← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 104

Sashe 74

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yake shima sai ta an kauda idanun ta. Yaya Rafeeq ka shirya yin aure yanzu? Mugun fa uwa gabansa yay dan abin yazo masa a bazatar da baiyi zaton ji daga gareta haka cikin sau i ba, duk da bai san ma'anar yimasa tambayar ba. Cikin nutsuwar ban mamaki ya ce, Miyasa kika mun wannan tambayar Maanal? asa ta ara yi da kanta, tana mai kokawar arfafa kan nata da danne dukan abinda ke neman rinjayar shawarar data gama yanke ma kanta tun a daren jiya. Ajiyar zuciya taja mai nauyi kafin ta saki murmushi mai ciwo. Ka amsa min kawai, ka shirya yin aure yanzu? Ban san miyyasa kika min wannan tambayar ba Maanal, amma tabbas na shirya yin aure, dan na isa yinsa, da ban shirya yin aure ba ALLAH bazan tunkareki da sunan soyayya ba. Saboda al awari naima kaina bazan ta atama kowacce yarinya lokacinta ba in har ba aurenta zanyi ba. Na da e ina addu'ar a duk sanda zan so wata iya mace ya kasance aurenta nake so zanyi Sosai ta kafesa da ido, sai kuma ta wani lumshesu da sake bu esu a kansa. Cikin son taushe muryarta dake neman fara yin rawa ta ce, Ina son zuwa Kaduna a weekend in nan. Kuma ina son na an huta a can.... sai kuma ta an yi shiru. Cikin za uwa RK yace, Uhumm ina jinki Murmushi ta sake saki mai ciwo idanunta dai na kallon asa. Na baka dama kaje ku gana da Daddy akan batun auren mu Ai ba zuciyar RK ba, hatta akin ma ji yay yana masa girgiza. Yayinda wasu irin hawaye masu azabar zafi suka silalo da gudun tsiya a kumatun Maanal. arar tarwatsewar abu da basu san ko minene ba ta ratsa kunnunwansu. A tare duk suka dubi ofar, dan tanan ne abun yay ara. Plates in abinci ne suka watse a asa. Dubansu suka maida ga wanda alama ta nuna daga hannunsa plates in suka su uto........... ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ ......... Subahanalillahi Naufal ya akai haka? . Oum ta fa a tana kallon Naufal first born in babban Yaya kenan da a safiyar yau suka dawo daga Kano shi da sauran annensa biyu ammata. Kafin Naufal da yay wal da idanu alamar zai yi kuka ya bata amsa ta maida dubanta ga AA da yay tsaye a ofar duk ya tare ko'ina babu ma ta yanda zata iya shigowa. Sake le o fuskarsa tayi daga bayan san da take sai kuma ta kalla direction in daya zubama idanun. Kallon cikin ido suka zubama juna shi da Maanal.. sai dai kafin ta iya yin wani yun uri RK da tuni ya baro inda yake yazo ya kama Naufal ya aga gudun kar ya taka fasashshen plate in daya tarwatse shi ka ai ya katseta da fa in, Alhamdullahi ai babu ma abinda ya zube kamar plates in ne suka su uto kawai daga basket in, inaga tuntu e yayi ne Ai kasan Naufal da wautan tsiya. Tun da naga ya figo basket in da gudu nasan komai zai iya faruwa. Baka dai ji ciwo ba ko? . Tai maganar tana kallon Naufal in dai. Kansa ya aga mata cike da shagwa a ya ce, Oum Uncle ne fa ya kusa sawa mu fa Yanda yay maganar yana kallon AA yasa duk suka kallesa suma. Ta a AA Oum tayi, dan gani tai ma kamar baya motsi, sai dai kuma tana ta a shin ya juyo ya kalleta, hannunsa ta kama cikin nata ta rumtse da yau, sai kuma ta juya ga Naufal da RK kema dariya da fa in, Ko kuma kai ka kusa sakawa ku fa in ba. Aunty ai banyi zaton yanzu zaku ma taho ba. Rafeeq ai bana wasa da Baby na sam. Balle kace yau za'a sallameta shiyyasa nace in sha ALLAHU da wuri zanzo. Sai kuma Auta da nake son yaga likita yau shima Karo na farko RK ya dubi AA sosai. Ganin yanda idanunsa sukai masifar ka ewa ya ce, Ya Salam badai kan nasa bane har yanzu? Shine kuwa wlhy ya i sauka, jiya haka ya kwana a wahale . Ta bashi amsa tana jan hannun AA in zuwa gaban gadon da Maanal take. A kwance take yanzu ta juyama ofa baya, hakan yasa Oum zama a bakin gadon kusa da ita. Shi kuma yay tsaya kawai daga gefen Oum yana kallon ofa dan ya i sake kallon Maanal. Kujera RK ya tura masa cike da kulawa ya ce, Zauna anan bara na duba Doctor Rasheed in muga. Ai da kun sanar min da gida yazo ya samesan Yayi ari ne ai Rafeeq, kwana biyun nan yanata zaryar zuwa gidan, kuma dama yace idan bai sauka ba yau asibiti ya kamata yazo ya duba shi da yau shiyyasa Jajantawa RK in ya sake yi kafin ya juya ya fita yana jaddadawa AA ya zauna. Sai dai ko kallonsa ya iyi balle ya zauna in. Yana daga tsayensa duk da hajijiyar da yake ji na jujjuya masa kai. Oum kuwa data ri o hannun Maanal a hankali ta shiga kiran sunanta. Hakan yasa cikin dauriya da jarumta Maanal da tuni ta goge hawayenta tas ta juyo in. Suna ha a ido da Oum ta sakar mata murmushi, sai kuma ta tashi zaune ta shige jikinta cike da shagwa a ta ce, Oum ni nayi fushi sai yanzu Oh oh my baby kada kiyi fushi kinji, ayima Oum afuwa yaya jikin naki? Naji sau i Oum. Yaya Rafeeq ma yace zasu sallameni yau To Alhamdullah ALLAH ya ara afuwa. Tun jiya naso zuwa shima sai Auta ya kwanta shiyyasa Hy Aunty Naufal ya fa a yana agama Maanal hannu fuskarsa da murmushi. Murmushin itama Maanal in tai masa. Sai kuma ta aga masa hannun itama ta ce, Hy Handsome Farin ciki ne ya kama Naufal jin an kirasa Handsome, dama Uncle AA ne kawai ke kiransa da sunan. Gaban gadon ya araso sosai. Ya ce, Nagode Aunty da kika kirani Handsome. Kun zama biyu kenan ke da Uncle. yay mata nuni da AA. Batare data kalli AA in ba taima Naufal murmushi kawai. Gaisheta yaron yay da tambayarta yaya jiki, ta amsa masa da kulawa tana zaunar da shi kusa da ita. Sai kuma ta kalla Oum tana fa in, Yana kama da babban Yaya sosai Dariya Oum tayi a karo na farko, idonta akan Naufal ta ce, Kodai Auta. Dan komai na Naufal Auta ne sak, duk da dai dama suna kama da Fadeel ne shima in, amma Fadeel ai fari ne, shiko Naufal irin fatanku gareshi ke da Auta Maimakon Maanal ta amsa zancen sai ta basar ta hanyar shagwa e fuska ta ce, Oum mi kika dafo min? Dai-dai Oum zata bata amsa RK ya shigo. Idonsa a kansu sai kuma ya kalla AA, da kulawa ya arasa garesa yana fa in, Wai baka zauna ba. Ko duk ulafucin Oum in kaka ne kazo ka tsaya mata a kai kamar zaka koma ciki kai da ayar Autar tata. Common malam zauna kada ka fa . Yanda baiyi magana ba tunda ya shigo yanzun ma bai tanka ba, sai dai ya zauna in dan shima yasan in ba hakan yay ba tabbas gab yaje da zubewa a asa, sam kuma baya son cigaba da tada hankalin Oum, dan kwana biyun nan da baida lafiyar nan har rama tayi, ga shi itama tana fama da kanta..... ____________ A Kaduna kam shirin kai lefe ake gidan su amarya. Shi ango ma baya nan yana Lagos kwana takwas kenan. Kaya ne na garari aka shirya na kuma fariyya. Jiya yini guda masu shiryasu na aikin nan. Akwatina set ashirin daa hu u cif, kaloli daban-daban. Kuma kowane set zaka samu kusan akwati biyar ko uku harda masu goma sha biyu. Ga galleliyar mota new model a 2023 sabuwa dal a ledarta. Hajiya Basariyya dai tana nane dasu a gabanta ake komai duk da zuciyarta a untace take, amma yafi yarda data danne ayi komai akan idonta, Ammie ko yanda ba'a gayyaceta ba bata saka kanta a sabgar ba daga ita har Sakina da har yanzu take a gidan. A yau in ma sai suka iri zuwa gyaran jiki abinsu. Duk bidirin shirin kayan da akai basa nan. Aiko Hajiya Yaya da anta suka samu na zaginsu wai Ammie tana hassada ne saboda ba iyarta bace ba. Koda suka dawo gidan haka suka cigaba da habaice-habaicen su Ammie tayi kamar ma bata jisu ba... Washe gari tun sassafe gidan ya fara tara dangin Hajiya Yaya. Sai wasu a dangin Daddy dake asawa da Hajiya Yayan. Yanda gidan ya cika saika auka bikin ne ma ya fara. Har lokacin kuma babu wanda ya zo ya cema Ammie tazo ga lefe kota shirya zuwa kai lefe, ita kuma tayi biris da kowa bata saka kanta ba. Bayan sallar azhar suka cika motoci goma cif sai ta amarya dake tsakkiya da toyota hilux da aka zuba kayan lefen a ciki. Haka suka tafi a jere gwanin sha'awa, duk inda suka gitta sai an tanka kuwa. Dama haka suke so, gari ya auka ko'ina ayi zancen wannan aure. To ALLAH ya cika burinsu dan kuwa an fara, sakamakon annen Yazeed kaf da wasu a dangi tun jiya sun gama watsa wannan lefe a kafafen yanar gizo tako ina.. A can gidan Aunty Sabuwa ma gida cike yake tan am da awayenta an duniya da dangin mijinta. Anyi abinci kala-kala domin tarbar ba i duk da kuwa aurene na dangin juna. Cikin abinda baifi mintuna ashirin ba anguwar ta gama rikicewa, dan kuwa ki a
Chapter 74 · 0% Book details