← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 104

Sashe 68

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kaga ba magana zai maka ba. Zuwa anjima in sha ALLAHU zan kiraka na shigo ba duba Auta ta itama To ALLAH ya kaimu muna zuba idon ganinki, idan kuma an shagwa arki bai bari ba mun yafe zan kira a waya sai ku gaisa. Dan itama ina yautata zaton zuwa anjima za'a sallameta, yau tunda safe take mitar ita a sallametan Dariya kawai Oum tayi tana mai girgiza kai, tasan Maanal da iriniyarta, damma taga yanzu kura tayi lafiya kamar ba Maanal in ba..... ______________ Jikin Maanal ma Alhamdullah, dan tama hana Shahidah sanarma su Ammie. Dama kuma Shahidahn ma batai niyyar sanarma Ammie in ba kamar yanda mijinta ya fargar da ita cewar tunda da sauki karsu tayar musu da hankali. Abinci Maanal in keci RK ya shigo, sai da ya gaisa da su Shahidah kafin ya maida hankalinsa a kanta. Cikin tsokana ya ce, Madam ba tayi . Ai baima gama rufe baki ba ta mi a masa plate in. Mi mijin Shahidah zasuyi ba dariya ba. Uncle Sadeeq ya ce, Doctor kai baka san dama neman kai take da abincin ba, an turketane tana ci dan dole Fuskar RK da murmushi ya ce, Ai naga alama Babban yaya. Irin wannan bani da sauri haka. Ni dai dan ALLAH kici abinci ki ara kumari Hararar RK in tayi, sai kuma ta tura baki gaba cike da shagwa a. Zama Shahidah tai kusa da ita cikin lallashi ta ce, Kinga yalesu Auta kinji, bari ma na baki da kaina . Haka ta amsa ta cigaba da bata cike da kulawa da so. Sai RK ya samu kansa da shagala a kallonsu. Shi ka ai yasan yanda yake jim aunar yarinyar nan a ransa. Komai tayi birgesa yake. Yasan hakan daga ALLAH ne. Dan yana jin feeling akanta irin wanda zai rantse bai ga a ji ga sauran amata ba. Kodan bai ta a yin budurwa bane oho. Sam shi ada matsoracin mata ne, babu ruwansa da harkarsu, badan bai cika namiji bane, kawai dai karatunsa na likitanci daya wallafa rai da aikin nan sun kwashe mafi yawan lokacinsa na rayuwa. Idan ka cire ibada da yake matu ar bata hakkinta. Shifa ko irin ar soyayyar uruciyar nan baiyi ba. Kuma a turai aka haifesa anan ya girma yay dukkanin karatittukansa. Gaba aya bai wuce shekara hu u da dawowa Nigeria gaba aya ba. Amma ALLAH bai ora masa damuwa da mata ba. Shiyyasa shi da kansa yake sake yarda da son Maanal yake bana wasa ba. Hakama an uwansa kowa murna yake da batun Maanal dan sun tabbatar da gaske son nata yake tunda shidai ba'a taba kamashi da case na mace ba. Sosai Maanal ta matsa ita sai an sallameta ta warke. Amma Dr Ranjet ya dinga lalla ata akan tayi ha uri zuwa gobe. Dole badan taso ba ta ha uran... ______________ Kusan arfe uku na yamma Abdul da amaryarsa Yaseerah sai Huznah suka iso katafaren family house in na Ambassador Aliyu Darma. Dan a gidan su Yaseerah Huznah ta kwana. Daga Mawaad Company can ta wuce ranta a ace tana hawayen abinda AA ya mata. Shine Yaseerah taita lallashinta da tabbatar mata a yau zasuzo Darma's house. Hakan kuwa akai, tun a daren take lalla a Abdull akan suje har ya amice. Sai kuma gasu sun iso yanzu. Sun sami tarba daga Mamy, yawar mace walisa data gama tafiya da zuciyar Huznah. Kai tun kafin ma Mamyn Darma's house ya gama tafiya da Huznah. Ta gama sallamawa da jinjina ku i irin na gidan su AA in. Ta kuma yarda ku in ma hawa-hawane. Tasan mahaifinta nada ku i, tunda suka tashi suke jin ana sakashi a jerin masu ku in jihar Kaduna, kai bama Kaduna kawai ba a dattawan arewa masu ku i za'a iya sako mahaifinsu. Sai dai kuma Baba ma fa da babansa. Ta shaida hakan a yau kuma ta aminta. Yanda take ta faman sinne kai da kaffa-kaffa da komai sai ya baka mamaki, ko gaishe da Mamy sai da ta du a har asa. Sai Mamyn ce dake binta da kallo ta kamata ta tadata ta zaunar a kujera. Still dai Huznah ta kasa kallonta. Ita ma dai Yaseerah bata da wata sakewa, dan dangin mijin nata alilan ke sonta, duk da dai ita Mamyn na sonta. Kawai dai dan Abdull in ya dage sai ita ne yasa suka yalesa. Hakan yasa su biyun duk suka nutsu, sai Mamy da Abdull ne ke hira. A haka Saheeba ta shigo suka gaisa tare da saka masu aikinta jere abincin da Mamyn tace tayo a sashenta na tarbar ba in. Saheeba dai ta danne sun gaisa da su Yaseerah, sai dai hankalinta nakan duk motsin Huznah ne. Bisa umarnin Mamy sukaje d/table, anan in ma dai Huznah bata sake ba ita adole mai kunya. Ita dai Mamy sai kallonta take tana murmushi. Dan haka kawai kuma sai taji son yarinyar a ranta saboda kunyarta da nutsuwa gefe ga ta yawa. Dan duk yawun Nuratu da da take kallo dai-dai da AA sai taga ai Huznah ta takata ta shanye. Dama dai a an kwanakin nan wasu abubuwa na Nuratu sunsa ta fara shakkar ha a aurenta da AA in, amma bata fito ta fa ama kowa ba. To tana ganin yarinyar nan itace zata zama raba gardama. Dan kodai ya aurenta ita ka ai kota sakashi ya ha a da Nuratun su biyu a masa auren gata auren huce takaice auren da tasan zai ba anta ran Oum fiye da auren su Fawzan. Bayan sun kammala cin abincin ta umarcesu da suzo su duba AA. Abdull ne ya tambayeta Baida lafiya ne Uncle AA in Grandma? (dan haka yake kiranta kasancewarta anwar kakarsa uwa aya uba aya). Amsa ta bashi da Eh son, yau ko aiki ma bai fita ba yana kwance Gaba aya ji Huznah tayi hankalinta ya tashi, dan har fuskarta ta nuna hakan aro- aro, amma dai ta daure batai magana ba. Mamy dai na lure da ita. Hakama Saheeba dake jin kamar ta sha o Huznah in. Sai faman tsine mata take a zuciya. Sashen Oum suka fara zuwa, Oum ta tarbesu da kulawa kamar yanda ta saba ma an uwan Mamyn, dan haka cikin girmamawa Abdull ya gaisheta, hakama Yaseerah da Huznah data kusa zubewa a tsaye da mamaki tana satar kallon Oum. Tabbas bata manceta ba, itace ta gani a gidan Shahidah tare da namiji mai kama da AA inta. Rashin sanin ala arsu da su Maanal in kuma yasa har yanzu bata sanarma mahaifiyarta ba, gefe kuma ta an shiga ru ani, shin tsakanin Mamy in da matar wacece mahaifiyar AA in? A dai kamanni yafi tsananin kama da Oum, shin yaya take ne?. Da yar ta iya dannewa dai suka baro sashen bayan Oum ta cika su da abin arzi i, sai dai fa da alama ita Oum bata gane Huznah ba. Koda yake a gidan Shahidah da suka ha u ita bawani ta maida hankali a kanta bane lokacin. Daga nan sashen AA suka nufa kamar yanda Mamy ta sanarma Oum cewar zata kaisu su dubashi. Wani irin lumshe idanu Huznah tai lokacin da suka shigo main falo in sashen da wani irin amshi mai da i ke tashi. Suna isowa falo na biyu taji zuciyarta na wani kalar tsaitsinkewa saboda ha uwarsa. Falo kamar bana tuzuru mara mata ba. Anan Abdul ya dogare, fuskarsa da murmushi ya ce, Grandma bari mu dakata anan a masa magana idan zai iya sakkowa mu gaisa. In ba hakaba bara na haura ni ka ai sai na dubashi kin san Uncle baya son wargi bakamar Uncle Fawzan ba Murmushi Mamy tayi, dan itama dai tasan maganar Abdull in gaskiya ne. Dan in har ta hau da su Yaseerah sai yaji haushi. Su Saheeba ma dake matsayin matan yayyansa kuma an uwansa na ut sosai yake tujara idan suka shiga masa koda falon sama ne balle. Yanzu haka ko azun tana jin yanama Fadeel mitan shi matansu su daina shigo masa har bedroom. Mamy ce ta haura saman da kanta. Dai-dai AA daya farka daga barcin da Doctor ya sakashi dole ya fito wanka. Knocking ofar da akai ne ya sashi yamutsa fuska cikin yanayin mara lafiya, muryar shi asa- asa da kamar baya son bu e baki ya furta, Ina zuwa . Daga haka ya ajiye towel in hannunsa da yake goge sumarsa da ruwa ya ji a saboda ciwon da kansa ke masa har yanzu ka an-ka an ya sakarma kansa ruwan. Boxer ya saka tare da cire bathrobe in ya saka jallabiya sannan ya nufi ofar dan duk zatonsa Oum ce. A hankali ya bu ofar, cikin an shagwa a ya furta, Oum sai yanzu, ni nayi fush....... Kasa arasawa yay saboda yin tozali da Mamy ba Oum ba. Ta koyi kicin-kicin da fuska tana masa wani irin kallo, kansa ya du asa yana mai ha iye busashen yawu ya furta, Am sorry, nazata Oum ce Humm kawai ta furta batare data kula zancensa ba ta juya tana fa in, Kasameni a asa ba i zasu gaisheka Kallo ya bita da shi, harta fara taka stairs case in. Ka an ya lumshe idanunsa ya bu e, sai kuma ya an furzar da iska ya koma cikin akin.......... ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ ........Fin mintuna goma bayan sakkowar Mamy sannan ya sakko. Duk da sanye yake da slippers masu taushi hakan bai hana bayyanar tahowarsa ba. Ga wani mayataccen amshin turarensa mai ratsa zuciya na rige-rigen shiga hancinansu tun kan su fara ganinsa. tuni zuciyar Huznah ta fara gudu a irjinta, yayinda
Chapter 68 · 0% Book details