Sashe 41
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta juyo tana masa wani kallon. Ganin yanda ta zuba masa manyan idanun nata masu rikitashi ya wani langa e kansa da marairaice fuska yana an du owa gab da ita ta yanda ita ka aice zata iya jinsa a maganar da zaiyi. Please ki daina min irin kallon nan kina rikita min lissafi na ne Harara ta an sakar masa tare da janye idanun gaba aya. Babu yanda ta iya da fitinar RK dole ta hure kamar yanda yake bu ata, dan ya tabbatar mata idan batayi hakan ba babu inda zaije yau. Ganin yaja kujera ya zauna ga mutane ya cika musu office da su ya sata hurewar kawai dan ka an kenan daga aikinsa ya zauna in. Cake ne dai duk yanda yayi taci ta gutsira ta bashi a baki i tayi, sai ma tai kicin-kicin da fuska ta yanda dole ya ha ura dan baya son yaga ta ha e masa yawar fuskar nan tata damuwa yake shiga. Haka dole da kansa ya gutsira yaci ya mi ama wanda ya gayyato da su Yaqub dake a office in kowa ya yanka yasa a baki. Daga hakan nutsuwa yay sosai yay mata addu'oin fatan alkairi da nasara a wannan aikin, ita harma hakan yaso bata mamaki, yayinda sauran ke amsawa da amin. Bayan ficewar kowa ya wani zabga tagumi yana kallonta. Itako ta sake maida hankalinta ne a aikinta. Sai da taji kallon nasa na neman cutar da ita ta ago ta kallesa tare da sakar masa ar harara, sai kuma tai masa nuni da su Yaqub da ido. Murmushi ya saki mai ayatarwa da gyara zamansa. Ita kuma ta maida kanta yay arin dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta. Maanal Har tsakkiyar kanta taji yanda ya ambaci sunan nata. Kodan ba cika kiranta da sunan yay ba akoda yaushe oho. Sake agowar tayi ta dubesa batare data amsa ba. Bai damuba ya cigaba da fa in, Maanal dan ALLAH ki iyakance min wahalar nan mana, na isa aure fa, ga kuma mata a kusa dani miya rage kuma dan ALLAH? . A hankali yake maganar yanda ita ka ai ke jinsa, duk da kuwa su Zaharadeen sarakan gulma sun baza kunne amma basa jiyo komai. Lips inta ta an cije zuciyarta na mata nauyi, (miyyasa su basa fahimta ne, miyyasa bazasu gane ba. Ita fa Maanal, wannan Maanal in da suke gani gaba aya a yanzu babu zuciya a irjinta, in dai zuciyace ta soyayya ta ta jima da mutuwa......) Maanal!! Ya sake katse mata tunani, yanzu ma bata amsa ba sai dai ta janye idanunta da suka cika da walla daga kansa. Aikinta ta cigaba da yi tana arin ha iye hawayen. Shima sai yay murmushi kawai tare da mi ewa gaba ayansa. arfe nawa zaki tashi? Batare data ago ba dan bata son yaga yanayinta ta ce, Bazan iya cewa ba, saboda ina son kammala aikin nan duka a yau an jimm yay sai kuma ya jinjina kai da fa in, Okay bari na kiraki kawai, ko kuma zuwa six, I will come back kawai Okay thanks Ta fa a a ta aice. Shima sai ya an murmusa kawai ya juya ya fita abinsa yana ma su Zaharadeen dallama. Fitarsa bai fi da mintuna biyar ba kira ya shigo a wayar gabanta. Koda ta aga sai ta samu AS in Boss ne, wai boss in na son ganinta a office insa. Idan tace ka an ya rage zuciyarta ta wantsalo ta baki kar kuyi mamaki, ta jima shiru da kan wayar a kunnenta bata iya ta ajiye ba. Sai zuwa can ta kife ta da yar ta mi e cikin arfafa kanta. A dakenta ta isa office in, bayan sun gaisa da AS ya mi e yana fa in, Bismillah . Komai batace masa ba, yana gaba tana biye da shi har cikin office in. Karo na farko kenan data shigo office in. aton gaske ne, ya kuma ayatu da abubuwan more rayuwa matu a gaya. Tamkar ba office ba komai dake a cikinsa fari ne al, hatta da kujerar zamansa da desk kai komai da komai. Sai kuma Mable's in da aka shimfi a a asan ya kasance ba i wulik tamkar wata ajiyayyar kwalba. amshi kam ba'a magana, ga ac kamar an uresa da gayya. A cikin sakanni da basu wuce biyar ba taima office in wannan kallon. Yana zaune a mazauninsa hankalinsa gaba aya nakan computer in gabansa, yayinda hannunsa ke danna keyboard dinta, na haggu kuma ri e da document. Yanzu kam ya cire rigar saman suit in nasa sai ta cikin kawai. Duk da shigowar tasu bai ago ba balle ya nuna yasan da su. Cike da girmamawa AS da ya an matsa kusan gaban desk in sosai ya an rissina tare da fa in, Sir gata tazo Sai da ya an ja sakan kusan biyu kafin ya ago mayan fararen idanunsa da ke nuna matu ar gajiya da aiki ya sauke akan AS in nasa. Sai kuma yay luu da idanun ya aukesu daga kansa ya maida ga computer in tare da an kai hannu ya gyara gilashinsa. A can asan ma oshi ya furta, Zaka iya tafiya Sake rissinawar girmamawa AS yay ya juya ya nufi ofa. Sai da yazo saitin da Maanal ke tsaye tayi kicin-kicin da fuska matu a a hankali ya furta, Sister Maanal bismillah ki arasa . Daga haka ya fice. Yitai kamar bazata arasa in ba, dan ta ata fin minti aya kafin ta aga afarta da yar. Koda tazo inda yake maimakon ta zauna sai tai tsaye abinta. Shima yi yay tamkar ya manta da ita sai aikinsa yake kawai hankali kwance. Sunja fin mintuna uku a haka kafin ya ago kansa a hankali ya wani zuba mata idanu, sai kuma ya sake aure fuska fiye da yanda ta shigo ta samesa. Cikin ausasa harshensa, da tsaurara kalamansa ya furta, Ba'a baki tsare-tsare da dokin wannan companyn bane? A yanda yay maganar yasa ta ago nata idanun ta kallesa. Kallon ido cikin ido suka zubama juna, fin miti aya kafin ta janye nata, sai kuma ta canja yanayinta, cikin yanayin girmamawa irin na oga dana asa ta furta, Am sorry Sir, an bani tun ranar farko da nazo Kamar wanda yaji haushin yanda tayi in sai ya wani cije lips tare da auke kansa a lokaci guda. Bu e-bu en document in gabansa ya fara yi, sai da ya sake jan minti aya a hakan, sannan ya cigaba da magana batare da ya kalleta ba. Wannan Companyn ba lambu soyayya bane ko club. Idan bu atar ganinki yake ko zuwa gareki ai yasan inda kike. Karya sake zuwa min nan da shirme in ba haka ba zan auki mataki a kanku ku duka zaki tafiya Tafasa zuciyar Maanal take, tafasa irin mai yun urowar nan daga irji zuwa ma oshi har ka dinga jin turirin a cikin bakinka. Karo na biyu ta ago ta dubesa kamar zatayi magana sai kuma ta ha iye, shiru ta sake yi tana daidaita kanta. Zuwa wasu sakanni kanta a du e da girmamawa ta ce, Kayi ha uri sir, in sha ALLAH zamu kiyaye. Na barka lafiya . Daga haka ta juya ta fita abinta. Wani irin wurgi yay da file in hannunsa tare da dukan desk da arfin masifa, sannan yay baya ya kwantar da jikinsa gaba aya a kujerar yana furzar da huci masu masifar zafi... Tofa, wai yaya take ne nifa na kasa ganewa Amin arin bayani mana mutanena ____________ Abuja? Daddy ya fa a da wani irin mamaki arara a fuskarsa yana arema Huznah kallo daga sama har asa. Cikin dake yanayin tsoronta dake neman bayyana ta jinjina masa kai. Eh Daddy, dan ALLAH ka barni naje sati aya kawai zanyi. Kaga tunda muka duba Maanal sau aya babu wanda ya sake komawa a cikinmu. Shiyyasa nake son naje na sake dubata na kuma sada zumunci kodan su Shahidah su cirema kansu tunanin dan bakai ka haifesu ba shiyya bama son zumunci da su Rasama abinda zaice mata Daddyn yayi, sai kawai ya zuba mata idanu sosai fiye da farko. Shi ba mazaunin gida bane kam koda yaushe, amma yana hankalce da abubuwa da yawa da suka shafi gidan nasa da iyalansa baki aya, zai iya cewa ko lokacin auren su Shahidah a kaf ansa idan ka cire Yazeed babu wanda yay ma su Shahidah rakkiya gidan miji, a lokacin ma su duka anan Kaduna aka ajiyesu, dan daga bayane ita Shahidah suka koma Abujan sakamakon arin girma da mijinta ya samu..... Uhm Daddynsu dan ALLAH kada ka kawo komai a ranka.. Hajiya Basariyya ta fa a cikin son kauda ma Daddy hankali, dan duk tattaunawar tasa da Huznah itama tana a falon kasancewar girkinta ne, juyowa yay yana kallonta dan haka ta sake marairaice fuska ta cigaba da fa in, Nasan zakai tunanin abubuwa da yawa a ranka game da hakan, sai dai ka tuna al'amarin UBANGIJI yafi na kowa, shi kuma mai canja kowa ne a lokacin da yaso, eh tabbas da anyi kuskure, sai dai abinda ya faru a an tsakanin nan yasa na koyi darasi da yawa, sannan ina da burin naga na gyara kuskurena ni da yarana duka. Dan ALLAH ka barta taje, na baka tabbacin in sha ALLAHU ba zaka ji komai mara yau ba sai dadda Shi Daddy ma rasa abinda zaice yayi, ga uwar da ar sun wani tsatstsaresa da idanu. Yafi mintuna uku a haka kafin yaja numfashi ya fesar, cikin an jinjina kai yace, Kije zanyi tunani Jiki a sanyaye Huznah ta mi e tana masa godiya. Koda ta fita sai Hajiya Basariyya ta sake fuskantarsa, cikin kwantar da murya da da in baki taita tsara masa magana, tun bai maida hankali gareta ba har ya nutsu yana saurarenta. Sai dai amsar da taso ji bai bata in ba a wannan daren. Da safe kamar yanda ta saba bayan ya baro massaci sallar asuba, kasancewa baya shigowa da wuri sai gari yay shaa ya wuce sashen Hajiya Yaya, haka yake yi a kowacce safiya in dai yana gida zai shiga ya duba kowacce a sashenta, hatta mai girgi yana shiga dan ganin lafiyar yaransa. Bayan ya koma nasa sashe kuma