← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 104

Sashe 35

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

bamu da maraba da marayu da suka rasa mahaifi da dukkan dangi. ALLAH ne gatanmu sai Ammien mu sai kuma Nene kawai sai kammu. Dolene fa mutattara komai daya faru a baya mu zubar da shi muyi mantawa irin ta AJIYA A DUHU duk da nasan akwai tabo da bazai ta a goguwa ba a zukatanmu amma komai na ALLAH ne. Sannan dole musan kammu mu kuma gina gobe yaranmu masu tasowa. Maanal Daddy ya ri emu babu banbanci da an daya haifa a cikinsa tunkan Ammie ta haifa masa Waleed da Hameed. Kuma muma a yanzu babu wanda mukema kallon uba sama da shi. Sai dai fa mu sani iyakarmu kiransa uban ne kawai a iyakar kayinmu, amma a wajen al'umma sunanmu AGOLOLI a gidansa. Maanal ba fata nake ba, amma ki sani a yanzu ALLAH ya auki rayuwar Daddy wlhy ko Amminemu bazasu bari ta rayu a wannan ahalin ba. Saboda su Waleed anana ne, basu kai girman da zasu wata mata anci ba. Mu kuma komu yarda ko karmu yarda munada iyakarmu a gidan nan. To mikike tunanin ya kamata muyi? Wannan aikin tu uru domin gina gobemu da goben yaranmu. Bazamu so mu sake maimaita rayuwar baya ba Maanal, bazamu so mahaifiyarmu ta sake maimaita wahalhalun data sha a kammu ba a shekarun baya, idan sannan muna da uruciya yanzu munkai girman share mata kukanta, mun girma Maanal mun girma Kuka ya sar eta. Suma duk sai suka fara kukan, koda yake dama Maanal ita tuni ta fara hawaye. Kusan mintuna biyu Shahidah ta share hawayenta da cigaba da fa in, Maanal bamu san mi gobe zatazo mana da shi ba. Dan muma mata ne. Idan har Ammie zata iya riskar kanta a irin rayuwar da mukai a shekarun baya bai kamata mu mushagala da tunanin komaima bazai faru ba saboda a yanzu rayuwarmu ta inganta. Karfa mu manta da irin labarin gata da rayuwar Ammie tasha a hannun iyayenta, amma hakan bai hanata fuskantar alubale ba a hannun mijin aurenta da kowa ke gani hakan bazata faru ba. To muma bai kamata ganinmu a cikin irin wa an nan manyan gidajen yasa mu shagala ba. Bai kamata mu cigaba da zaman jiran kullum a mana ba. Saboda haka ki dawo cikin hankalinki Maanal, ki tuna su waye mu a yanzu. Ki ajiye abinda ya wuce baya ki manta da shi, ki kaishi cikin duhuwa ki ajiyesa tamkar ma ba'a ta a yin komai ba. Yanda Ajwaad ya nuna bai sanki ba ki zama JARUMA kema ki nuna baki sanshi ba, ki manta da shi, ki manta da abinda ya shafesa, ki tsaya da afafunki, kisa a ranki shi bai isa hanaki kaiwa ga cikar burinki ba, karki wani damu da zamowarsa shugaban kamfanin ko matsayin nasa ke aiki ya kaiki domin kanki. To kiyi kuma aiki tu uru a companyn nasa domin kanki da cigabanki. Maanal ki duba yanda Rafeeq ke hidima dake da son ganin farin ciki ki, hatta Yazeed ma ni wlhy ban ta in kasantuwar aurenku ba saboda mutumin kirki ne. Koba komai yasan mutuncin mahaifiyarmu, ya taimakemu a lokacin da muka rasa taimako daga jininmu ma. Kawai mahaifiyarsa ce matsala. Idan kuma da alkairi a zamanku sai ALLAH ya auketa ku zauna in babu yanda zatayi. Amma dan ALLAH ki amshi al'amarin Rafeeq ki gwada ki gani shima. Ki kwantar da hankalinki addu'ar mu na zagaye dake ki manta da baya, ki saka a ranki addarar data gitta rayuwarki bazata hanaki aure ki zauna a gidan mijin ba har kuma ko samu farin ciki fiye da zatonki. Dan ALLAH shine shaida baki je kin aikata dan son zuciyarki ba. Dan haka ki manta komai, dan ALLAH ki manta komai kije ki fara aiki, abu nagaba kuma kiyi arin fidda mijin aure tsakanin Rafeeq da Yazeed kodan ki tabbatar ma Ajwaad kina rayuwane domin kanki. Dan kuwa cikakkiyar amsa kika samu a jiyanki game da shi, idan a baya hasashe kawai mukeyi bisa dalili yanzu ya tabbatar miki shi da kansa Sosai Maanal take kuka yanzu kam, Amal ta jawota jikinta ta rungumeta itama tana kukan, sam basa son tunawa da bata, basa son tunawa da addarar data ratsa rayuwar autarsu, basa so ba sa so. Cikin rawar murya da son ture komai Amaal ta ce, Duk abinda Didi ta gaya miki shine gaskiya wlhy Auta. Ki dake zuciyarki kiyi abinda ya dace da rayuwarki a yanzu. Ki manta da abinda ya wuce kamar ma ba'ayi komai ba. Koda wasa kada ki zubda daraja da kimarki ta iya mace. Ki amshi addarki kamar yanda muma muka rungumi tamu. Hakan da zamuyi sai ya ara arfafa Ammien mu, ki duba kiga rayuwar data baro, mai cike da tarin gwagwarmaya amma a yanzu ALLAH ya mata canji, canjin kuma baisa ace babu wasu jarabawoyin ba kuma. Tunda anan in ma tana fuskantar alubalen bawai sun are bane. To haka rayuwa take duk yanda ka kai ga samun sauyi da nasara da jin da i dole addararka aminiyar NUMFASHINKA ce Maanal. Tare suke tafiya a jefe afa da afa. Aminan juna ne tamkar gangar jiki da numfashi. Hakama jarabawarka abokiyar gangagar jikinka ce. Kinga ko har abada babu ayan da zai rayu babu aya a tsakanin gangar jiki da numfashi ko? .........
Chapter 35 · 0% Book details