Sashe 27
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
musamman da nima nasan harkar zane-zane hubby nata ne. Kawai dai ina jin haushinki ne da tunanin baki son ha a jini dani, shiyyasa yau ba fanshe haushin ta nan, sai nake ganin kamar baki son wannan ha in da nake sonyi ne Asia. Alhalin ni kuma na aitu warai da gaske da son ganin jinina ya sake gauraya da naki kozan cigaba da samun nagartattun zuria daga tsatsonki a cikin zuri'ata. Hakan zai sake dun ulemu ya curemu waje guda. Tun akan Amal naso nayi wannan ha in, sai na fahimci hankalin Yazeed akan Maanal yake shiyyasa na wallafa raina a kanta. Kayi ha uri Daddyn Hameed sam ba haka bane kamar yanda kake tunani. Ka fahimceni dan ALLAH. Wlhy koda bana aurenka zan iya bama Yazeed auren Maanal. Domin ya taimakemu a ga ar da muke matu ar bukatar taimako. Zanma iya cewa ALLAH ya addara Manaal nada sauran kwana ne a duniya amma ya saka sanadin hakan a hannun Yazeed. Domin da ace kwannata ya are tun a randa muka fara ha uwa da sai dai wani zancen ake ba wannan ba. Dan haka ban ta a jin bazan bama Yazeed Maanal ba. Kawai dai hankalina na matu ar tashi kasancewar bakowane angare bane ke bu atar wannan ha in, hakan kuma zai iya cutar da Yazeed in kansa da ita kuma Maanal in dake fama da rauni irin na ciwo mai ha ari. Amma yanzu masalahar da aka samu zai taimaka komai ya zama dai-dai itama ta samu sassauci haka shima Yazeed in. Dan koba komai Hajiya Yaya mahaifiyace tana da tata darajar. Sannan Yazeed ya san komai daya shafi rayuwar Maanal, basai anyi sabon zama da zagaye-zagayen fa a masa da fargabar zai amsheta ko zai canja ra'ayi Hakane Asia. Na kuma fahimceki yanzu ari bisa ari. Zan kuma cigaba da addu'ar za in ALLAH akan al'amarin insha ALLAHU. Sannan abinda ya shafeta ki daina wani damun a kansa kanki ai addara ce, bata wuce kan kowa ba kuma, ALLAH kuma shine shaida bataje takai kanta ba domin yin hakan jarabawace, wanda ma suke aikatawa kai tsaye ko suke zuwa bariki su kama akin kansu suke auruwa cikin salama da kwanciyar hankali yanzu a asar nan balle ita. Saboda haka na amince Maanal tayi aikinta. ALLAH ya sanya albarka ya kuma sa hakane yafi alkairi. Wani irin da i ne ya ratsa zuciyar Ammie. Ta ame Daddy da yau tana amsawa da amin. Shima murmushi ya saki mai fa in gaske da kar arta sosai ya rungume. A ransa kuwa yana sake ganin fara aikin Maanal in wata masalaha ce. Dan zai fake da shi bayan anyi auren suyi zamansu acan, ita kuma wannan za in uwar Yazeed in anan cikin gidan yake son ta zauna tare da su saboda wasu dalilansa...... Tofa, mi kuke tunanin wai ya faru da Maanal ne? . Sannan zamuga yanda wannan cakwakiya zata __________ Wani irin farin ciki ne ya mamaye Maanal lokacin da sa on Daddy ya risketa akan amincewarsa tayi aiki. Su kansu su Shahidah sai da suka tsaya suna kallonta ganin yanda taketa murmushi yau kamar ba Maanal ba. Sai suma hakan ya sakasu a farin ciki. A karo na farko na tarihi Maanal taima RK text massage da albishir in amincewar Daddy. Ai ba'a ha a awa guda ba sai ga bawan ALLAH a gidan. Yau ko lalla atan da Shahidah keyi na taje ta samu RK in ba'ai ba. Yana kiranta yace gashi a gidan sai gata babu jimawa ta fita. Tunda ta fito ya zuba mata ido, sai ya zam tana takune tamkar da bugawar zuciyarsa. ALLAH ya jarabcesa da son wannan halittar warai da gaske. Yana kuma fatan mallakarta in har hakan shine alkairi a garesu. Maanal ta tsani kallo, dan haka sai da ta masa tsogumi akan kallon urillar da yake matan. Baice komai ba face basarwa yana sakin murmushi. Itama sai ta sharesa kawai ta shiga gaishesa. Ya amsa mata da kulawa, kafin ya ora da tambayar yanda abubuwa suka kasance. A ta aice ta fa a masa, bai damu ba dan ya gama karantar ta zuwa yanzu. Bata da son yin doguwar magana sai idan itace taso hakan da kanta. Shine ya dinga zuba mata zance da yanda abubuwa zasu kasance. Ya kuma tabbatar mata nan da kwana biyu zaizo ya amshi takardunta. Ya kuma bu aci ta an zazzana wasu samples na agogunan zaizo ya amsa gobe idan ALLAH ya kaimu dan zai sake nunama mai Companyn. Duk da dai ya nuna masa wanda ta zana a asibiti. Ta tabbatar masa babu damuwa zatayi in, daga haka sukai sallama ya fice ita kuma ta shiga gida. Kamar ko yanda sukai al awari a wannan daren ta nutsu ta zana agoguna masu shegen yau da aukar hankali fin kala goma. Dan har gabannin asuba tana wannan aikin. Hakan ya saka mata makara. Tana yin sallar asubahi kuma ta sake kwanciya. Bata farka ba sai aya saura. Ta samu RK yazo ya amshi zanen ma. Dan sun sanar masa tana barci yace kada a tasheta a barta tai barcinta, a bashi zanen kawai. Yana kuwa amsa bai jima ba ya wuce abinsa. Sai da ta tashi take jin yazo in ya amsa. Har ta auka waya kamar zata kirashi sai kuma dai ta fasa kawai. Tata tsumayen nasa kiran amma shima sai bai kira in ba har dare. Sai da tana shirin kwanciya ne ma sa onsa ya shigo. Ina Kaduna yanzu haka. Mun gana da Daddy da Ammie, na kuma amso takardunki suna hannuna. Amma sai da safe zan dawo Abuja in sha ALLAHU. Kiyi barci cikin aminci tare da mafarki mai nutsuwa gimbiyar mata Baki kawai ta ta e tare da jefa wayar saman gado ta cigaba da saka ma allan rigar barcinta. Sai kuma ta tsaya cak kalamansa na dawo mata. Ya gana da Daddy da Ammie kamar yaya? Kai itafa shishshigin mutum nan ya fara bata tsoro. Kaji bala'i ko mi ya kaisa Kaduna?. Rashin mai bata amsa ya sakata jan aramin tsaki ta haye gadon kawai ta kwanta. Addu'a tayi kamar yanda ta saba sannan ta kashe wutar akin tana sauke ajiyar zuciya......... ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama .......Maanal bata sake jin labarin RK ba tun ranar. Ya dai kirata washe gari yace ya dawo Abuja. Daga haka bata sake jinsa ba. Gashi ita kuma ta agu taji yaya ake ciki. Dan haka kawai sai ta wallafa ranta a aikin saboda zaman waje ayan kuma ya isheta. Da yaran Shahidah sun wuce makaranta itama da mijinta duk aiki suke fita, sai ita sai mai aiki kawai. Bata da aiki sai karatun novels da kwanciya. Amma kasancewarta sarkin kamewa da dakiya sai bazaka ta a fahimtar hakan ba kai tsaye. Sati aya dayin hakan sai ga Ammie da Amal sunzo. Matu ar farin ciki Maanal ta kasance a wannan ranar, gashi weekend ne duk masu gidan suna nan. Yini sukai dan Ammie tace bazata kwana ba. Babu irin shagwa ar da Maanal bataima Ammie akan ta kwana in ba amma tace sam ita bata sanarma Daddy zata kwana ba. Haka babu yanda zasuyi bayan magrib suka rakasu train station kasancewar jirgin asan zasu bi. Dama a cikinsa suka zo.... Kwanakin su Ammie biyar da zuwa da daddare tana shirin kwanciya sai ga kiran RK. Ido kawai ta sakama wayar tana kallo harta tsinke sannan ta kauda kanta. Sake kira akayi nan ma kamar bazata auka ba sai kuma dai mita tuna oho mata tai yun urin aukar, sai kuma taga bashi in bane Ya Yazeed ne. Fuska ta ata shima kamar bazata aga ba ta dai daure ta auka. Gaisheshi ta farayi da girmamawa kamar yanda ta saba. Shi kuma ya amsa mata cikin nutsatstsiyar muryarsa dake nuna alamar a kwance yake. Sun an yi shiru sai kuma ya katse shirun da fa in, Ina muka kwana akan batunmu Maanal? Shiru tai kamar bazatace komai ba. Sai da ta mula dan kanta ta amsa masa da, Yaya ni mikake son nace to. Ni duk abinda su Daddy suka yanke zanyi biyayya a kansa kawai Saboda dama baki sona? Ni dai Yaya bance ba. Amma ka tausaya mun mana. In dai kai namiji ka ha ura ka musu biyayya ni kuma sai naje nace ba haka ba. Humm shike nan, amma ke yanzu baki jin kishin na fara auren wata kafin ke? Karan farko ta saki murmushi mai fa i, sai kuma ta zame ta kwanta. Yaya ko naji kishi yaya zanyi. Ni dan ALLAH mubar ma maganar nan kawai ALLAH yasa haka shine yafi alkairi Murmushi taji ya saki da ga can, sai kuma ya ce, Okay shike nan an barta. Tunda dai na gane ana kishina na gode Shiru ta masa batace komai ba. Shima daga haka yay mata sallama akan maybe gobe ma ya shigo Abujan, zai kuma le o ya fara ganinta kafin ya fara sabgoginsa. Daga haka sukai sallama. Kamar jira RK yake dama, Yazeed yana yankewa kiransa na shigowa shi kuma. Sai yanzu ma ta lura ya mata kira yafi goma ashe sanda take wayar. Kanta kawai ta an girgiza. Sai da tana gab da zata tsinke sannan ta aga. Muryarsa a cinkushe ya mata sallama. Amsawa tai itama ciki-cikin tai shiru. Tsahon minti aya babu wanda ya sake magana. Oh bama zaki gaisheni ba? RK in ya fa a daga can. Yitai kamar bazata tanka masa ba sai kuma ta ce, Good evening Humm good evening to baturiya. Fatan kin yini lafiya? Itama ta amsa masa a da ile jin yana mata magana cikin wani ji da kai. Humm! saboda kina