← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 104

Sashe 90

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba ko sau aya. Sai dan kawai kar ace yama iyayenta rashin halacci ya kasa ri eta. Shima namiji ne, yana son ya auri wacce yake so, yana son haihuwar a namiji.. kai tujara dai kala-kala data sanya Shahidah da Amaal kuka sosai. Ita dai hajiya Maanal hidima bata san ma anai ba. Tana can tare da Baba Haruna daya fita da ita gaisuwa gidan wani abokinsa. Ammie tayi kuka har ta godema ALLAH, taji inama iyayenta na raye, ashe duk zaman da take da Babu ba soyayyarta a ransa har zuwa yanzu... Anyi haka da kwana hu u Babu baya kulata hakama an gidan kowa ya ara auke mata wuta ita da anta sai ga batun yima Shahidah da Amaal wai baiko. Ranar ji Ammie tai kamar tabar duniya ta huta. Karon farko ta sami Baba Haruna da ro o. Yayi mamakin jin bada son ranta ake shirin auren yaran ba. Dan shi Babu ya nuna masa komai da amincewarta ne. Lallashinta yayi akan hakan, yace taje zai zauna da an uwansa akan al'amurin. Wannan ya sakata an jin sanyi a ranta. Sai dai me, koda Baba Haruna ya zauna da an uwansa duk sai suka kasa fahimtarsa, arshe ma mahaifiyarsa da har yanzu tana a raye duk da ta tsufa sosai ko tafiya bata iyayi sai tace idan bai bari amma yaran nan aure ba bata yafe ba. Hauka ake yara sunyi zagada-zagada ace an barsu babu aure. Ko so yake suna a musu irin yanda Umaru yay ma ita Asiya in kamar ar arna sai da ta shekara ashirin a gida. Wannan yasa dole Baba Haruna ya bar maganar, ya kuma dinga lallashin Ammie. Ina hankalin Ammie ya kasa kwanciya, dan ko ma iyinta bazata so ya kasance cikin wannan zuri'ar ba balle iyanta. Balle kuma yara anana kamar su Shahidah. Inama udan yake ballantana romonsa. Komai yama Ammie tsanani, dan sun tabbatar mata bazata koma da su Shahidah ba. Maanal ma za'ayi mata miji da lokaci yayi su dawo da ita gida. Ranar da aka saka ranar auren daya kasance sati hu u kacal Ammie batai kwanan lafiya ba. Dan jininta hawa yayi ololuwa sai a asibiti ta kwana. Duk da wannan halin da take ciki sai zaginta mutane keyi wai kishi ne. Tana kishi dan mijinta zai ara aure. Babu wanda yay mata uzuri akan anta da ake shirin musu auren fin arfi. Washe gari ta an samu dai-daito, iya tunaninta ta rasa wazata tunkara ya taimaketa ya ku utar mata da yaranta, anwar mahaifiyarta Shamsiyya kawai ta sani, itama a yanzu bata san duniyar da take ba. Dan tun bayan rasuwar iyayenta bata sake ganinta ba. Minna kuwa dama ba zuwa take ba tunda babu wanda ta sani sai kakanta ko'a lokacin, sai matarsa mara mutunci, yanzu kuma babu shi wajen wa zataje?. Wannan mutanen sune dangin mahaifinta, su kawai ta sani. Sai su Oum da suka zame musu an uwa yanzu a garin Kano. A wannan karon kam sai kawai ta yanke shawarar kiran Oum in, dan itace kawai mafitar data rage mata. Bayan ta gama zayyanema Oum komai tana kuka itama Oum in kukan take. Da yar suka lallashi juna Oum tace ta saurareta zatai magana da Aban Fadeel in sha ALLAHU za'a ku utar da su Shahidahn daga wannan auren. Wannan waya itace ta sanya Ammie jin an sanyi a ranta, har jininta ya an sauka aka sallameta daga asibitin a ranar.... Washe gari kusan azhar saiga Amaal data fita sayo mata fura ta dawo cike da oki. Kallonta Ammie da Shahidah keyi, sai kuma Shahidah ta ce, Ke kuma ina furan? Kin san fa Ammie bataci komai ba ga magani zata sha Zama Amal tayi da fa in, Yanzu zan koma na sayo, Abah na gani a waje tare da Ajwaad Da mamaki Shahidah ta ce, Aban Kano wai? Cike da zumu i Amal ta amsa mata da Ba aramin waro ido Shahidah tayi ba. Yayinda Ammie ta saki murmushi mai fa i tana rufe idonta sai ga hawaye sharrr. Da sauri tasa hannu ta goge kafin yaran su gani, wata irin aunar Oum na ratsa mata zuciya da ruhi. Kallon Maanal dake barci sukai, Shahidah ta ce, Lallai yau da bidiri a gidan nan ga Bestyn Maanal a Giro . Dariya Amal tayi tana matsawa kusa da Maanal in ta shiga tadata. Da fa a kuwa ta tashi, dan dama fa an sukai da wata yarinya a gidan ta fasama yarinyar baki shine Ammie ta daketa tai barcin dole. Dan uwar yarinyar har sashen tazo tana fa in bazata yarda ba sai ta daki Maanal, yarinya duk tabi ta addabar musu yara. Ha uri Ammie taita bata amma matar nan sai da ta gama cima Ammie mutunci da gori sannan tabar sashen. Hakkanne ma ya saka Ammie kasa cin abinci dan kanta wani irin ciwo yake mata mai zafin gaske...... A cikin gidan ma tuni labari ya kai musu daga bakin yaransu. Kasancewar duk suna a ainahin babban tsakar gidan kowa na ayyukansa. Masu surfe, masu sakar mahucin kaba, bamu hira, masu sana'oinsu. Sun auki in zance sai ga wani almajiri ya shigo hannunsa ni i-ni i da kaya wani matashin yaro biye da shi. A zahirance dai yaro ne, dan dudu bai wuce shekaru goma sha ba. Sanye yake cikin ananun kaya na jeans daga wandon har jacket in saman duk sky blue. Sai rigar ciki data kasance red haka ma belt insa da boot in takalmansa. yawar fuskarsa sakaye da farin siririn gilashi mai shegen yau da a kallo aya zaka fahimci mai tsada ne duk da kuwa na arin gani ne. Tafiya yake a nutse babu hayaniya balle garaje, kallo aya kuma yayma tarin matan dake cike da tsakar gidan ya kauda nasa idon ganin yanda suka zuba masa idanunsu har yana jin tsigar jikinsa na tashi. Cikin muryarsa mara arfi da hayaniya ya gaishesu a jimlace batare da ya damu da sunji ko basu jin ba, shi dai yana biye da almajirin nan da kai tsaye ya nufi sashen Gwaggo. Sun a gab da shiga sai ga Maanal a guje ta fito har tana ture almajirin. Kanta tsaye Ajwaad tanufa, shima da ya jiyo ihunta tuni ya tsaya cak yana kallonta. Ko damuwa da yanda jikinta yay bu u-bu u da asar danben da sukai kafin tayi barci ma baiyi ba. Tuni ya bu e mata hannayensa tazo ta shige jikinsa. Yako agata camak sama yana juyi da ita illahirin fuskarsa na washewa da wani irin sassanyar murmushi daya bama an gidan mamaki. Dan daya shigo sam babu alamar fara'a a tattare da shi. Sai da yay juyi sosai da Maanal dake yala dariya kafin ya sauketa, sai kuma ta sakar masa kuka. Zuru yay yana kallonta, sai kuma ya kai du e a gabanta dan ya fita tsoho sosai, duk da kasancewarsa yaro shi in dogo ne kamar sauran yayunsa da mahaifinsu. Tuni fuskarsa ta koma ta tsuke daga murmushin da yake, idanunsa farare tas da kamar an watsa madara sun fara canja launi. Is something bothering you? . Ya tambaya kamar wani babba yana tsatstsareta da idanunsa. ara arkewa Maanal tayi da kukan iskanci, tare da fa in, Ni tare dakai zan koma. Bana son nan mugaye sunyi yawa. Kullum su Safare sai sun dakan, Ammie ma haka, su Didi ma suyita zaluntata. Wicked old woman in can taita min harara da zagina tana cemin shai aniya. Kowa cutata yake anan auyen Baffa ne kawai ke sona da saya min kayan da i. Kuma dama na fa ama su Lami duk randa kazo saika rama min duk abinda suke min. Sosai acin rai ya bayyana a fuskar Ajwaad. Har yama ji ya kasa magana. Dan shi fa idan kana son kaga ainahin fushinsa to kuwa ka ta a Maanal. Ko Ammie da Babu dan baida yanda zayi ne kawai.... Ajwaad! Sassanyar muryar Ammie ta saka shi janye idanunsa daga kallon Maanal ya maida ga Ammien. Murmushi ta sakar masa da fa in, Kaga tashi kaji karka biyema wannan ibilishiyar. Kadai san halin mutuniyar taka maza taso Dan Ammie ce kawai ya tashi, hannunsa ri e dana Maanal suka shiga. Su Shahidah na masa sannu da zuwa yana faman balla musu harara. Amaal daba barin saita kwana take ba itama tai saurin fa in oh har an kai maka munafuncinmu kenan? Caraf Maanal dake nani e da shi ta murgu a mata baki da fa in, in an fa a, kuma duk abinda kuka min sai ya rama min har ma Ammie ko Besty? . Tai maganar tana kallon AA. A hankali ya jinjina mata kansa, sai kuma ya ce, Amma banda Ammie . Fuska ta ata sai kuma ta sanya kuka tana turza afafu. Ni dai harda ita Besty, kullum fa sai ta dakan, yanzu ma ta daken ta sani barcin dole..... An dake kin, oh ni Asiya nima arar tawa kika kawo wajen Ajwaad . Ammie ce tai maganar tana ajiyewa Ajwaad ruwa a gabansa. Sai kuma ta zauna idonta na harar Maanal ta ce, Karma ka bari ta ata maka rai kaji Ajwaad. Yarinyar nan tabi ta fitini an mutane a gidan nan, kullum babu ranar banza saita fasa kan wani an kota jawo min magana. Fitinar Maanal ta isheni wlhy. Kuma ALLAH in baki min shiru ba zan miki duka agaban Ajwaad Sarai Maanal ta san halin Ammie, tanada zafi akansu, sanyinta akan Babu ne kawai da mutanen gidan nan nasu. Mu ut ta ha iye kukan tana mai lafewa a jikin Ajwaad. Cikin maganar nan tasa sanyi-sanyi ya ce, Ammie kiyi hakuri, amma idan bata ramawa ai sai suyita dukanta. Yanzu ma jiba duk yanda ta rame tai ba Baki Ammie ta saki tana kallonsa. Yayinda Shahidah da Amaal ke kwasar dariya. In dai Ajwaad ne zai yi fiye da haka akan Maanal, dan haka Ammie ta ce, Shike nan ai dama kai ke aure mata ugu, amma dai kubi a hankali, dan ina tsoratar muku randa hajar mai gari zata tsinke Babu dai abinda Ajwaad yace, amma Maanal sai tura baki take yi. Koda aka kawo masa abinci bai iya ya nutsu yaci ba sai da ya dinga bama Maanal a baki. Itama sai ta dinga amsar spoon
Chapter 90 · 0% Book details