← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 104

Sashe 33

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya arrahaman Auta! Baka da lafiya amma kazo nan ka kwanta? Are you mad da baka san muhimmancin lafiyarka bane? Maimakon amsa masa sai AA in ya maida idanun nasa kawai ya sake lumshewa. Tsaki mutumin yaja tare da mi ewa ya tada AA in shima. Oya get up and go home? Bai masa musu ba ya mi in, haka ya kamashi suka fito yana bama AS da hankalinsa ya tashi da ganin halin da boss insa yake ciki umarnin tattaro abubuwan AA in. Cikin sauri ya amsa shi kuma ya wuce da shi...... _____________ A hankali yake juya steering kamar baya so. Yayinda gaba ayan hankalinsa ke akan al'amarin Maanal. Yama rasa yaya zai fassara lamarin, musamman a yanzu daya koma Maawad yaji komai daya faru. Shin murnar samun aikin ce ta sakata kukan? Ko kuwa mike faruwa?. Rashin mai bashi amsa ya sashi aukar hanyar gidan Shahidah, dan gaskiya yana bu atar ganin Maanal in. Ya an yi nisa da tafiya kira ya shigo masa. Kamar bazai auka ba sai kuma dai ya auka saboda ganin abokin aikinsa ne na asibiti. Neman gaggawa ake masa zuwa asibiti yanzun nan, dole yay reverse zuwa asibitin dan yanda yaji Doctor in a rikice yasan akwai babbar matsala. Kafin ya isa kiran wasu doctors biyu an uwansa ya sake shigo masa. Dole ya ara gudu cikin anin lokaci sai gashi ya iso..... _________ angaren Maanal kuka taci sosai na tashin hankali. Dan har yamma ta kulle kanta a aki ta i ta fito. Yara da suka dawo makaranta sunata buga mata bata kulasu ba. A haka shima baban nasu ya dawo ya tarar da al'amarin. Linda ce ta sanar masa iya abinda ta sani na shigowar Maanal in da gudu tana kuka ta wuce aki ta kulle kanta... Hankalinsa ne ya tashi shima. Ya shiga knocking ofar yana kiran sunanta amma shiru. Sai ya fara tunanin kodai batama rayene? Gata tare da ciwo mai ha ari. Wayar Shahidah ya kira yace ta dawo gida yanzun nan. Hankali tashe ta shiga tambayarsa lafiya? Dan ita bata tashi a nata aikin ba. Amma sai yace ba komai tazo dai kawai. Daga haka ya yanke kiran ya fita neman maigadi dan yazo su gwada alla ofar. Babu jimawa suka dawo, zuwa lokacin yaran nata kuka suna sake buga ofar. Sunta arin buge ofar amma bata allun ba, dole maigadi ya ce, Yalla ai sai dai fa a nemo wanda yasan aikin karma ayi arna. Bara muga na kira wani yaro dana sani Kai kawai Uncle Sadeeq in ya iya aga masa. Dai-dai nan Shahidah ke shigowa a ru e. Cikin tashin hankali take tambayarsa abinda ya faru. Bayani ya mata kamar yanda Linda ta masa. A take jikin Shahidah ya kama rawa. Itama ofar ta fara bugawa muryarta na rawa tana kiran sunan Maanal in amma shiru. Wani tunani ne yazo mata, ta fita cikin sassarfa zuwa can baya inda windows akin suke. Binta shima mijin nata yay. Kwance suka hango Maanal shar an a gado babu alamar rai a tare da ita. Ai Shahidah bama tasan tayi wani irin yin baya ba tana neman fa uwa sai da mijinta ya tarota. Cikin rawar baki data murya ta ce, Honey ta rasu ko? Da alama Maanal bata numfashi In sha ALLAHU bata rasu ba Honey cool down. Zata iya yiwuwa suma tayi ko barci take Barci! Ina badai barci ba Honey..... Isowar su maigadi ya hanashi bata amsa. Kamata yay suka koma cikin gidan. Cikin abinda bai wuce mintuna goma ba aka alle ofar akin. Daga Shahidah har mijinta da yaran a guje suka afka ciki. Lokaci aya ita da yaran suka zagaye Maanal in. Koda ta cacumota sai tai mata wani jagab alamar babu rai tare da ita. Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un . Ta shiga ambata jikinta na rawa. Yayinda yaran suka fara ihun kuka suna kiran Maanal in. Shi kam mijinta arin neman number RK yake yi, sai dai sam ta i shiga. Dole ya koma neman Dr Ranjet. Cikin Sa'a kuwa sai ita ta shiga. Bayani ya masa a ta aice, hankali tashe Dr Ranjet yace gashi nan zuwa gidan RK ya shiga theater in gaggawa ne tun azun shiyyasa bazai samesa ba. Alhamdullah Dr Ranjet ya iso akan lokaci tare da wata abokiyar aikinsa. Dandanan ya saka kowa ya fito suka kasance su biyu kawai a akin. Taimakon gaggawa suka shiga bama Maanal in, sunfi awa aya kafin cikin amincin UBANGIJI ta farfa o. Dama ya tabbatar musu su kwantar da hankalinsu bugun zuciyarta ne yay asa sosai shiyyasa numfashinta ya dakata ma amma tana da rai. Basu bari kowa ya shigo ba sai da suka gama dai-daita komai suka saka mata ruwa da allurai sannan. Bayanin da Dr Ranjet yamusu ya saka su dinga sauke ajiyar zuciya a tare. Shahidah ta dinga share hawaye. Su duka suka shiga tare da yaran da mijin nata, ganin Maanal in na barcinta hankali kwance ya sake saka musu nutsuwa. Bayan fitowarsu ne Dr Ranjet ke sanar musu dolene su kula sosai da shan maganin Maanal in, dan yanzu ma yana tunanin sakacin hakanne ya kawo wannan matsalar, duk da ya fahimci akwai damuwa tattare da ita bai fa a musu ba dai. Hakan kuwa in ne kamar yanda yay hasashe, dan yasa an kawo masa magungunan ya duba ashe kona safe bata sha ba ta fita. Ya sake tabbatar musu da kula da shan maganin nata da shigarta kowacce matsalar damuwa komai antarta sannan suka wuce. Dole yau Shahidah tare ta kwana da Maanal. Alhamdullah ta tashi cikin aminci kuma. Dukkan wata kulawa Shahidah ce ta bata a wannan safiyar, harda yara kowa tattalinta yake yi, hatta da abinci tara suka bata a baki, hakan ya sakasu makarar fita dan sai da ta sake komawa barci sannan. Bayan ta farka Linda tai arin taimaka mata tai wanka taci abinci tare da sanar mata zuwan RK gidan har sau biyu, amma sai Maanal in ta i cewa komai tana zaune kawai tana hawaye. Ana haka RK ya sake dawowa. Babu lallashin da Linda batai mata ba akan taje su gaisa ko shi ya shigo amma ta i, tanata kukanta kawai. Hankalinta sai ya sake tashi tai kiran Shahidah dake a wajen aiki ta sanar mata. Cikin anin lokaci kuwa sai gata ta dawo gidan... Haba Maanal wai mike faruwa ne duk kinbi kin aga mana hankali. Jibafa office na baro saboda kiran da Linda taimin duk da tarin ayyukan dake a gabana. Amma inata magana kinyi shiru sai kuka kikeyi. Idan jikin naki ne kuma muje asibiti. Ko na kira Ammie ne dai? Da sauri Maanal ta shiga girgiza mata kanta tana sharce hawayen da suka gagara tsaya mata. Didi kar ki kirata dan ALLAH. Ba wani abu baneba fa Haba Maanal ya zakice bawani abu bane gaki kinata faman kuka. Idan baki son na kira Ammien to ki fa a min mike faruwa ne? Wani abun Rafeeq in ya miki jiyan da kuka fita? Ko aikin ne basu aukeki ba? A'a Didi babu aya daga ciki, ina son yai zan koma KD Okay mune mukai miki wani abu kenan? Kai Didi ni mi zaku min. ALLAH ki kwantar da hankalinki babu komai Batun kwantar da hankali kam bazai kwantu ba Maanal, yanzu fa kike cewa zaki tafi KD. Amma dai bara na kira Ammien ni kam, ila ki sanar mata ko Nene. Ga Rafeeq can Linda tace yayi mayawa takai hu u tunda safe amma kin i fita, kin i cin abinci, kin i wanka Maanal why? Gara nai kiratan dai zai fi Caraf ta ri e mata hannun tana girgiza kanta. Yayinda idanunta suka cika da walla tab. Please Didi karki kirata zan gaya miki . Kai Shahidah ta jinjina tare da sauke numfashi sai kuma ta sakar mata wayar da fa in, To ina saurarenki, mike faruwa? . Sai da Maanal taja kusan mintuna biyu kafin da yar ta iya furta, Didi sun aukeni aikin amma bazanyi ba Baza kiyi ba kamar ya? To saboda mi?. A wannan lokaci da aiki ke wahala Maanal. Kin samu cikin sau i haka amma kice baza kiyi ba. Ko auren Yazeed in kike so to? Ko kuma dan kinji jiya ankai ku insa gidan su Nazeefa ne har kika nema tadana kanki ciwo? Didi mizai sa na damu da auren Yaya Yazeed tunda ba'a kaina zata zauna ba. To mike faruwa? Wajen aikin ne ya miki alamu na marasa a'a ko me? A'a Didi kawai dai Miye kawai dai. Maanal ki fito kimin bayani mana yanda zan fahimta na kuma gamsu Rasa yanda zataima Shahidah in bayani tayi, ta fito fili ta sanar mata abinda idanunta suka gani a jiyan ko kuwa ta shanye al'amarin a cikinta kawai ta dage akan aikinne bazatayi ba. To amma tasan nacin RK, shima bazai barta ba ai. Sannan ita kanta Didi ba barinta zatai ta huta ba har sai ta san gaskiyar al'amarin. Sanin gaskiyar kuma na nufin abinda zata oye a yanzu dan sai sun san komai. (Ya arrahaman) ita ina ya kamata ta kama ne?..... Maanal!! Shahidah ta kirata tana mai girgizata. Firgigit ta dawo hayyacinta kamar wadda aka tada daga barci, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tare da kai hannunta saman goshi tana murzawa a hankali. ALLAH Maanal tambaya ta arshe zan miki daga nan zan kira Ammie ne kawai tunda ni baki son nasan damuwarki Jin yanda Shahidah tai maganar a hasale tana arin mi ewa yasa Maanal saurin kamo hannunta ta dawo da ita. Idanunta cike da walla ta ce, Didi ba oye miki nake ba wlhy, kema kin sani bana ta oye muku komai a rayuwata. Kawai dai na fasa yin aikin ne saboda companyn na Bes... sai kuma ta canja ta ce, AA Darma_* ne? Cikin matu ar razani Shahidah ta mi e zumbur hannunta dafe da irji ta ce, What!! Kina nufin *_Ajwaad!!_* Maanal! Shi Didi, shi! Shi! in dai. Maanal ta fa a wasu hawaye masu zafi na sake gangaro mata. Jagwab Shahidah ta koma ta zauna tana mai dafe kanta da duka hannaye biyu, ita kanta jikinta tsuma yake, sai kuma ta ago tare da jawo Maanal in jikinta ta rungume dan kuka take mai ban
Chapter 33 · 0% Book details