Sashe 7
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ambaliya a saman yawar fuskarta. Amaal da dama tun azun hankalinta ke kanta ce ta araso wajen da sauri. Kamota tai cikin rawar jiki tana tambayarta mike faruwa? Maimakon amsa sai ta fa a jikinta kawai ta rungumeta tsam ta saki wani sirrin kuka mai ban tausayi. Rikicewa Amaal in tayi, hakama Didi Shahidah tuni ta taso ta nufosu. Ammie ce dai kallo aya ta musu ta kauda kanta gefe, dan ta aura ammarar itama bazatai sanya a wannan karon akan Maanal in ba. Ta gaji da zamanta haka gara ai auren nan ko hakan zaisa ta manta da baya. Tana jiyo yanda an uwanta ke sake jera mara tambayoyi a rikice batabi takansu ba tama tashi tabar falon zuwa bedroom in ta. Bakin gado takai zaune tare da fara sarrafa wayarta, sai kuma ta kaita kunne alamar kira tayi. Babu kuwa jimawa aka aga daga can, bayan sun gaisa da tambayar juna iyali ta fara magana kamar haka. Nene na kiraki ne akan ar gidanki, yau dai ta dawo an kammala service . Ta an yi shiru alamar saurare. Sai kuma tai murmushi da cigaba da fa in, Shine ma dalilin kiran naki Nene. Dan anyi sa'a shima Yazeed in yana gida yazo wani aiki kuma zai jima kamar yanda ya sanar min. To sai nake ganin hakan damace da za'ayi kawai a huta. Dan nagaji da wannan age- agen saka ranar auren nasu shi kuma Baban nasu na biye mata. Gara ayi a huta, idan taga abin bawasa bane tama arasa nutsuwa. Saboda na fahimci Maanal fa bazata ta a kasancewa a yanda ake bu ata ba a haka gaskiya. Amma shi idan suka je can zai san ta yanda zai arasa mantar da ita komai dan yaron nada hankali da nutsuwa. Banga abinda Yazeed bai mallaka ba da mace bazatai alfahari da shi ba ako'ina matsayin miji . Nan ma tai shiri tana saurare. Ta jima kafin ta amsa da, Ni abun sake bani tsoro yake. Yanzu haka bakiga yanda ta dawo a fige ba wannan karon kamar kazar fakat. Al'amarin Maanal na tayar min da hankali Nene wlhy . Ta are maganar muryarta na rawa. Hakane Nene ina kan yimata iya ari na. Dan ko sadakar nan wlhy kusan don itane bana iya jinkirtawa. Amma dai a aiko mata da ruwan addu'ar ma sai ta cigaba da sha. ALLAH ya kawo iyakar komai ya kuma bama yaron nan warin gwiwar kwantar mata da hankali ta sake manta komai In sha ALLAHU Nene bana jin Yazeed. Yarone mai addini da sanin yakamata tamkar mahaifinsa. Dan sam baida halin mahaifiyarsa, baya kuma biyema al'amarinta kamar ba daga jikinta ma ya fito ba. To Amin ya rabbi sai kin shigo in ma arasa . Daga haka sukai sallama. Auta dan ALLAH kibar kukan nan haka. Wlhy yana aga mana hankali. Ki mana bayanin mike faruwa ne? Ko wani abu yace dake mara da Kanta ta shiga girgiza musu tare da share hawayenta. Sai kuma ta tashi daga kwanciyar datai a jikin Didi Shahidah ta koma ta jingina da fuskar gadonta. Didi dan ALLAH ku taimakeni, wlhy bana son auren nan bana bu atarsa dan bazan ta a yin aure ba wannan al awarine da naima kaina. Amma su Ammie da Yaya Yazeed sun kasa fahimtata. Wlhy kosun matsa nayi auren nan GANGAR JIKINA kawai zai aura, sannan bazan ta a biyayya irin ta aure ba a gareshi, bama shi ba ga kowanne a namiji. Didi miyyasa bazai fahimta bane, Maanal ta jima da mutuwa babu ita a wannan DUNIYAR ta mutane. Duk gangar jikin dake rayuwa da matacciyar zuciya bashi da wani amfanin rayuwa. Amma sun kasa fahimta, sun kasa min uziri, dan ALLAH ku ku fahimtar dasu maybe zasufi saurin yarda daku idan ni basa gane yarena. Koku fahimtar da Yaya Yazeed shi maybe ya fisu gane illar yin AJIYA A DUHU da yayi, cigaba da matsawarsa kuma zai zama onewar komai daga hasken fitilar da yake arin haskawa don lalubo abinda ma babu shi koda a cikin duhun.... Maanal Please... Didi Shahidah ta fa a tana kamota jikinta ta sake rungumewa. Itama cikin murya da lallashi ta ce, Please ki kwantar da hankalinki mana. Kin san ba wani lafiyace ta isheki ba. Ciwonki baya bu atar irin wa annan abubuwan kinfi kowa sani. Maanal iyayenmu suna son taimakon rayuwarki ne ba cuta miki ba. Sannan Yazeed babu abinda ya rasa daga zama cikakken Namiji. Yana kuma matu ar kaunarki, duk da boren mahaifiyarsa akan al'amarinku bai ta a canjawa ba. Miyyasa bazakiyi ha uri ki manta da komai ba ki amshi wannan addarar?...... Saboda addara tana tafiya ne da rayuwa Didi, ni kuma na riga na jima da Mutuwa, mi zaiyi da gawa? Mi zai yi da gangar jikin da babu zuciya? Mi zaiyi da wadda labarinta ya jima da rubutuwa da arewa? Tuni fa Maanal ta gama mutuwa, na mutu! ni tamkar hawace Didi.. Keba gawa bace Maanal, ya kamata ki fahimci bafa komai a rayuwa kake samu hundred percent ba, dole sai kayi ha uri da wani abun sannan kake mallakar wani. Please ki amshi addararki a karon na biyu, nasan zaki ji da in zama da Yaya Yazeed wlhy mutumin kirki ne, tunda kin san dai babu yanda za'ai a barki haka babu aure. Kuma Yazeed ya dace dake matu Didi ban musa miki kirkinsa ba ko nagartarsa ko cancantarsa. Duk abinda kuke hange min nasan fiye da haka gareshi, sai dai bana bu atar kowanne namiji a rayuwata gaba aya ku fahimta mana dan ALLAH .......... _Tofa, mace kuwa zai yiwu tace bata bu atar namiji a cikin rayuwarta?????. Shin jama'a mike damun Maanal ne haka????? ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama .......Hawaye ne suka cika idon Amaal, yayinda Shahidah ke arin shanye nata itama. Tausayin ar uwar tasu na ara cika musu zuciya. Dai-dai nan Ammie ta shigo, kallo aya tai musu su duka ta kauda kanta. Sai kuma tai gyaran murya. A tare duk suka kalleta, Maanal ta share hawayenta da arin kaiwa kwance, amma sai Ammie ta ri ota tana kaiwa zaune kusa da ita da fa in, Auta wai yaushe zaki bar shagwa a ne? Baki Maanal ta tura gaba da yin narai-narai da idanu zata sake sakin sabon kukan Ammien tai mata hararar wasa. Kina sakin min kuka zan zaneki ne tas a akin nan A tare suka kwashe da dariya, dan yanda Ammie tai maganar sai ya tuna musu baya. Kai Maanal ta zuba fitina a rayuwarta, ga tsoron dukan masifa. Dan duk rashin mutuncin da zata zuba da Ammie tace zata zaneta take nutsuwa. Ammie data ji da in ganin damuwar tasu ta kau sai ta cigaba da jansu da hira. Idan ka gansu abin sha'awa kamar wata babbar yayarsu can ba mahaifiyarsu ba. Dan Ammie an mata aure da arancin shekaru ne, kuma ALLAH ya bata haihuwan da wuri, shiyyasa idan baka sani ba sai ka ma auka ba itace ta haifi su Shahidah ba, dan za'afi ganin Maanal a ar farinta kamar. Kamar wasa suka sha hira sosai sai da aka kira Magrib Ammie ta fita. Babu wanda ya sake tada batun auren Maanal in har dare. Sun idar da salla Shahidah da Amaal suka shiga kitchen, yayinda Maanal ta nufi akin Ammie dan tana son tambayarta gobe in sha ALLAHU da wuri zata fita gyaran jiki. Ta samu Ammie akan abin salla tana waya da mijinta, dan haka ta haye gadonta ta kwanta tana saurarenta. Sun jima kafin suyi sallama ta juyo ga Autar tata tana tambayar, Mi kuma ya faru ar shagwa ar Ammie? Murmushi Maanal in tayi, cikin yanayinta na miskilaye da shagwa a ta ce, Ammie ina son naje gyaran jiki gobe in ALLAH ya kaimu, ban sani ba ko kina da ku i. Jibafa yanda jikina duk ya bushe ga kaina sai ayi yake mun Uhm ko bani da ku i auta ai dole na nemosu, ke idan fitinar gyaran jikin nan naki ya tashi ai duk fatarata ba ya raga min Sosai Maanal takema zancen Ammien murmushi. Yayinda Ammien ke kallonta cike da jin da i, idan taganta cikin farin ciki haka da i take ji, sai ta dinga ganin asalin Maanal inta ta baya sarkin rikici da kwaramniya, amma yanzu duk ta zama sanyi-sanyi ga miskilanci, sam bata son sabon yanayin nata na wannan shekarun, sai dai babu yanda zatai tana mata addu'a. Katse mata murmushin tai da fa in, Ke duba wayar nan taki tun azun take haske alamar kira . Amsa Maanal tayi da fa in, Inaga Zezaa ce ko Anees.... sai kuma ta kasa arasawa saboda ganin number mai kiran, dan ko saving batai ba, amma nacinsa yasa tuni ta haddace lambarsa a kanta. Fuska ta an tsuke, har zata maida wayar ta ajiye sai kuma ta dakata, dan tasan shegen nacinsa ba lallai ya barta ba idan bata aga in ba. Inda Ammie take ta an kalla, ganin hankalinta baya kanta ta aga tana mai kai wayar kunnenta. Can asan ma oshi cikin muryar nan tata mai zurfi da rashin sakewa tai sallama. Tana jiyo sautin ajiyar zuciyar RK da ga can, dan haka ta ta e baki kawai. Baby duk kin saka hankalina tashi. Ai da nace idan nayi kira dubu baki amsa ba komai dare zan sake kamo hanyar Kaduna ne Hummm kawai tace a ta aice tana an satar kallon Ammie. Ganin ita take kallo yanzu sai ta an sake ata fuska. Yayinda kunenta ke sauraren RK dake magana cikin kulawa da tambayarta ta samu gida lafiya. Cikin sake maida muryarta asa sosai ta ce, Alhamdullah ina yin abune an jimm yay