Sashe 93
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
biyar ne akan nata a zuwansu. Koda suka dawo cikin gidan fushi ta dinga masa, sai ta koma kula Fawzan shiko Ajwaad in ya sharesu. Hakan da yake yi idan tana tare da wani a cikinsu yake sa suke fa in suma yana kishi da su akanta.. _____________ Washe gari suna gama breakfast Ajwaad ya tasa Maanal gaba zuwa wajen kitso. Ita ko tana faman kuka da fa in bafa zataje ba. Sai da yar Oum ta lalla ata ta yarda bayan ta mata al awura. Koda suka fito tsakar gida inda an kekensa yake sai da ya hau itama ta hau daga gabansa tanata cika baki da iska. Shi dai bai kulata ba yaja keken suka fito. Ai tun daga gida har zuwa shagon Aunty Saloon duk inda suka gitta sai an musu magana. Dan Maanal fa cele ce a anguwar tasu saboda tsabar fitinarta da neman fa a. Yara ai ne batai rigimar da taja Ajwaad ya jibgesu ba. Da farin ciki Aunty Saloon ta tarbesu tanama Maanal oyoyo da dawowa. Itako ta ata fuska taje jikin Ajwaad ta ma ure idanunta cike da walla. Dariya Auntyn ta fara yi da fa in, Maanal ke baki girma da in kitso? Haba ar gatan Ajwaad Bestyn ta. Shi gashi yana son yaga ana gyara masa ke da kitso ke kuma ba ya so Baki Maanal ta sake turawa gaba da kallon Ajwaad, shima kallon nata yake yi. Sai ta sake ata fuska zatai kuka. A hankali ya kai dur ushe gabanta ya dai-dai tsahonsu hannayensa duka akan kafa arta cike da lallashi ya ce, Ba kin min al awari bazakiyi kuka ba? Ko kina son yaran anguwar nan su ganki su samu abin raina ki da tsokana Kanta ta girgiza masa hawayen dake cike a idonta na gangarowa. Hannu yasa ya share mata, To kada na ara ganin hawayen nan. Inba hakaba kuma na fasa shiga secondary in tare dake Da sauri ta ha iye kukan, cikin rawar murya ta ce, To bana bari ba Yauwa my sweet Besty. Fa a min mi kike so naje na saya miki? Ko awaran can? . Ya nuna mata waje can tsallaken titi da mai awara ke ta soyawa. Kanta ta jinjiina masa. Shima sai ya mi e tare da kama hannunta ya kaita saman kujerar wanke kan ya zaunar, fita yayi tana kallonsa daga nan. Bai wani jima ba ya dawo da awaran a leda. Lokacin har Auntyn Saloon tayi shirinta na fara wankema Maanal in kai. Dan duk ta fito da kayan shampoo inta da suka zo dasu a cikin ar bag. Haka komai na Maanal a tattale yake ga Ajwaad. Sam bai yarda a mata amfani da kayan wankin kan wajen saloon in ba, duk abinda yasan ana bu ata idan sukaje shopping da Abah ke kaisu duk arshen wata zai akkosa. Dan shi dama ko a wajen shopping in zakaga duk abubuwan da yake akkowa na Maanal ne. alilan zaka samu nashi. Kujera ya jawo gabanta sosai ya zauna, dan yasan bazata yarda ba sai anyi darun. Bai bata awaran ba ya ajiye gefe yacema auntyn Saloon ta fara. Kuka Maanal ta fara arin farawa ya girgiza mata kansa, sai tai shiru. Haka dai aka wanke kan yana ri e da hannunta da lallashi kamar wata ar mitsilar yariya can ba ar shekara kusan takwas ba. Koda aka gama shi da kansa ya goge mata kan da towel in da sukazo da shi ya aure mata shi, sannan ya dinga bata awaran a baki ana busar da kan. Da aka zo kitso kam daru aka sha na ha a, dan dole sai da ya ri eta, amma a hakan yasha cizo a hannu da bibbigewa. Kitson ma ba wani mai yawa ba dan shikku ne. Sosai ya mata yau aka saka mata bet. Maanal akwai gashi Masha ALLAH, dan sun biyo Ammie ne cikar gashi da tsaho kamar ba nasu ba. Sai faman sauke ajiyar zuciya take idanu sun yi jazur saboda kuka ta kama hannunsa tana dubawa, dan duk sayin ananun ha waranta. Sake fashewa tai da kuka tana shafa cizon da kallonsa, shima idon nasa duk ya ka a saboda kukan nata. A hankali ya ce, Minene kuma? Ba'an gama ba? Hannunta na bin wajen cizon ta ce, Da zafi ko? Muje na amshi magani wajen Oum na baka Murmushi yay mata da girgiza kansa, sai kuma ya shafa kitson nata da yay yau sosai ya ce, Babu zafi fa. Jiba yanda kanki yay yau. Ya kamata ki daina kukan kitso Besty kin girma. To ai Oum ta ce idan na girma zan daina Wane girma kuma ya rage Besty. Secondary fa zamu shiga ai kin girma ko. Ba kiga ni idan kika rakani wajen aski bana kuka ba A sanyaye ta ce, Zan bari. Besty muje gida zanyi barci Kansa ya jinjina mata tare da mi ewa. Cikin girmamawa ya kalla Auntyn Saloon dake kallonsu cike da sha'awa da mamakin irin wannan al'amari tamkar ba yara anana ba. Godiya ya mata ya auka bag in sannan ya du a Maanal dake faman lumshe ido ta hau bayansa. Kekensa ya kalla sai kuma ya kalla Auntyn Saloon in. Aunty zanje na kaita sai na dawo na auka To babu damuwa Ajwaad sai ka dawo. Ka gaishe da Hajiya. Maanal daru sai kuma next Maanal dai bata kulata ba, sai ma sake lafewa da tai a bayansa dan barci take ji sosai. Tana fita wanda ke a cikin shagon suka fara gulma. Aunty Saloon dai dariya take yi da sake basu labarin wannan sha uwa ta Maanal da Ajwaad dake birge kowa a layin tamkar ba yara ba... Kafin su iso gida har tayi barcin. Oum da Mamy na falo suka shigo. Muskar Oum da murmushi ta mi e tana fa in, Ai na sani dama da barci zaku dawo gidan nan. An sha darun ma yau kenan? Fuskar Ajwaad da murmushi shima ya ce, Tab Oum miza'a fasa. Duk na sha cizo Dariya Oum in tayi da fa in, In ba Bestien taka ba wazai cijeka a zauna lafiya Auta. Maza jeka ka kwantar da ita to akin Oum ya kaita ya kwantar, sai da ya rage acn akin ya cire mata ab hijjabinta sannan ya fito. Oum na tambayarsa ina kuma zaije yace zai akko kekensa ne. Daga haka ya fice. Mamy dai bata saka musu baki ba. Yana kuma fita suka ora da hirarsu da suke yi ita da Mamyn hankali kwance cike da farin ciki kuma kamar ba kishiyoyi ba. A haka Ajwaad ya sake dawowa ya samesu. akinsu ya wuce yana tambayar ina su Fawzan. Oum tace sunje aikan datai musu ne. Daga nan zasu duba malaminsu na islamiyya suji yaushe zasu koma. Dan tun wancan satin ya kamata su koma matar ya sayyadin ta haihu, haihuwar kuma tazo da matsala shine ya ara hutun, sai dai bai sanar da ranar komawar ba taka maimai. Ciki ya shige suma su Oum in suka mi e dan lokacin salla yayi......... ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 9:48 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ .......Abah bai samu zama da su Oum ba sai daren yau akan batun daya faru a Giro. Komai bai oye musu ba daya faru A to Z har hukuncin daya yanke akan Fadeel da Fawzan. Sosai tausayin Ammie ya sake baibaye Oum. Dan tamkar anwa uwa aya take jin Ammie a ranta ba ma wafciya kawai ba. ari bisa ari kuma ta bada goyon baya ga hukuncin mijin nasu. Ta kuma yabama dattakonsa. Itama dai Mamy ta jimanta al'amarin warai da gaske. Akan batun yara kuwa ta nuna kawaici kamar yanda ta saba. Daga arshe ma mi ewa tai tana fa in, Wannan maganarku ce Oum, mu an ALLAH ya sanya alkairi ne . Daga haka ta fice tabar falon. Da kallo duk suka bita. Kowanne na sake jin aunarta a cikin ransa daga Oum in har Abah. Mamy abar alfahari ce a garesu, dan suna matu ar alfaharin shigo da ita cikinsu. Tana da wasu irin nagartattun halaye masu matu ayatarwa a zahiri. Oum da Abah sun cigaba da tattaunawa, kafin suma su mi e bayan sun gama yanke yanda zasu fahimtar da yaran nasu batare da sunga an antar da su Shahidah a idanunsu ba. agaren Mamy kuwa koda ta shiga akinta kasa tsaye da zaune tayi. Ta jima a haka kafin ta auka waya tayi kira. Ba'a wani jimaba kuwa aka aga. Sallama tayi tana kaiwa zaune. Sai kuma ta ora da gaisuwa. Yaya mutanen nan ban san mi suke so dani ba. Shike nan ni bani da wani arfin iko akan ana ma. Daga mijin har matar kamar tare suka auro ni? Nifa na fara kaiwa ga ar da zan nuna ma matar nan ina bu atar ana nima. Sai dai ya sakan ko itama tayi zuciya ta haifi nata....... kuka ya sar eta. Numfashi aka sauke mai nauyi daga can, kafin cikin isa a furta, Kamila! Dama wannan shine abinda aka dinga guje miki tun farko. Amma kika kasa fahimta soyayyar mutumin nan ta rufe miki idanu. Daga baya aka sake nusar dake illar sakar mata yaran nan tun suna zanin goyo nan ma kika kasa fahimta ke wai neman soyayyar miji. Ai gashi nan, an da mijin duk suna a hannunta ke baki amfanu da komai ba sai ba in ciki da damuwa. Kin san wacece Hajiya Fateema kuwa akan mijin nan nata? Dukkan fa bincike sai da nayi a kansu. Akwai matsananciyar soyayya da sha uwa a tsakaninsu tun ta uruciya. Tun fa tana ar shekara goma sha a duniya aka aura masa ita. Shi ya raineta, gida