Sashe 15
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
asibiti. Sai baba maigadi ne daya iso wajen a hargitse yake fa in asibiti ya kamata a tafi. Da wannan magana tashi suka zabura gaba aya. Cak Yazeed ya auki Maanal daketa aman jini ya nufi hanyar gate a maimakon motocin gidan saboda tsabar yanda ya rikice. Shahidah, Amal, Ammie suka take masa baya sai Amara da itama ta zabura ta bisu tana kuka. Fitowar Yazeed dai-dai da isowar RK ofar gidan, dan haka a cikin rikicewa Amal ta bu e motar RK in kawai tana cema Yazeed in ya shiga batare data tantance motar waye ba itama. Shima bai wani tantance komai ba ya saka Maanal a ciki, da sauri itama Ammie ta shiga ta rungumeta tana kuka da fa in, Haba Maanal ya zaki mun haka, dan ALLAH kiyi ha uri kada ki tafi ki barmu mu muna sonki, muna tsananin aunar Maanal. Muna bu atar ki a duniyar mu Maanal... Wannan furuci na Ammie shi ya zaburar da RK da ya tsaya yana kallon ikon ALLAH, sai kuma lokacin ya gane Ammie da Amra dake kuka. Duk da halin da Maanal ke ciki itama bai gagara ganeta in ba. Ai da wani irin tashin hankali ya tada motar, Yazeed ya shiga kusa da shi suka bar anguwar. Napep Amal da Shahidah da Amrah suka tare suma suka bi bayansu.... Yazeed ne ya fa a masa asibitin da zasu je, inda Maanal ke ganin likita kenan. Asibitin ku in ne, kasancewar kafin su isa ma Yazeed ya kira abokin nasa doctor Nazeer ya sanar masa zuwansu suna isowa suka samu nurses har hu u da Doctor Nazeer in kansa na jiransu a waje. Da yar aka iya are Manaal daga jikin Ammie. A kallo aya idan kai mata zakai tunanin bazata sake rayuwa ba. Dan yanda take yun urowa irjinta na agawa tana aman jinin ka ai ke nuna akwai sauran numfashi a tare da ita. A haka dai aka shiga da ita ciki kowa a ki ime. Dai-dai nan suma su Shahidah da suka biyosu a napep suka iso... Abu kamar wasa sai ga aramar magana ta zama babba. Dan yanda doctors ke shiga da fita akin da aka shiga da Maanal basa ko sauraren kowa zai tabbatar maka al'amarin yayi tsamari da yawa. Dan har zuwa goman dare babu wani bayani mai da i. Zuwa sannan Nene ta iso, (Nene anwar mahaifiyar Ammie ce da yanzu take kallo kamar mahaifiya. Zamu iya cewa ma ta sandinta Ammie da anta suka zo cikin Kaduna. Ita a anguwar dosa take, ita da zuri'arta. Dan itama yaranta hu u duk maza a yanzu haka duk suna da aure da ansu suma, sai aya ce kawai mace itama dai tayi aure). Har wannan lokacin RK na asibitin, hasalima tuni ya shige cikin likitocin da shi ake bama Maanal taimako kasancewarsa shima wararren likita masani a fannoni da dama daya shafi aikin. I'd card insa kawai ya nunama Doctor Nazeer ya amince masa shiga cikinsu aka rufu kan Maanal. Haka shina Yazeed tsaye yake da afafunsa. Duk abinda akace ana bu ata kafin wani dogon lokaci zakaga ya kawosa. Sai su Ammie suka kasance an addu'a da share hawaye. Daga can gidan dai babu wanda ya biyo bayansu, sai dai Yazeed ya kira mahaifinsu ya sanar masa. Ya kuma tabbatar masa a yau in nan zai baro inda yake zuwa Nigeria. Domin shima hankalinsa yay matu ar tashi bana wasa ba. Koda yasa Yazeed ya ha ashi da Ammie kasa magana tayi sai kuka data fashe masa da shi kawai. Sai hakan ya sake birkita masa lissafi gaba aya babu shiri ya fara neman ticket ta online...... ___________ Alhaji Usman Chalawa bai iso ba sai washe gari wajen misalin arfe aya na rana. Babu wanda yasan da dawowar tasa a cikin matansa, dan hatta ita ma Ammien bai sanar mata ba. Sai Yazeed kawai ya sani. Shi kuma tashin hankali ya mantar da shi sanar ma kowa sai da Daddyn ya tura masa sa on yazo ya aukesu sun kusa sauka sannan ya tuna. Ya bar asibitin ne dai-dai lokacin RK na bada shawarar yima Maanal transfer zuwa Abuja. Dan gaskiya jikin nata sam babu da i. Su kansu likitocin sun fara karaya, RK in ne ma ke arfafasu duk da shima gwiyawunsa a sare suke yana dakewane kawai da arfafa kansa... Kai tsaye asibiti Yazeed yayo dasu Daddyn. Rungume Ammie su Waleed sukayi, yayinda take kallon mijin nata cikin karaya idanunta cike da walla. Cike da kulawa ya girgiza mata kansa alamar kar tai kuka. Sai kawai tai asa da kanta tana mai rungume Hameed da Waleed sosai a jikinta. Idanun nasa ya auke cike da damuwa ya maida kan su Shahidah dake gaishesa. Ya amsa musu da kulawa yana tambayarsu mai jiki. Maimakon amsa sai suka fara hawaye suma. Jiyay gaba aya zuciyarsa ta ara karaya, da yar ya iya gaishe da Nene, sannan ya wuce office in doctor inda suke meeting shi da su RK. Doctor ne yay ma RK bayanin matsayin Daddy a wajen Maanal duk da tare da Yazeed suka shigo, dan RK bai oyema doctor ala arsa da Maanal in ba. Cikin girmamawa RK ya rissina ya gaishe da Daddyn. Nan ma doctor ya sanarma Daddy RK likita ne, ya kuma masa bayanin shawaran da suke akai yanzu haka game da maida Manaal in Abuja. Babu wani musu Daddy ya yarda, tare da arfafasu cewar ayi komai yanda ya kamata ama bar ata lokaci, bari yaje ya bincika ko akwai jirgi mai wucewa yanzu sai su wuce a ciki zaifi mota sauri.... Hakan kuwa akayi, dan zuwa la'asar an gama shirya Maanal zuwa tashar jirgin asa. Zasuyi gaba harda Nene da su Shahidah. Ammie kuma sai zuwa gobe in ALLAH ya kaimu da safe zasu bisu ita da Daddy kamar yanda ya bu ata. Suna isowa Abuja ambulance ce tazo ta auki Maanal dan tuni RK ya gama booking komai. Shi da Yazeed ne suka bi ambulance in, yayinda mijin Shahidah da yazo shima ya auki su Shahidah in da Nene da Amal. Yaran duk suna Kaduna sai gobe idan ALLAH ya kaimu Ammie zata taho da su nan. KK HOSPITAL asibiti ne mai tsanani yau da kowa ya sani a cikin Abuja. Suna da wararrun likitoci da suka san aikinsu warai da gaske. Suna ari matuka wajen bama mara lafiya kulawa yanda ya kamata, ga sau in kashe ku i dan talaka da mai arzi i duk zasu iya biya. Babu wani ata lokaci cike da kulawa aka shiga da Maanal, yanda ake girmama RK a asibitin yasa suka fahimci eh lallai yana da wani matsayi babba a wajen......... ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ Abubuwan da nake saidawa Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries __________ .......Yau kwanakin Maanal biyu a KK HOSPITAL. Zamu iya cewa Alhamdullahi abubuwa sun fara dai-daita, duk da dai har zuwa yau ba'a barin kowa shiga inda take sai doctors kawai. Tun a jiya su Ammie suka iso suma ita da Daddy. Tsabar munafunci na Hajiya Basariyya sai ta ce zata biyosu taga jikin Maanal in. Dan a waccan ranar da Daddy ya dawo tunda ya koma gida ya rufesu da fa a ita da Hajiya Yaya akan in zuwansu asibiti, sai dai fa an nasa yafi tsamari akan Hajiya Yaya d ata zama itace sanadin komai, dan yama sanar mata ya haramtawa Sabuwa zuwa masa gida, idan kuma tai gigin zuwa ALLAH sai ya saka jami'an tsaro sun kamata. Itama kuma ta jira hukuncinsa bayan Maanal ta warke dan yanzu baida lokacinta. Tofa wannan abu da Hajiya Basariyya dake la e taji yasa ta dawo ta lalla a Daddyn ta bashi ha uri akan nata laifin daya fa a na in zuwa asibiti kawai, ta kumaji duk halin da ake ciki akan maida Maanal Abuja shine ta ma ale itama zata bisu. Ammie bata san da batun ba sai da suka fito zasu wuce taga Hajiya Basariyyan. Sosai ta sake jinjina makircin matar a ranta, dan ta jima da gane wacece Basariyya, sai dai bata ta a nuna mata ba ta barta da halinta. A lokacin ma murmushi kawai tai batace komai ba, hakan kuma sai ya onama Hajiya Basariyyan rai, ta rasa wacece Ammie, ta rasa ta inda zata kamo lagon matar, ta rasa ta inda zata shiga jikinta kamar yanda take shiga jikin Hajiya Yaya tasan sirrinta. Amma ba komai, idan tasan wata ai bata san wata ba. Anan Abujan itama ta kwana dan Daddyn nada gida anan in dan yana harkar sayen gidaje da sayarwa ne. Kasancewar komai akwai a gidan yasa sauka kawai sukai anan in. A yanzu ma haka tana a asibitin tare da su. A akin da aka kwantar da Maanal akine na musamman kamar palor da bedroom, dan haka duk suna a palor in zaune itama Maanal na daga ciki babu mai shiga sai dai su le ata ta jikin ofar glass in. Shahidah da Amal suka iso auke da abinci, bayan duk sun gaishesu suna arin zama Daddy da RK suka shigo akin sai wani ba'indiyen likita da shine akan case in Manaal in ma. Gaishe da Daddy su Shahidah sukayi, sannan suka gaisa da su RK da suma suke gaida su Ammie. Su RK na arin barin wajen kamar daga sama sai Hajiya Basariyya cewa tai, Nikam likitan nan kamar na sanka . Yanda tai maganar idonta akan RK ya sakashi fahimtar da shi take, kallonta ya an yi sai kuma ya rissinar da kansa tunda bai san matsayinta ba a