Sashe 45
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tai wasa. Suna nan suna ar hira ita da Shahidahn dan Huznah ba saka musu baki take ba sai ma latse-latse take a waya kamar bata falon mai gidan ya dawo... Dalilin dawowar tasa yasa Shahidah shigewa part insa, aka bar su Maanal kawai. Sai itama ta mi e ta taimakawa Linda suka kwashe su Barrah da sukai barci a falon. Daga haka tacema Huznah ita zata shige ta kwanta. A ciki Huznah ta amsa mata, Maanal bata damu ba tai wucewarta. Ita kuma ta rakata da harara. Maanal na shiga akin kiran RK ya shigo mata, bata aga ba sai da takai kwance, ta gaisheshi a mutunce kamar yanda ta saba, daga haka ta fara mata hira da albishir in gobe in sha ALLAHU yana hanya. Ganin yanata jan hirar ta fara masa hamma, dole yay mata sallama. Kamar jira sai ga Yazeed shima ya kira, jitai kamar zatai kuka, haka dai ta aga. Dawa kike waya haka Maanal? Furucinsa na farko kenan maimakon amsa mata sallamar da tai masa, muryarsa a cinkushe. Sai da ta an yi jimm kafin a nutsenta ta bashi amsa da, Rafeeq ne! Rafeeq!? Sai da ta an lumshe ido saboda yanda ya maimaita sunan RK in a kausashe yanzu kafin ta ce, Uhhum! Okay yayi . Ya fa a yana yanke wayar. Shiru tayi na mamakinsa, Yazeed mutum ne mai nutsuwa da fahimta, sannan yana da ha uri, zata iya cewa tunda ta ha u da RK bai ta a tunkararta akan al'amarinsa ba sai dai can a tsakaninsu. Amma yau minene ya hasalashi haka? Kai ita kam taga takanta. RK ya nuna fushi idan ya ganta da Yazeed ko tana waya da shi, yanzu shima kuma ga Yazeed in zai fara nashi. Ita kam dan ALLAH karsu rikita mata lissafi mana, suma barta da abinda ya dameta... Tana cikin wannan yanayin Huznah ta shigo, bata mata sallama ba dan haka itama tai kamar bata san da shigowarta ba. A gadarance ta jefa wayarta saman gadon, fuuu ta wuce bathroom, ita dai Maanal binta tayi da kallon mamaki, bata jimaba ta fito, ta bu e akwatinta ta canja kaya sannan ta hawo gadon. A mamakin Maanal dai taji Huznah na jera fillos a tsakkiyarsu, sai kawai abin ya bata mamaki ta saki murmushi. Bata kulata ba tai addu'a taja barko. Barci take son yi saboda gajiya da tayi ga gobe ma dole ta fita aiki, amma Huznah ta hanata sai charting take, kuma voice note. Tun Maanal na dauriya har dai ta mi e tsam a gadon ta koma saman sofa doguwa dake a akin, kwanciyar bata mata wani da i ba amma ta ha ura anan in duk da nan in ma ba tsira tai ba tana jin Huznah in da bata fasa abinda take ba harda su aka dariya kamar ba dare ba. Daga arshe bata san sanda tayi barci ba ita dai, dan itama ALLAH ya taimaketa barcin yay awon gaba da ita. Da asuba kuma koda ta tasheta in tashi tayi, sai kawai ta yaleta. Har gari ya waye tai shirin fita aiki Huznah ta i tashi salla. Sai kawai ta fice abinta tana nema mata shiriyar UBANGIJI. Yau ma Shahidah ce ta ajiyeta a office sannan ta wuce nata aikin, tun a harabar companyn suke gaisawa da mutane har ta shigo. Dama dai tsakaninta da kowa gaisuwar ce, rashin yawan fara'arta da yawan magana ma kesa mafi yawansu ke kiranta da sunan mai girman kai. an rukuninsu mutum uku ne kawai sukazo, ta gaisa da su taja kujerarta ta zauna. Dama ita ka aice mace a cikinsu, shiyayasa daga gaisuwa sai zancen aiki ke ha ata da su. ALLAH kuma ya taimaketa kujerarta itace farkon shigowa, suma ganin yanda take ha e fuska da kame kanta yasa suke shakkar shige mata duk da wasunsu na kwa ayin hakan tun ma a ran farko da tazo. Aikinta ta kamayi kawai kamar yanda ta saba, a haka sauran suka iso, kowa yazo zata ago su gaisa daga haka ta maida kanta ga aikinta. Kusan eleven ta tashi zuwa office in Director Mustapha. Duk da kallo suka bita, wanda ke zama kusa da ita cikin yin asa da murya yace ma na kusa da shi, Wato yarinyar nan akwai girman kai wlhy Ema.. Caraf Yaqub da ke facing insa ya ce, Ba wani girman kai wlhy, ta dai san kanta ne. Idan mace ta cika faran-faran ace ma ballagaza, idan ta kame kanta ace girman kai. Kufa lura ita kamar yanayintane ma haka, miskila ce kawai Tab ai ni kuma bana son miskilar mace gaskiya. Ita mace ko yaya da sau in kai tafi da in rayuwa A wajenka ba..... Oh to kodai santa kake yine wai Yakub To laifi ne idan na sota Zaharadeen, naga dai namiji ne ni. Kuma in inda zata amsa muku son nata kuke shiyyasa kuke gulmarta. Yarinya na girmamaku amma bakwa gani. Yanzu da sakewa take cikinmu da surutu da fara'a sai kuma ace ta saki kanta a tsakkiyar maza. Ta kuma kama kanta kunzo kunayi da ita mtsooww! Ya mi e ya bar musu wajen. Duk da kallo suka bisa, sai kuma suka kalla juna cikin yamutse fuska. Wannan guy in na kula fa son yarinyar nan yake Oh kai sai yau ka gane, ai na jima da fahimtar hakan. Kuma banga laifinsa ba dan koni ALLAH na yasa Dariya suka sanya a tare harda tafawa. Maanal kam da bata ma san sunai ba kanta tsaye office in Designer Director Mustapha ta nufa. Tana shiga Elevator massage ya shigo wayarta, arin dubawa ta fara yi sai taga Yazeed ne. Nutsuwa tai a karanta sa on, sai ya zam har elevator in ta tsaya hankalinta nakan wayar, a haka tai arin fitowa batare da duban gabanta ba. A dai-dai lokacin da CEO AA Darma ke isowa ga elevator in Assistant insa biye da shi. Ya riga ya kawo jiki, kamar yanda itama ta riga ta taho gashi hankalinta ba a wajen yake ba balle taja da baya kawai sai jitai ta bugi abu. A an razane tayi baya, wayarta ta su uce asa hakama gilashin idanunta da document in duk suka tarwatse kasa. Sosai ta ago cikin acin rai dan ganin wanene da wannan aikin bayan ta gama bin kayan da kallo aya bayan aya. Shima sai hakan ya zam dai-dai da tashi agowar bayan ya gama bin kayan da kallo musamman zanen agogon da yay masifar aukar hankalinsa. Wani kalar zubama juna ido sukai kowanne fuskarsa a matu ar tamke, sai dai na Maanal in ya an cika da ruwan hawaye dan har yallinsu ya nuna. Yanda tai masa iri da idanu sai ka auka zata fara zazzaga masa ruwan bala'i ne, dan tuni AS insa da wasu da suka zo wajen bayan faruwar accident in duk sunyi kasare cikin unbin mamaki suna son suga mizai faru. Amma mi, a mamakin kowa sai suka ji cikin sanyin murya Maanal in ta furta, I'm sorry Sir Ta are maganar da rissinar da idanunta harma da kanta cikin nuna girmamawa. Shi kansa wani irin rumtse idanu yay da masifar arfi, sai kuma ya zagayeta ya shige cikin elventor in batare da yace komai ba. Wannan abu ya bama kowa mamaki, hatta da AS insa daya gama tattaro ma Maanal kayayyakinta. Wannan shine abu na biyu daya faru tsakanin Boss da Maanal ko yace na uku harda kaita gida da sukai jiya. Shi sai ma ya rasa kalar tunanin da zai yi akan al'amarin. Sauran ma duk sun ma Maanal sorry, kanta kawai ta jinjina musu da an yin murmushi ta wuce zuwa office in Director Mustapha. Bayan tayi knocking aka bata iznin shiga. Ta gaishesa da girmamawa kamar yanda ta saba yima kowa. Shiko ya amsa fuskarsa da murmushi tare da nuna mata kujera. Kanta ta an girgiza masa da ajiye document in hannunta saman desk insa. Sir dama na kammala ne shiyyasa nace bara na kawo maka sai ka duba Yauwa sister Maanal dama kamar kin san yanzu nake shirin nemo ki, dan ban jima da baro office in CEO ba akan batun. Woow ai sai naga ma kamar wa an nan sunfi ma wancan Ita dai Maanal komai batace da shi ba kanta a asa, sai da ya gama santinsa sannan ya sallameta akan ta zama cikin shiri koyaushe za'a iya nemansa a conference room. Koda ta koma saita samu har gulmar abinda ya faru tsakaninta da CEO in taje can. Dan ta wuce wasune nayi batare da su sun farga da ita ba. Kowa bata kula ba har abokan zamanta da wasu ke us ta zauna ta cigaba da aikinta. Bayan anje break daga massalaci Maanal ta dawo kan aikinta, dan tunda tazo companyn bata ta a zuwa kitchen cin abinci ba. Kullum da abinda zata ci take zuwa daga gida, dan haka bata ta a maida hankalinta ba. Tana cikin aikin ta samu kira daga head of design office ana nemanta a conference room. Tashi tai auke da drive in data ha a abinda zata gabatar ta wuce. Batayi mamakin ganin duk manyan companyn a wajen meeting in ba, dan ta fahimci project in nada matu ar muhimmanci. Sai da ta gaidasu cikin girmamawa sannan ta zauna a kujerar da aka nuna mata. Kusan zaman mintuna biyu sannan CEO ya shigo AS nashi biye da shi. Dukansu mi ewa sukai domin girmamawa, sai da ya zauna a kujerar da AS ya gyara masa sannan yay musu nunin su zauna. Duk zaman sukayi, ita dai Maanal bata yarda ko inda yake ta kalla ba. Sai da Director Steven ya mata magana sannan ta tashi. Kamar waccan ranar yau ma ta gabatar da sabbin zanenta, tare da bayanai akan yanda zai iya kasancewa. Yau in ma dai kowa ya yaba mata matu a, dan hatta shi kansa CEO in a mamakinta ya wani zuba mata ido, ita dai kame kanta ta arayi. Tattaunawar ta cigaba da gudana, musamman ta angaren Head of design and engineering da R&D Director da Sales and Marketing Manager sai shi CEO in dake an saka baki. Sun kwashi kusan awa aya da rabi kafin a tashi, yau kam Maanal ita ta fara fitowa daga conference room in tana sauke