama can ana maka soyayya da girmamawar ne saboda kana amsa sunan wane.... ewarsa ta saka tunaninsu katsewa. Document in ya tura gabansu tare da mi ewa da yau yana ha e rigar suit insa ya saka botirin dake jikinta waya aya tak. Batare da ya sake kallon inda Maanal take ba ya nufi hanyar fita yana fa in, Zata fara aiki damu gobe in sha ALLAH Daga haka ya fice abinsa cike da takun mazantaka da asaita har ma da gayu na matasan samarin wannan zamanin musamman irinsa da ke ji da kansu da MANDA A GIDAN SANYI .... ___________ A lokacin da anan Maanal ke Maawad company domin yin interview acan Kaduna su Daddy ne ke shirin mi a ku in auren Yazeed ga mahaifin Nazeefa iyar Aunty Sabuwa saboda matsawar Hajiya Yaya akan al'amarin. Ganin abin na neman zama wata fitinar kuma a tsakaninsu Ammie ta saka baki tanata ro on Daddy dan yace shifa sai arshen shekara. Da yar dai ya amince za'a kai in bayan ita kanta Ammien ya gaya mata ba ar magana. Duk da abin yay mata zafi sai tai murmushi kawai ta yalesa. An kai ku i inda suka samu tarba ta musamman kamar wasu bare. Dan abin har mamaki ya bama Daddy in. Amma dai sai ya danne kawai akai gaisuwar mutunci. Dana shi ne da amininsa Alhaji Sunusi na Zaria. Sai ma wafcinsa Alhaji Isa da wani abokinsa Alhaji Sulaiman. Abinda ya sake aure musu kai ana maganar tsaida date caraf mahaifin Nazeefa yace ai wata aya ma ya isa. Dan shi a shirye yake dama. Kallon kallo aka koma yi a tsakanin su Daddy, sai dai babu wanda yace komai sai Alhaji Isa ne ya ce, Amma Alhaji kodai a ara, ko kuma shi Alhaji Usman in aji ta nashi angaren Caraf yace, Alhaji bazaka gane ba, yanzu idan arka ta samu miji ba'a sanya wlhy, mu da Alhaji Usman ai duk aya ne. Kawai a taimakeni ayi a hakan, kai ko auren ne a aura to daga baya sai ayi bikin Rasama abin cewa sukai su duka. Sai Daddy ne ya an girgiza kansa kawai. Sai kuma ya gyara zamansa tare da fa in, Shike nan ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Amma bayan wannan in shi yaron akwai wata kuma, itama idan anyi an gama kamar nan da watanni biyar haka sai ayi nata. Naso ma ayi gaba aya ne a huta sai kuma larura ta gitta, to shi ciwo ya wuce komai a rayuwa shiyyasa aka aga natan za'a fara shi wannan an jimm Baban Nazeefar yayi, sai kuma zuwa can ya saki guntun murmushi da fa in, Babu damuwa Alhaji Usman, ai duka gidane tunda itama in dai ta gida ce. ALLAH ya kaimu lokacin Da amin duk suka amsa baki aya. Daga haka suka arasa abinda ya rage aka bar saka rana a matsayin wata biyu in. Suna fita a gidan Aunty Sabuwa dake la e ta afko falon, rungume mijin nata tayi cike da farin ciki, shima sai yay murmushi a ransa yana fa in (wannan farin cikin nawane ba naki ba Sabuwa, dan lokaci yayi da zan maidama Alhaji Usman martani, lokaci yayi da zan waci abinda ya hanani a baya da arfin tuwo. Lokaci yayi da wasan na gaskiya zai fara tsakanina da shi....) _Tofa masu karatu, shin mike a tsakanin Alhaji Badaru mahaifin Nazeefa da Daddy kuma?. Ku dai kumuje zuwa mutanena ___________ Wai hawayen nan basu isa haka ba ne Maanal? Tunda muka taho kike sharar hawaye inata magana kin i cewa komai. Kin san kuwa yanda zuciyata ke agawa da wannan yanayin naki. Please! Tell me! Is something bothering you? Wani abu suka fa a miki mara da i ne? Ko basu aukeki aikin bane sukace? Yanzun ma komai in cewa da shi tayi, sai hankalinsa ya ara tashi matu a. A haka suka iso gidan Shahidah. Ko parking kuma bai gama yi ba ta bu e motar ta fita, shima saurin fitowar yayi sai dai harta shige abinta cikin sassarfa da an gudu-gudu. Hankalinsa ne ya sake tashi, sai kuma ya rasa inama ya kamata ya kama. Kamar zai bita sai kuma ya dakata. Yayi hakan yafi sau uku sai kuma ya koma cikin motar da sauri ya mata key ya bar gidan. Wani irin gudu ya dinga shararawa daya kawosa Mawaad Company cikin anin lokaci. Yana shiga kai tsaye office in Boss in ya nufa. Ko jiran Assistant insa ya masa iso baima yi ba yanzu. AS in ne ya biyosa yana arin tsaida shi da sanar masa Boss yace kada abar kowa ya sake shigo masa sai in har shine ya bu ata amma sam RK bai sauraresa in ba ya afka Office in kansa tsaye cike da fushi kuma. Shi dai shi kuma arin sake sanarma RK yake yi cikin damuwa da tashin hankali, dan tunda yake aiki a ashin ogansa bai ta