← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 104

Sashe 50

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 2 min read

gaba aya sai sake sakani a wani irin dogon tunani mai rikitarwa kuke wlhy Aunty, wacece Maanal a wajenku dan ALLAH? Ya akai kuma ni ban santa ba? Ai kwantar da hankalinka Uncle kada ka wani ru ar da kanka. Maanal dai iyar Oum ce, mu kuma anwa ce. Abinda yasa baka santa ba lokacin da mukai zaman Kano ne, kai kuma sannan kuna Paris Da mamaki RK yace, Kenan har AA ya santa? Su dukansu juyawa sukai suka kalla AA in da furucin RK in ya wani daki zuciyarsa, hakan ya sashi tsayawa cak da karatun da yake duk da dama tun azun ba fahimta yake ba. Kai Fawzan ya jinjinama RK. Sai kuma ya ce, Tabbas ya santa Cike da mamaki RK da ke kallon AA ya ce, Lallai, amma gaskiya na sake yarda kai abin tsoro ne AA. Amma shine koda wasa baka nuna min kasanta ba. Aunty kusan fa 3 weeks da fara aikin Maanal a companynsa shiyyasa kikaga inata ara jinjina mamakina ai Kallon juna Oum da Fawzan sukayi, sai kuma suka kalla AA in da har yanzu dai yana a yanda yake, sai ka rantse baya falon ko kuma baya jin mima suke fa a akansa. Fawzan ya girgiza kansa kawai da murmusawa, Ai autan Oum sai addu'a Uncle. Little kice har an kammala karatu? ya maida hankalinsa ga Maanal. Idanunta ta janye daga satar kallon AA in itama. Ta amsa ma Fawzan da, Eh Yaya har sarvese nayi Kai Masha ALLAH, kinga rigimarki ta saka kin kammala karatu da arancin shekarunki, kai Little rigima Hannu Maanal tasa ta rufe fuskarta dan tuna baya. Yayinda Oum keta dariya itama tana tuno abubuwa kamar labarin Film. A mamakin su sai sukaga AA ya mi e batare da yacema kowa komai ba ya nufi hanyar ficewa daga falon. Da kallo kawai suka bisa.... Sai da ya taka step na farko batare daya jiyo ba ya ce, Oum na wuce massalaci . Murmushi Oum tayi da masa addu'a, yayinda RK ya mi e yana fa in, an rainin hankali shine bazakace mu tashi lokacin salla yayi ba . Fawzan ma mi ewa yay yana dariya. Sai kuma ya fara raira wa ar Hamisu breaker _ ar Arewa_.
Chapter 50 · 0% Book details