← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 104

Sashe 86

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/F7aIYP99bGn9mIqLhjUWKR GOLDEN COLLECTIONS TA TANADAR MUKU KAYAN ADO N FITA KUNYA KAMAR SU ATAMFA,LACES ABAYA SHOES AND BAGS DA KAYAN DECORATIONS D FURNITURES A FARASHI ME SAUKI __________ .........*_SU WAYE SU AMMIE?:-_* Alhaji Umar da mutane sukafi sani da Alhaji Umar Giro an asalin jihar Kebbi ne a garin Giro dake ashin Suru LG. An haifesa a babban gida da yay suna matu a a cikin garin Giro saboda kasancewarsu manyan mutane masu arfin ilimin addini. Su kusan ashirin da bakwai mahaifinsu ya haifa, maza sunfi yawa, dan mata hu u ne kawai a cikinsu, sauran su ashirin da uku duk maza ne. Malam Ibrahim shine mahaifinsu, sai iyayensu mata su uku. Ta tsakkiyar itace mahaifiyar Alhaji Umar, shi ka ai kuma ta haifa a duniya, sauran a ashirin da shida duk na matan biyu ne. Dan matarsa ta farko haihuwarta goma sha aya amma a goma sha shida duk nata ne. Sai amarya nada goma cif duk da itama dai wasu sun rasu a ciki. Kishi sosai ake zubawa a gidan Malam Ibrahim, hakan yasa ansa suka tashi da zafin an ubanci. Kowa akinsu kawai yake so. Wannan a idar tafi wahalar da Umar, dan shi ka ai shi mahaifiyarsa ta haifa shiyyasa sam baya wani jin da in zaman. Yasha wahala warai da gaske a hannun an uwansa, har takai karatun ma baya fuskanta dan anan cikin gidansu suke aukar karatu wajen mahaifinsu, an uwansa manya kuma sune gardawa a yanzu. Ganin yanda Umar in ke cikin tsangwama da yara yasa mahaifinsu aukarsa ya bama wani amininsa shima malami ne amma a can cikin birni, yanada tarin almajirai kuma Alhamdullah ana karatu. Mahaifiyarsa tasha kuka, amma hakan yafi mata kwanciyar hankali akan zamansa a gidan. Umar ya koma cikin birnin kebbi, kuma Alhamdullah yana samun ilimi, ya kuma kwantar da hankalinsa sosai dan Malam Khamisu ya saka shi cikin ansa babu banbanci. an malam Khamisu su suna karatun boko, hakan yasa shima Umar aka saka shi a boko. Zamu iya cewa Umar ya fara karatunsa cikin nasara, kasancewarsa yaro mai basira cikin anin lokaci yay zarra. Ga kuma ilimin addini shima alhmdllh. Umar na zuwa Giro akai-akai saboda mahaifiyarsa, dan haka canjin da rayuwarsa ta samu a bayyane yake ga kowa. Cigabansa na saka an uwansa sake jin tsanarsa da hassadarsa su da iyayensu, sai dai babu yanda zasuyi. A haka ya gama secondary school ya fara jami'a, yana level 2 ALLAH yay ma mahaifiyarsa rasuwa. Ya shiga tashin hankali matu a daga shi har mahaifinsu, sai dai babu yanda aka iya da hukuncin UBANGIJI. Bayan rasuwar mahaifiyarsa ya sama ransa dangana ya maida hankalinsa ga karatunsa, har ALLAH yasa ya kammala jami'a. A kuma wannan lokacin ALLAH yay ma uban ri onsa Malam Khamisu rasuwa shima. Umar ya sake shiga ru ani, dan komai ya fice masa a rai. Dan haka ya tafi yin sarvese insa nesa da Kebbi. A jihar Niger cikin garin Minna Umar ya fara Sarvese, inda anan kuma ALLAH ya ha ashi da matar aure. Lubabatu yarinya yawa mai ilimin addini da nutsuwa. Gata da ha uri da tarbiyya. Cikin anin lokaci soyayya ta ullu tsakaninta da Umar da hidimar asa ta kawosa garin Minna. Lubabatu su biyu ne a wajen mahaifinsu, daga ita dai anwarta Shamsiyya. Suma ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa matar uba ke ri onsu, suna matu ar shan wahala a hannunta. Hakan yasa Umar na nuna yana son Lubabatu mahaifinta ya bashi. Cikin anin lokaci aka gama komai, dan kafin ya gama sarvese har ranar aure an saka musu. Yana kammalawa akasha biki. Nan Giro aka kawo amarya family house insu, dan ba auren nasu ka ai akai ba harda wasu a cikin an uwansa da suma akayi duk a ranar. Sai da aka gama shan biki, bikin da aka nuna matu ar banbanci dan sam Umar baida wani gata a cikinsu, gashi itama Lubabatun duk sai a hankali tunda basu da wani gata suma sakamakon rashin uwa. Haka dai akayi biki aka gama, amare suka tare da mazajensu. Umar baya son zama a Giro, amma saboda kunyar mahaifinsa ya kasa magana. Ga aiki ya samu a Kebbi, sai ya zam dole ya koma Kebbin sai weekend yake zuwa. Sam Lubabatu bata jin da in zama a cikin wa an nan ahali, dan kishi da an ubancin da an uwansa ke nuna masa duk sai ya tattaru ya koma kanta a yanzu. Ga matan an uwansa suma sun sakata a gaba, facalanci mai muni ake zubawa a tsakaninsu. Musamman ma da Matar yayansu na biyar wanda Umar ke bimawa a wajen mahaifinsu mai suna Talle. Talle irin matan nan ne masu mugun hali da hassada da yashi, duk wani cigaba tafi son ace itace da shi. Yaranta biyu a gidan, Habibu da mace, sai aramin ciki da take laulayi. Tayi matu ar tsanar Lubabatu a gidan, dan tafisu wayewa da cigaba. Ita tayi karatun boko har zuwa secondary kuma gana addini dan tayi sauka. Suko mafi yawansu musamman ma Talle kota allon bata nutsu tayi ba sai talla. Sosai matsi yayma Lubabatu yawa, dan matan an uwan mijin nata sun ha e mata kai bisa jagorancin Talle. Koda yaushe tana a aki babu sakewa, idan kaga farin cikinta sai idan Umar na gidan. Ba kuma wai zaman nasa na hana ai mata abu bane, a'a farin cikin da yake bata a gidan ne kawai ke sau a mata ba in cikinsu. Ana haka ta samu ciki, haka taita rainonsa har lokacin haihuwa, sai dai ALLAH baiyi mai rayuwa bane wajen haihuwa ya rasu. Itama tasha wahala, wahalar data saka Umar ro on mahaifinsu aukarta su koma cikin Kebbi, dan kuwa tana na uda matan gidan babu wanda ya kulata wai ai bata gaya musu ba. Wannan yaja tasha wahala har an ma ya rasu. Sai da Malam ya shigo gidan ne yake ji a wajen yara ransa ya aci yasa aka kira wata unguwar zoma dake anan kusa da su. ari bisa ari Malam Ibrahim ya basa goyon baya. Aiko ya tattara matarsa suka wucewarsu. Wannan abu ya ba antama mutanen gidan rai sosai musamman irin su Gambo, sai dai basu da yanda zasuyi sai ha uri. Komawa Kebbi tama Lubabatu da i matu a, dan hayar gida madaidaici Umar ya kama musu. Ya kuma nema mata admission ta koma makaranta. Alhamdullah komai Lubabatu na samu yanzu, bata da wata damuwa. Ga Umar abubuwa nata zama masa. Dan ya shiga harkar kasuwanci tako ina ku i ke shigo masa. Sosai yake arin taimakama mahaifinsa dama an uwansa duk da basu ta a nuna jin da in abinda yake musu ba, sai dai Haruna mijin Talle shi da yake dama tun can yana son Umar, kasancewar sun tashi ne a tare. Matarsa ce da mahaifiyarsu da an uwansa kan canja masa tunani wasu lokutan. Amma a yanzu sai yake in biye musu suka ulle da Umar in har ya fara jan ra'ayinsa ya fara kasuwanci shima anan dai Giro in. Abinda Haruna in yayi ya ona ran matarsa da an uwansa, amma ya nuna musu shifa babu abinda Umar yay masa dan haka babu ruwansa da aukar ma kansa hakkin untata masa. Wannan abu da Harunan yayi yasaka mahaifinsu farin ciki, ya dinga saka masa albarka kuwa. Sha uwar Haruna da Umar tasa Umar in cewa Haruna ya bashi Habibu ya saka shi a makaranta, babu musu kuwa Haruna ya bashi yana faman godiya. Sai dai rigima ta arke dan Talle tace bata yarda anta ya koma hannun ma iyinta ba. Shi ko yace bata isa ba dan ya bashi kuma babu yanda zatai. Rigima tai rigima har Haruna yama Talle saki aya, ya kuma auki Habibu ya bama Umar. Sai da akaita ro onsa Talle ta ma kusa gama idda sannan ya maidota. Rayuwar Habibu ta inganta, dan Lubabatu da zuciya aya ta ri e Habibu kamar ba uwarsa ce ba ta gallaza mata. Habibu ya fara boko da islamiyya, kuma Alhmdllh yana fahimtar komai Dan yaro ne mai wazo. Yana son Lubabatu da Umar, dan yanda suke tattalin rayuwarsa har ji yake sunfi masa iyayensa, saboda Talle masifaffiyace har su an nata ba da i suke ji ba. Sai da Habibu ya kammala primary sannan ya fara zuwa Giro, dan malam ne ya saka wannan dokar saboda sanin halin uwarsa. Duk da cigaban da Habibu ya samo bai hana Talle nuna tashin hankali da son ganin anta ya dawo gareta ba. Sai dai kuma babu yanda ta iya, dan Haruna ya tabbatar mata idan tai masa hauka sauran matan hu u ma da take dasu zai kwashe ya bama su Umar ita kuma ya saketa. Wannan furuci ya tada mata da hankali dole tai shiru, amma ta koma yima Lubabatu habaici da gorin haihuwa dan ita tun wancan haihuwar bata sake ba har yanzu. Yanda take mata gorin haihuwa haka sauran matan gidan suma suka fara, sai ya zam sam kwanakin da sukai a Giro bai mata da i ba, bama su gama cika kwanakin ba tace ita dai zata koma. Ha uri malam Ibrahim ya dinga bata kamar ba surukarsa ba. Ita kuma tace ba komai baba. Haka dai suka dawo Giro harda Habibu. Ashe ALLAH mai rahama mai jin ai tana ma ale da ciki harna wata biyu. Ta raini cikinta cikin aminci da yarjewar UBANGIJI, babu kuma wanda yasan da shi sai da ya shiga wata takwas Baba Haruna yazo Kebbi ya ganta da shi. Ya taya an uwansa murna matu a, yana dawowa Giro kuwa ya fasa zance. Ashe shi Baba yasan da cikin, dan Umar ya sanar masa amma yay shiru dan ya fahimci yanda Umar yake rayuwa a cikin yan uwansa da matansa, da yanda itama matarsa ke fuskantar yara da hantara wajen surukansa. Aiko wannan batun ciki sai da ya aga musu hankali, musamman Talle, dan da farko ma saida ta jefa cikin da mummunar kalmar data saka Haruna marinta. To babu dai yanda suka iya, haka ALLAH ya sauki Lubabatu lafiya, ta haifo arta mace. Habib yafi kowa farin ciki dan ya samu anwa.
Chapter 86 · 0% Book details