Sashe 9
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba ya sashi an kallonta. Kanta tai saurin kaudawa tana mai arin ha iye acin daya mamayeta. Shima sai ya auke kansa bai sake magana ba. Babu jimawa suka iso gaban gidan da take zuwa gyaran jikin, wanda yasani ne tuni saboda yanda take ma'abociyar zuwa gidan kusan duk arshen wata. Jikinta har tsuma yake nason ta fita a motar, dan bata so ya sake mata wata magana amma sai taji motar a ame alamar ya saka luck. Dole ta an dakata tana rumtse idanunta. Sai kuma ta juyo ta dubesa, ganin shima ita yake kallo ta maida kan ta du ar. Murmushin ya sake saki ka an da auke idanunsa a kanta cikin son basar da yanayin ke bashi a jikinsa. Ki tayani murna? Batare data sake kallonsa ba ciki-ciki ta ce, Tami? Akan albishir in da akai min yanzu a waya. Mutumin nan kusan shekara guda kenan muna son ha a Bussines dashi amma ko ganinsa ya gagara a gareni. Amma yau kinji har zan samu ganinsa, nasan Daddy zaiji da i akan hakan shima matu Karo na farko tai an murmushi. Sai kuma ta ce, ALLAH ya tabbatar da alkairi a ha uwar taku to Amin ya rabbi dear. Ammafa nasha wahala sosai. Mutumin ya riga yayi nisa ne matu a saboda yanda yake hu a da manyan mutane na wajen asar nan dama cikin gida Nigeria. Nasan dai bazaki rasa jin Mawaad ba Ina dai ganin sunan Companyn a jikin buhunan shinkafa, ban sani ba ko sune ko kuma da banbanci Yes sune. Dan yana harkar noma yanzu matu a a asar nan. Kuma Kinga wannan harkar ma bai wani jima da farata ba. Amma da yake ALLAH ALLAH ne cikin anin lokaci nan ma yayi zarra. ALLAH sarki . Kawai Maanal tace dan bataga ma'anar bata wannan labari ba ita kam da dam bata da ala a da shi. Cikin marairaicewa ta ce, Yaya bara naje kada na makara Ammie tace zamu rakata anguwa Amsa mata yay da Okay bari na barki ki wuce. Inata baki labarin abinda bai shafeki ba, haka nake bu atar rayuwata Manaal, wato iyalinna su dinga sanin komaina dan su kasance masu min addu'a. Dan haka sai ki shirya, dan zaki dinga raba farinciki da mijinki hakama akasinsa idan ya gitta ya are maganar yana mi a mata atm card insa. Kanta ta girgiza masa da sauri. A'a yaya ga Ammie ta bani nata zanyi amfani da shi. Hararta ya an yi da zare atm in Ammien ya ajiye mata nasa a cinyarta. Kiyi amfani da na mijinki, dan nike da hakkin hakan ba Ammie ba. Idan kin kammala ki kirani dan ba nisa zanyi ba Yanda ya tsatstsareta da ido yasa ta kasa magana. Dole ta bu e motar ta fita dan shi in baiso wasa ba dole kaji shakkarsa. Bai bar wajen ba har saida yaga ta shige. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali da jingina jikinsa da kujera yana mai lumshe idanunsa. Ya jima a hakan dan yaci kusan mintuna biyar kafin ya tada motar yabar wajen yana mai danne abinda ke tsikarar zuciyarsa game da ita..... Yanda Maanal ta samu tarba a ciki zai tabbatar maka akwai sha uwa da sanayya sosai tsakaninta da mai gyaran. Dan duk miskilancintan nan sai murmushi take da an maidama mai gyaran hiranta dan tana mata tambaya ne akan Jos. Basu wani jima ba aka fara gyaran saboda tun jiya ta sanar mata. Kafin tazo ta ha a komai. Gyara sosai jikinta ya sha. Ga turarruka kamar wata amarya. Hatta kanta da afafunta zuwa farce an musu al. Haka Maanal take akwai son gyara jiki, ar gayuce sosai da son kwalliya, sai dai yanzu yanayi yasata arar da kwalliyar gefe gyaran jikinta da tsafta ne dai tana nan da abinta akoda yaushe. Sun gama a urarren lokaci, dan har Ammie na kiranta a waya ma. A gurguje ta bata ta cire ku in aikinta tare da amso kayan amshin data ha a mata suka fito zata mata rakkiya. Turus taja ta tsaya da ganin motar Yaya Yazeed a ofar gidan, kafin ma ta samu abin fa a ya bu e mata gefensa alamar ta shigo. Ganin fuskarsa babu wasa sam yasa batai magana ba ta shiga kawai. Sallama sukai da mai gyaran bayan ta gaida shi ya amsa mata ciki-ciki yaja motar suka wuce. Shiru motar har sun an yi nisa a tafiyar cikin arfin hali ta ce, Yaya dama baka wuceba ne? Mi kika gani? Ya fa a cikin wata irin kasalliyar murya data bata mamaki. Gashi ya i kallonta sam a yanzu. Itama sai kawai ta ce, Ba komai Bai sake magana ba, itama tai shiru har suka iso gida. Sai da ya gama parking ta mi a masa atm in tana godiya. Kansa kawai ya aga mata batare daya kalleta ba ko tankawa yanzu ma. Itama sai kawai ta bu e motar tai ficewarta. Da Hajiya Yaya dake daga can ofar sashensu da wata ba uwa suka ha a ido, ganin irin kallon da suke mata yasa duk ta tsargu, amma sai ta dake ta nufesu badan taso ba, sai dan mahaifiyarta ta mata tarbiyya na girmama duk wanda ke gaba da ita. Sannan kodan Yaya Yazeed dake iya arin sa na girmama Ammie zata iya shanye komai daga mahaifiyarsa itama. Tofa, kice agola kafi an masu gida an dawo kenan? Matar da suke tare da Hajiya Yayan ta fa a cikin yamutse fuska idonta akan Maanal dai-dai tana isowa inda suke. Wani harbawa zuciyarta tayi har tsakkiyar kanta. Ba wai yau ne karo na farko da aka fara kiranta da sunan AGOLA gidan ba, amma har yanzu ta gagara sabawa. A duk sanda aka kirata da shi kuma tana jin matu aci da zafi a ranta. Har takanyi yunkurin son barin gidan, sai dai yin urin nata baya zuwa ko'ina take komawa tai la was saboda wasu dalilai. Hawayen da suka cika mata idanu ta ha iye, tare da dai-daita kanta sannan ta an risina fuskarta da murmushi ta ce, Barka da gida Mamma. Aunty ina yini Kafin Hajiya Yaya ta amsa wadda ta kira da aunty in ta sauri ta cafe zancen cikin masifa, Oh kaji wani an iskan gaisuwa wai barka da gida sai kace wasu sa'oinki? Cikin sake hasala Hajiya Yaya ta ce, Kinga da yawa ai, idan batai iyayi ba ai bata cika jinin Asiya ba, Amma wai a haka Alhaji ke neman abama jinina ita Humm kar kiga laifinsa wlhy Yaya, tunda uwarta ta shanyesa kina ganin shima Yazeed in zasu barsa ne. Balle suna ganinsa shine gidan da uban gaba . ta fa a tana mai ballama Maanal wata shegiyar harara. Tsamm Maanal ta mi e kafin Hajiya Yaya ta bama anwar tata amsa. Cikin an sassarfa tabar wajen tana mai jin aci da ciwo sosai a zuciyarta game da cin mutuncinsu ga Ammien ta. Tarasa mi Ammie ta tsare musu a gidan da su duka basa aunarta... Shikam Yazeed tana fita ya kife kansa a saman steering yana mai cije bakinsa da masifar arfi. Kai bazai yiwu ba, dolene ya zigirgi i Daddy azo ayita ta are a bashi matarsa. Dan gaskiya yana cikin tashin hankali, da yasan ma abinda gyaran jikin nan zai zame masa yanzun nan daya hana yarinyar nan yinsa ko kuma ya i komawa akkota. an buga glass in saitinsa da akai da arfi ya sashi agowa. Sai da ya an saisaita kansa kafin ya sauke glass in. Da Hajiya Yaya yaci karo, ai da sauri ya janye idanunsa da sukai wani irin ka awar da duk mai hankali idan ya kallesa zai fahimci halin da yake ciki. Ita kanta Hajiya Yayan sai da taji wani iri a ranta, amma ta dake cikin masifa ta ce, Yazeed miye ha inka da waccan yarinyar? A ina ka akkota? an gyaran muryarsa data koma can asa yayi, kafin ya furta, Mamma anan ofar gida ne mai napep ya ajiyeta shine nace ta shigo na araso ciki da ita. Wani abu ne ya faru? Wata hararar bana son rainin wayo ta balla masa. Kafin cikin masifarta ta furta, Yazeed! Yazeed wlhy ka kiyayen, ni zaka maida sakarai ko.... No Mamma ba hak.... Hannu ta aga masa cikin tsawa, Bana son ji, ka sameni ciki yanzun nan . Tana gama fa a ta juya ta bar wajen. Iska mai kauri ya furzar daga bakinsa tare da sake maida kansa jikin steering yana mai lumshe idanunsa. Yafi mintuna biyar a haka sannan ya bu e motar ya fita yana mai saka glass a idanunsa domin oye abinda ke cikinsu. A falo ya sami mahaifiyar tasa da ar uwarta. Cikin girmamawa ya gaida innar tasa dake wani binsa da kallon urilla kamar mai son gano halin da yake a ciki batare data amsa masa gaisuwarsa ba ta ce, Yazeed! Anya kuwa kana son nemawa mahaifiyarka mutunci damu an uwanta a gidan nan. Wai kai bazaka bar batun yarinyar nan ba ne shin ko yaya kake nufi? Sai da ya an ha iye abinda ke masa yawo a ma oshi sannan ya furta, Aunty Please mun wuce maganar nan fa tuni. Dan ALLAH a barta kawai i a bari in dan ubanka. Yazeed ni dai kake son cigaba da tozartawa ko? Ni dai mahaifiyarka dana sha ba ar wahalar rainon ciki ka da na udar haihuwarka da shayar da kai. Asiya dai ta fini muhimmanci a wajenka ko? Shike nan kaje kayi duk abinda kake ganin dai-dai ne agareka. Amma ka sani ko mutuwa nayi kurwata bazata barka zaman aure da yarinyar can ba. Dan na riga na maka mata kamar yanda na fa a maka. Garama ka shirya tun kafin takaimu da bakanta a cikin gidan nan. Amma bari shi Alhajin dake aure maka ugu ya dawo gidan ina dai-dai dashi wlhy Kasa iya furta komai Yazeed yayi, sai wani irin ha iyar zuciya yake acan asan ransa dan mutum ne mai zuciyar tsiya dama. Haka suka cigaba da masa masifa bai iya sake cemusu komai ba har sai da ALLAH ya taimakesa Daddy yay kiran wayarsa sannan ya tashi ya fita domin amsawa. Daga haka bai koma wajen su ba ya gudu sashensa dan ya shirya gashi har yana neman