Sashe 42
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
duk su bishi su gaishesa. Daga sashen Hajiya Yaya na Hajiya Basariyya ya shiga, duk kuwa da ita tana nashi sashe, bai wani ja lokaci ba ya wuce na Ammie. Kamar yanda ya sani ya sameta zaune tana azkar itama. Dan sam bata barcin safe. Zama yay daga bakin gadonta daya sha gyara, dan tana tashi sallar asuba take gyara kayanta kafin ma ta shiga toilet. Cikin nutsuwarta da dukkanin anta suka gada ta ajiye littafin hannunta ta juyo tana gaishesa. Da kulawa ya amsa mata fuskarsa da an murmushi, itama murmushin ta sakar masa kafin ta mi e, fita tayi, babu jimawa ta dawo auke da aramin tray da kofi a samansa daketa tururi. Rissinawa tai ta mi a masa, ya auka yana murmushi da fa in, ALLAH yay miki albarka ke da zuri'arki baki Amin ya rabbi tare da kai da zuri'arka kaima . Ta amsa masa da girmamawa. Ba wani abu bane shayi ne mai an karan da i na wasu itatuwa masu muhimmanci da take dafa masa safe da yamma. Idan ranar girkinta ne takan basa, idan ranar da ba girkinta ba ne kuma idan ya shigo da safe yakan sha anan, da yamma kuma taba yara su kai masa ko idan ya shigo yimusu sai da safe. Da farko an auki rikici akan wannan bada shayi tsakaninsa da sauran matansa, dan sai da suka bi kwaf-kwaf suka gane abinda ke sakashi jimawa a sashen Ammie in a duk sanda zai shiga da nufin gaisuwa. Rikici yay rikici Ammie tace ya raba musu kayan shayin kowa ya dinga dafo masa a ranar girkinsa. Badan yaso ba yayi hakan, sai dai baya jin kaf in su sunyi masa sau bibbiyu suka arar wai su gaskiya bazasu iya wannan wahala ba, ace daka yi sallar asuba sanda zaka koma ka huta ka wani tafi dahuwar shayi kitchen, daga nan aka samu maslaha Ammie jurau in ta cigaba da dafa masa. Sai da ya kammala shan shayinsa tsaf kafin ya fuskanceta. Cikin taus asawa da kulawa ya dubeta tare da kiran sunanta. Amsa masa tayi itama da girmamawa. Ya ce, Jiya Huznah da uwarta sun sameni wai tana son zuwa wajen ar uwarta Shahidah tai sati Wani irin bugawa da arfi irjin Ammie yayi, babu shiri ta ago da sauri ta zubama Daddy idanu......... ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ........Shima kallonta yake tashi zuciyar na rawa. Amma a mamakinsa sai ya ga ta saki murmushi kamar yanda ta saba. Cike da jarumtar danne dukkan abinda zuciyarta ke kissima mata ta ce, ALLAH na gode maka da naga wannan rana Daddyn Hameed. Wlhy bakaji yanda naji wani irin shock ba. Wannan ai abun farin cikine a garemu, dan wata hanya ce ta samun ha in kan yaran nan ne da muketa fata tuntuni. Ni Huznah ta biyani ALLAH yay mata albarka Humm Asia! Shin ba ya tunanin akwai wani dalili? Haba Daddynsu wane dalili kuma? Dan ALLAH kada ka atama yarinya yawar niyyarta mana Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, acan asan ransa yana sake jin matu aunarta da jin alfahari da ita. Ita in ta dabance a duniyarsa. Shi yasan da sauran ne cikin an Asia wani yace zai je gidansu sai anyi bala'i kuma ace wani daliline zai kaisu. Amma ita gashi maimakon tai zaton sharri kai tsaye saboda komai a bayyane yake sai tayi na alkairi. Jawota kawai yay jikinsa ya rungume. Murya a raunane ya ce, Asia ALLAH yay miki albarka kinji. Tabbas UBANGIJI yamin babbar ni'ima da samunki Nima haka Daddyn Hameed, kai in babbar ni'ima ce a gareni daga cikin ni'imomin UBANGIJI na. Bani da abin fa a sai cigaba da godiya a garesa Sosai ya saki murmushi mai ayatarwa, sai kuma ya sake kai hannu ya rungumota tare da arin ha e bakinsu. Da sauri ta kauce tana dariya, sai ma ta zare jikinta gaba aya ta mi e daga kusa da shi. Fuska ya ata da mata nunin ta dawo amma ta ma e masa kafa Shike nan ni kike ma rowa ko? Murmushi ta masa kawai. ara jinjina kansa da nufar ofa yana fa in, Zan rama . Ya fice. Nan ma murmushin kawai tayi, sai da taji ficewarsa daga sashin gaba aya ta koma jagwab a saman gadonta zuciyarta na wani irin harbawa. _(Jiya Huznah da uwarta sun sameni wai tana son zuwa wajen ar uwarta Shahidah tai sati aya)_ kalamansa suka shiga dawo mata cikin kunne da amsa kuwwa. A bayyane cikin dafe kanta ta ce, Ya ilahil'alamin Basariyya mi kike shirya min kuma? Ni nasan dole wannan zancen akwai wata a . Rashin mai bata amsa yaa sata yin shiru ta cigaba da zancen zuci. Ta jima a haka kafin hankalinta ya dawo jikinta ta mi e ta shiga kitchen ha ama su Waleed abincin breakfast dana tafiya makaranta. Tana aikin tana tunani nan ma harta kammala. Tana cikin ha a musu suka shigo sanye da uniform insu. Duk gaisheta sukayi suna mai rungumeta, tai musu murmushi tana amsawa. Har an shirya an makaranta? Kawunansu duk suka shiga aga mata. Sai kuma cike da shagwa a irin ta autoci Waleed ya ce, Ammie mikika dafa min? Oh tama dafa maka bata dafa mana ba, kuji min an iya . Cewar Hameed yana hararsa da kai dankali bakinsa. Murmushi Ammie tai da fa in, Ni dai kunga kuyi ku wuce bana son surutu yau in nan. Kowa ya duba abinda yake so shi aka dafa masa Murna suka shiga yi, sai kuma suka auki wanda zasu ci suka koma work table dake kitchen in kowa yaja kujera sukai zaman ci. Ammie kuwa ta fara an wawwanke kwanikan data ata dan bata son taga ambar kaya da datti, duk da tasan yanzu mai aikinta zata zo ta fara aikin ta gwammace ta tsaftace wa an nan in kafin ta iso. Tana kammalawa suma suka kammala. Sallama sukai mata kowa ya auka lunch box insa suka fice. Sai kuma six dan makarantarsu tana tare da islamiyya ne... Koda ta koma aki saita gagara shiga wankan datai niyya, zama tai ta auki waya ta shiga kiran Nene. Ba'a wani auki tsawon lokaci ba Nenen ta amsa kuwa. Sai dai suka gaisa da tambayar juna gida kafin Ammie ta ce, Nene yau zan sameki a gida? Daga can Nene ta ce, Eh bazanje ko'ina ba. Dama nina naso kiran naki ai sai kika kirani, zaki shigo ne? Eh Nene indai ya bari zuwa anjima ka an zan shigo To shike nan sai kinzo in ina saurarenki Daga haka sukai sallama kowa ta yanke..... Sai kusan sha biyu Ammie ta samu damar barin gidan. Dan da yar Daddy ya barta dan ma tace masa kitso zataje. Da yake yasan tana zuwa kitson kuma bai kawo komai a ransa ba. Shi irin mutanen nan ne da sam basa son yawan fitar iyalansu, sunfi bu atar ko yaushe kina gida, shiyyasa a cikinsu babu mai fita aiki ko wani business. Ammien ce ma taga bazata iya wannan kashe kan ba komai sai abinda namiji ya baka tuni ta fara kasuwancinta a gidan Nene. Kuma Alhamdullah komai yana tafiya dai-dai. Gidan Nene gida ne a matsayin family house. Dan kuwa ita da duka matan anta suna a cikinsa. ALLAH yayima mijinta rasuwa tuni, ita ta cigaba da gwagwarmaya da yaran har suka girma. Yanda ta horesu yasa duk suna da sana'o'in su, dan babu mai zaman banza. Badai ku i garesu ba amma ci da sha gwargwado da sutura irin ta gidan mai rufin asiri sun wuce da wannan kam. Sashen Babban an Nenen ta fara shiga, matansa biyu, yaso auren Ammie a baya matarsa nata zuba rashin mutunci akan hakan sai ALLAH ma bai addara ba, to ashe kishiyar dai na bibiyarta, dan bayan Ammien tayi aure ya auro budurwa gal a leda yanzu haka haihuwarta uku a gidan itama. Wannan dalilin ne yasa sama-sama suke da Ammien. Koda ta shiga a kitchen ta samu Maman Salima kamar yanda suke kiranta, ta wani zubama Ammien ido zuciyarta na bugawa, tuni murmushin fuskarta kuma ta ace. A yanzu kam ba kishin Ammie ne ke damunta ba hassada ce. Ko'a jikin Ammie ta gaisheta da tambayarta yaranta. Daga kitchen in ta amsa a da ile, sai dai idonta na'akan suturar jikin Ammie. A'a Aunty Asiya ce a gidan namu? Amarya dake le owa daga falonta ta fa a. Murmushi Ammie tai mata da fa in, Aiko nice Amarya To sannu da zuwa Bismillah ki shigo Babu musu Ammie ta shiga, falon al an gyara shi sai amshin turaren wuta yake kamar bamai ananun yara ba. Gashi da gani tana fama da laulayin wani cikin ne ma. Cike da girmamawa ta gaida Ammie kafin ta fita sai gata da ruwa. Ammie ta ce, Amarya ai da baki wahala ba ma. Ina yaran nawa ko duk an wuce makaranta? Duk sun wuce shiyyasa ai muka samu lafiya Aunty, sai Ameen kawai yana barci ne A'a ai shima ko ya kamata a sakashi makarantar tunda naji bakinsa akwai surutu cikin dariya Amarya ta ce, Sosai kuwa Aunty Bayan Ammie ta sha ruwan ta fito, amarya biye da ita har ayan sashen. Nan kam mace aya ce, itama ta amshi Ammie da girmamawa da mutuntawa, bayan sun gaisa ta fito ta shiga wajen sauran suma su biyu. Daga haka ta shiga wajen Nene. A falonta ta sameta zaune ta baje kaya tanata lissafi. Sai wata dake gefenta tana tayata. Da mamaki Ammie ta furta, A'a Saratu yaushe a gari? Nene shine baki sanar min munada da ba uwa ba? Murmushi wadda aka kira Saratun tayi, yayinda Nene ta an ta