Sashe 81
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
suke mata matu a kasancewar itace kamar auta a gidan yanzu. Kowa ya kwaso abunsa zai ce Maanal. Musamman ma mahaifinsu da suke kira Baabu. Dawowarsu cikin Kano sun samu abubuwan cigaba da dama, ciki harda arin girma da Baabu ya samu, ita kuma ta fara kasuwancin turarruka da gyaran jiki irin na mata. Inda suke sabon wajene da aketa gine-gine, dan ko gidan dake a jikin nasu ma ana kan gina shi ne ba'a kammala ba. Sai dai an kusa kammala aikin. Hakan yasa kusan kullum zakaga mai gidan yazo da yaransa maza uku musamman ma weekend. Jefi-jefi sukan an gaisa da Baabu idan anyi sa'a yana gida ko ya dawo wajen aiki. A haka ranar wata asabar yana gida suka tashi da shirin yin alala da yace yana bu atar ci. Ammie ta kammala gyara wake ita da Shahidah da zata kai marka e. Sai kawai Maanal ta sanya rigima itama zataje. Cikin haushi Shahidah ta ce, Dama kin bar damun kanki dan babu inda zanje dake. Haka kawai muje kita jibgar yaran mutane a gidan marka en kamar ranar da kika fasama ar mai marka en kai Ihu Maanal ta sake wallarawa tare da zubewa asa tana burgima akan ita wlhy sai taje fa. Dai-dai nan Ammie ta fito da bulala da nufin tsula mata amma sai Baabu ya hana ta hanyar amshe bulalar ya aga Maanal daga asan. Daga haka ya fita da ita a gidan yana lallashinta. A dai-dai lokacin motar makwafcin nan nasa ta iso anguwar. Baabu bai wani maida hankalinsa ba dan baima san shi bane kasancewar bawai ya wani ri e motar tasa bane. Sai da yay parking a gaban gidan nasa ya fito tare da matasan samarin ansa uku sannan Baabu ya maida hankalinsa kansa. Sun gaisa cikin mutunta juna, yayinda suma yaran suka gaida Baabu da girmamawa. Ya amsa musu da kulawa yana mai shafa kansu, yayinda shima babansu yakema Maanal wasa. an samari yaya sunanku? Cewar Baabu yana shafa kan aramin su. Babban ne ya bashi amsa da. Ni Fadeel. Wannan Fawzan. Sai Auta Ajwaad. Masha ALLAH, ALLAH ya albarkaci rayuwarku manyan gobe. A tare suka amsa da Amin. Yayinda mahaifinsu keta faman murmushi saboda surutun da Maanal ke zuba masa. Sai kuma can ta kalla Ajwaad dake ta faman cin chocolate insa, cikin an tura baki ta ce, Kai yaron nan bazaka tsammin alawanka bane. Inata ha iyan yawu amma sai sha kakeyi rowa haramun dai Ba aramin dariya ta basu ba. Banda Ajwaad an kimanin shekaru goma sha aya daya wani yamutsa fuska ya harareta ya auke kansa. Sai Baabu da ya an harareta shima. Amma ita ko'a jikinta ta maida kallonta ga Babansu ta na sake fa in, Abbansu kace masa ya tsammin raina ya biya Kinga manta da shi Babyna. Muje na baki ina da ita da yawa. Daga yau kuma kema ni Abbanki ne ba nasu su ka ai ba. Cike da murna tace, Gaba yay da ita zuwa motarsa. Ya fiddo chocolate uku ya bata biyu a hannu, tare da are aya ya sake mi a mata. Cike da jin da i ta amsa. Tare da juyawa ta murgu ama Ajwaad baki da fa in, Mai rowa an wuta. Nima kuma ga nawa Harararta nan ma yayi. Yayinda su Fawzan sukayi dariya. Shiko Baabu duk kunya ta ishesa. arfin halin Maanal da banne a rayuwa. Shegen surutunta da wayonta da suka girmi shekarunta na tada masa da hankali. Duk inda ake neman fitinannen mutum aka samu Maanal an rufe littafi kawai. Sai dai yana mata fatan idan ta ara girma ta canja daga hakan.. iri- iri da zai shiga gida yace tazo suje ta i. Dole babu yanda ya iya ya barta wajen Alhaji kamar yanda ya ro Yini guda Maanal na tare da Alhaji Aliyu Darma, Tare da yaransa uku da tuni ta saki jiki da su. Musamman Ajwaad da tunda ya fito da kayan wasansa ta nani e masa. Lokacin da rana tayi sai ga Shahidah da kula cike da alala an kawo musu. Sosai Alhaji Aliyu ya nuna jin da insa tamkar ya ari baki dan godiya. Anan ma Shahidah tayi-tayi Maanal ta bita suje gida amma ta i. Dole ta barta itama ta tafi. Sai da akai la'asar sazu tafi sanan su Fawzan suka rakata har gida da ledan kayan ciye-ciye da kulan da aka kawo musu alala sukai godiya. Yayinda ita kuma ta shiga kuka saita bisu, sai da Baabu ya mata tsawa sannan ta nutsu. Dan a duniya Maanal na tsoron hargagi musamman na Baabu.. Wannan rana itace sanadin tarayyar wa an nan ahali guda biyu. Dan kuwa washe gari sai ga itama mahaifiyar su yaran ta biyosu domin yin godiya. Anan ne kuma ta tarar da Ammie nama wata amarya gyaran jiki, itama tace ai sai ai mata kuwa.. tunda tazo Maanal na manne da ita. Kasancewar yaranta ita duk maza ne tana masifar son ar budurwar yarinya, shiyyasa tana ganin Maanal da jiya tasha labarinta a wajen anta yarinyar ta shiga ranta. Ga wayonta da surutunta na sakata nisha i. Yau in ma dai da yar aka raba Maanal da su, musamman Ajwaad da wasansu na yau yafi na jiya armashi. Dan yau ya saki jikinsa ba kamar jiyan ba. Haka yake bashi da saurin sabo sam, akanyi ba i a gidansu kwana da kwanaki babu ruwansa da su, dan shi yarone mai irin shegen tsantsenin nan, ga zuciyar tsiya da ulafucin iyaye. Ammafa idan ya soka to yaso ka kenan. Idan kuwa baka masa ba to babu abinda zakai masa ka birgesa ko kaja ra'ayinsa da shi. Shiyyasa a yau in ma mamakinsa ya kasa barin Oum ganin yanda ya saki jiki a gidan tamkar a gidansu. Dan duk inda kaga Ajwaad yaje yaci maka abinci kansa tsaye to lallai yanayi da masu gidan.... Kafin Alhaji Aliyu ya kwaso iyalansa su tare a sabon gidan nasu daya ha u matu a gaya sha uwa da zuminci mai arfi ya shiga tsakaninsa da iyalan Baabu ta yanda har suna kallon kansu tamar wasu an uwa na jini. Oum ba itace kawai matarsa ba, ashe tana da amarya ma, sai da suka tare su Ammie suka sani. Bayan tarewar tasu kuma sai al'amarin ya ara arfi fiye da tunanin mai hasashe. Ba sha uwar ahalin biyu ne kawai abin mamaki ba. Wadda ke a tsakanin Ajwaad da Maanal tafi zama abin kallo ga kowa. Dan takai a yanzu ako ina aya yake aya na wajen, shiyyasa idan baka sani ba baka ta a gane ainahin gidan kowannensu. Dan takai yanzu ma Maanal ta i zama a makarantar da take yi da yan uwanta. Da safe anta dagama kenan tace ita Ajwaad zata bi tasu makarantar. Anyi lallashin, an daka, anyi kurarin duk a banza. Hakan yasa Alhaji Aliyu ro ar Baabu damar maida Maanal makarantar su Ajwaad in, kasancewar itama tana tare da Nursery, primary harda da secondary ne a tare. Da yar Baabu ya yarda dan bashi da yanda ya iya, haka aka maida Maanal makarantar su Ajwaad amma a angaren Nursery. Shiko yana a primary 3 ne. To ashe rigima bata are ba, dan kuwa Maanal sam bata zama ajinsu saina su Ajwaad. Anyi-anyi amma ta i, da malaman sukaga tanada walwar karatu matu a, dan duk abinda akayi kafin kace me ta aukesa a kanta harma tafi wasu an ajin sai kawai aka yaleta. Dan koma an kaita can in ba zama take yi ba, sai dai taita jibgar an jama'a tana kukan ita dai wajen AA zataje. (Dan itace ta saka masa AA daga ji Oum ta fa a ta kama ta haye tana kiransa AA). Hajiya Maanalu mai abin mamaki kenan. Dan daga Nursery 2 dai tuni tayi jumping zuwa primary 3 abinta. Hakama a islamiyya tuni ta koma ajin su Ajwaad. Dambe da rigima kuwa sai abinda ya aru. Duk da tana a cikin wa anda suka girmeta kullum cikin takalar tsiya take. Taimaka rashin kunya kace zaka daketa ka gamu da Ajwaad. Dan duk abinda zai ta a Maanal a duniyar nan Ajwaad baya aunarsa. Hatta Ammie idan ta daki Maanal sai taga fushi a fuskarsa. Idan ko su Shahidah ne duk da sun girmesa koda yake kusan sa'an Amaal ne yana girmeta ka an sai fa yarama mata. Idan kuwa yana gidan tai laifi Ammie tace zata daketa sai yaje yace shi a dakesa a maimakonta, idan kuma ta riga ta ritsata tana duka zaije ya kareta shi a dake san. Idan abu aka bama aya aya bazai ta a cinsa ba sai aya na nan. Hatta da kaya ya koma yanzu iri aya ake musu, idan kuma ya banbanta na mace da namiji kamar atamfa, lass, yadi to dole a akko kala guda. Ajwaad shine tsifar kan Maanal, shine rakata kitso, shine wankin ananun kayanta irinsu pant, hula, vest da sauransu. Haka shima nashi idan zai yi tare zasuyi tana jagwalgwalo. Tun ana aukar abun nasu wasa har kowa ya fahimci ba wasan bane aka kawo ido aka zuba musu. Sai dai iyayen na matu ar kulawa da duk wani motsinsu saboda tsoron bin wata hanya mara ma'ana da a yanzu har yaran akan samu a ciki.... Alhamdullah a yanzu dai haka Maanal nada shekara tara cif a duniya, yayinda Ajwaad keda goma sha biyar. Suna a ajin arshe na primary. Kasancewar Ajwaad nada tsayi kamar an uwansa tuni ya tserema Maanal a girman jiki fintinkau duk da dama can ya fitan. Itako tana tsaka tsaki a tsayi saboda bata gama girma ba, gata muguwar siririya kamar ka hureta ta zube a asa. Zuwa yanzu sha uwarsu ta sake wuce inda ake tunanani, baka isa kaji kansu ba. Hatta abinci tare suke cin abinsu. A hakan ma dan ana tsaye a kansu wasu abubuwan da yawa ana arin hanasu da tunatar da su halacci da haramcin dake a tsakanin iyakar da ala arsu zata yiwu. Kuma Alhamdullah suna fahimta da kiyaye abubuwa da dama duk da bawai sun balaga bane ba. Garama shi Ajwaad alamomin hakan sun fara kusantoshi yanzu... __________________ Yanda take tura baki gaba ya sashi tsayawa yana kallonta. Sai kuma ya auke kansa ya maida ga agogon falon. Ganinfa idan ya biye mata makara