Sashe 17
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai ka arar daku malam Rafeequ ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ Abubuwan da nake saidawa Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries ______________ ........ Kamar ya sonta Aunty? Wace magana kike haka? Ba mahaifinsu aya ba? Ba mahaifinsu aya ba Rafeeq. Dan Alhaji Usman bashi ne ya haifi Maanal ba ita da yan uwanta biyu mata. annen Maanal maza biyu da kake gani Waleed da Hameed sune an dake tsakaninsa da Hajiya Asiya. Kaga ko zata iya kasancewa Yazeed son Maanal yake yi shiyyasa. Kuma kamar yanda ka fa a ya fahimci kana sonta ne a yanzu shiyyasa ya canja maka. Amma ka bari zan bincika komai in sha ALLAHU Wata irin zufa ce ta gauraye illahirin jikin RK. Idanunsa har sun ka a na damuwa. Yana ganin ya fara bin hanyar nasara ashe akwai sabuwar ura a tafiyar, dan tabbas indai har Yazeed son Maanal yake da wahala shi ya samu. Ammie dai bazata an mijinta ba, haka shima Alhaji Usman in bazai ansa ba, ita kanta Maanal in bashi da tabbacin bata son Yazeed in ma a..... Kaga ka kwantar da hankalinka fa, in sha ALLAHU komai zai kasance cikin sau i. Ba nace zaka iya samun Maanal bane cikin sau i, ban kuma ce bazaka iya samunta ba tunda komai na ALLAH ne. Dan ha in Yazeed da Maanal zai yi matu ar wahala saboda nasan wacece mahaifiyar Yazeed. Hajiya Sadiyya da wahala ta amince da wannan ha in musamman yanda nasan tayi bala'in tsanar Hajiya Asiya. Dan haka kada ka karaya da izinin ALLAH nasara tamu ce, kai dai kawai ka cigaba da neman soyayyar yarinyar shine babban makami a hannunka bayan goyon bayan Hajiya Asiya a yanzu Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke. Sai kuma ya zari handkhachief ya goge zufar goshinsa. Hakane kam Aunty, ina jin tsorone kawai kar ya kasance itama Maanal in tana sonshi, wannan kam kinga bazan iya jayayya da kowa ba tunda itace mai zaman auren. Eh tabbas kam, amma nidai ban ta a jin akwai wata ala ar soyayya a tsakaninsu in ba gaskiya. Tunda da akwai na fa a maka mahaifiyar Yazeed sai a hankali ce, da sam bazata bari a zauna lafiya ba. Amma yanzu ma inda wata shawara, ka samu lokaci ka shigo Zaria wajen Abbansu Najma. Ka masa bayani a matsayin kana son ya maka iso wajen Alhaji Usman in akan maganar mana, ni kuma kafin kazo zan sake bincikawar kamar yanda nayi maka al awari Ajiyar zuciya mai ha e da ayataccen murmushi RK ya saki, sai kuma ya kama hannun ar uwar tasa ta sumbata yana fa in, ALLAH ya saki a aljanna Aunty na mai share kuka na Dariya tayi tana mai kai masa an rankwashi a kai, hakan ne ya sakashi shima yin dariyar sannan ya tada motar suka cigaba da tafiya...... Alhamdullah wannan zuri'a suna cikin farin cikin farfa owar Maanal a yau, duk da ba'a barsu sun ganta ba har zuwa yanzu saboda likita dake tare da ita hakan bai hana bayyanar murmushi a fuskokinsu ba. Sai da su Dr Ranjet suka gama mata dukkan abinda ya dace kafin su ka bu aci Nene dake goge mata jiki kullum ta shiga ta goge matan. Shahidah da Amal kuma sukai shirin komawa gida ha o mata abincin da Doctor yace zata iya ci. Bayan kammalawar Nene Daddy da Ammie ne suka fara shiga. Tana kwance fayau da ita saboda ramar da tayi na ciwo. Gaba aya na'urorin da aka sanya mata a kwanakin da suka gabata an janyesu, sai igiyar daketa jikin hancinta kawai. Jin amshin turaren Daddy kusa da ita sosai ya sakata bu e idanunta da suka an kumburo, daga cikinsu sun an yi ja sun kuma ara girma. Daga shi har Ammie dake tsaye ta zubama idanun, sai kuma a hankali ta saki murmushi mai sanyi tare da mi a musu hannunta. Ammie dake murmushi tana hawaye ce ta kama hannun tana kaiwa zaune bakin gadon kusa da ita. Yayin da shi kuma Daddy ya an du o ya shafa kanta yana murmushi shima, kafin yakai zaune a kujerar gaban gadon. Sannu kinji Daughter. ALLAH ya baki lafiya yasa kaffara ne Kanta ta an jinjina tana sakin murmushi, sai kuma ta motsa lips inta a hankali ta furta, Amin Daddy nagode Murmushi ya sake mata, tausayin yarinyar da aunarta na sake gauraye zuciyarsa. Maanal ta maida kallonta ga Ammie dake sharar hawaye. Nan ma a hankali ta ce, Ammie ki daina kuka na samu lafiya fa . Kai Ammie ta shiga jinjina mata tana share hawayen da sakin ar dariya. Na daina Maanal kinji, ALLAH ya ara miki lafiya da nisan kwana. ALLAH yasa kaffara ne, ALLAH ya rabaki da wannan ciwo gaba Amin Ammie nagode. Ina su Didi fa? Sunje gida yimiki abinci yanzu zakiga sun dawo. Ko kina son cin wani abune a kirasu su yi miki? an shiru tayi alamar tunani, sai kuma ta kalla Daddy dake ta kallonsu yana murmushi, itama an murmushin ta masa sannan ta sake maida dubanta ga Ammien. Ammie sumin faten dankali, sai kunun gya To shike nan bari na kirasu karsu taho Kai Maanal ta jinjina mata, yayinda Ammie ke arin kiran su Amal. Dai-dai nan Yazeed ya shigo akin da sallama Waleed ri e da hannunsa, sai Hameed biye da su. Daddy ne ya amsa masa. Yayinda ita kuma ta zuba musu raunannun idanunta. Da sauri Hameed da Waleed sukayo inda take cike da farin cikin ganin idanunta a bu e. Hannunta duk suka kama suka ri e suna kaiwa dur ushe daga asa ta yanda fuskokinsu zasu daidaita da tata. Alhamdullahi Didi ta samu lafiya . Cewar Hameed yana sake ame hannunta. Shima Waleed cike da oki ya furta, ALLAH mun gode maka yau muna cikin farin ciki Daddy Didi ta bu e ido aramar dariya Daddy yayi da fa in, Alhamdullahi shima. Maanal cikin magana a hankali tace, an turai kamarku daban . Dariya duk suka yale da shi. Itama saita maida kallonta ga Yazeed dake tsaye kawai yana kallonsu fuskarsa awace da murmushin farin ciki. Kallon da take masa ya sashi arasa arasowa gaban gadon sosai. Sai kawai ta lumshe nata idanun a hankali ta kuma sake bu ewa duk a lokaci guda. Alhamdullahi. Sannu Maanal ALLAH ya ara lafiya yasa kaffarane kinji Murmushi ta sakar masa a karo na farko, murya can asa ta ce, Amin Yaya nagode Amsa mata yay cike da farin ciki, jiyake tamkar ya rungumeta a jikinsa sai dai babu damar hakan. Balle ma ga Ammie a wajen ga Daddy. Suna a hakan dai kuma sai ga RK. Tunda ya shigo idanunsa akan Maanal in ne shima, itama dai shi in take kallo da unbin mamaki. Yayinda zuciyarta ke raya mata (shi wannan duk inda naje sai ya bini ne shin?) Rashin mai bata amsa yasata janye idanunta a zahiri daga kansa. Shima sai dai janye nasan yayi tare da arasowa ya gaida Daddy da Ammie cike da girmamawa. Maanal ta sake shan mamakin ganin yanda duka amsa masa da kulawa da alamar sanayya sosai kuma. Dubansa ya maida a kanta yana mai an kashe mata ido, hakanne ya sakata yimasa aramar harara. Murmushi ya saki mai fa i da arin aukar file inta dake a drower in gefen gadon yana fa in, Gawa ta i rami yaya jikin? Dariya Daddy da su Waleed sukayi, yayinda Ammie tai an murmushi kawai. Yazeed kam fuska ya sake tamkewa kamar bai san minene dariya ba. Yayinda Maanal ta an tsuke fuska itama tana hararar RK in yanzu ma. Yi yay kamar bai ganta ba ya mi ama Yazeed hannu cike da sha iyanci yana fa in, Babban Yaya barka anwa ta mi e. ALLAH ya ara lafiya yasa kaffara ne ya kiyaye gaba Rasa abinyi Yazeed yayi, sai mamakin RK in ke sake mamaye masa zuciya. Wani gefe kuma na tunanin RK fa bawai yasan ainahin ala arsa da Maanal bane, dan kuwa kallon yayanta uba aya yake masa kenan. Daurewa yay ya an sake fuska ganin Daddy na kallonsu ya bashi hannun shima suka gaisa yana amsawa da, Amin doctor muna godiya, kuma kunyi ari ai sai fatan alkairi a gareku Doctor! Manaal ta fa a a hankali cikin su utar baki idonta akan RK. Kafin ma RK yay wani yun urin bata amsa Waleed yabata amsar da Eh mana Aunty shine likitanki tare da Dr Ranjet. Kuma yana da kirki kullum sai yaje damu yawo ya saya mana abubuwa, yana kuma cemana mu dinga miki addu'a a dallarmu ALLAH ya baki lafiya ko warke gaba aya ki daina wannan ciwon Sake dai kallon RK in Maanal tayi kawai, zuciyarta na wani irin motsawa a irjinta da sauri-sauri kamar ma ciwon nason dawowa sabone komi. Ganin kallon da Ammie ke mata ta sata lumshe idanu kawai tai shiru dan ita kam bata kuma san abin fa aba bayan hakan. oyayyen murmushi kawai RK yayi yana cigaba da dudduba abinda ya kamata, sai kuma ya fara mata tambayoyi a hankali. Dole ta bu e idanunta a kansa dan yanda yake magana can asa- asa tsigar jikinta har tashi take. Kasa amsa masa ko aya tayi da baki, sai jinjina masa kai kawai da girgizawa. Wani irin kishi ne ya turni e Yazeed, dan shi mutum ne mai kishi sosai. Rai a ace ya an du o shima gareta murya can asan ma oshi ya furta, Kina son cin wani abu Miss? Idanunta ta an maida garesa, Yaya su Didi na zuwa da abinci ai