Sashe 16
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
garesu ya ce, Mommy zata iya yiwuwa. Sai dai ban san a ina kika sanni ba Batare data damu da kallon harara da Daddy ke mata ba ta ce, A zaria gidan Alhaji Saminu Ashafa Cikin jinjina kai RK ya bata amsa da, anin amaryarsa ne Majdiya Kafin Hajiya Basariyya ta samu yin magana Ammie da Daddy suka dubeshi. Abinda ya faru a ranar da sukaje aurin aure gidan Alhaji Saminun ya shiga dawo mata a rai. In dai batai kuskuren fahimta ba shine yaron da Hajiya Majdiya ke mata bayanin yana son Maanal kenan. Wani irin sanyi taji a ranta, dan koba komai ita dai yaron ya shiga ranta a lokaci guda, sannan ta samu kar uwar addu'ar ta akan al'amarin Maanal in da Yazeed tunda ga raba gardama yazo.. Shikam Daddy murmushi yayi cike da nuna mamaki ya ce, Ikon ALLAH ashe ma kai in na gida ne doctor. Ai nasan Hajiya Majdiya kuwa sosai saboda Alhaji Saminu aminine kuma an uwana ta fanin mahaifiya, zan iya cemaka ma neman auren Majdiya da komai dani akayisa Wani an karen da i ne ya ratsa RK har cikin ma wallaton zuciya. Sai yake jin gaba aya matsakarsa ma shi ta are kenan. Nan take ya ara sakewa da Daddy. A karo na farko Daddy ya shiga akin da Maanal ke kwance shi da Ammie da Nene kawai. Sosai tausayin Maanal ya ara mamayesu, dan Ammie kasa daurewa tayi sai da tai kuka. Duk wanda yaga Maanal in sai yayi matu ar tausaya mata. Numfashi ma sai da taimakon na'urori take yinsa. Duk ta sake figewa. Sun mata addu'a suka fito aka bar Nene kawai dan doctor ya bu aci a an goge mata jiki a canja mata kayan jikinta. Da ance Ammie tayi amma ta nuna bazata iya ba. Sai dai Nene tayi. Tsaf Nene ta gogema Manaal jiki aka canja mata kaya. Doctor da RK suka shigo, hakan yasa Nene fita ta basu waje dan suyi aikinsu. Ta tarar da Hajiya Basariyya cike fam da takaici, wai tana fushine ita ba'ace ta shiga ta duba Maanal ba, shine taima Daddy orafi akan hakan. Shi kuma ya i tanka mata shine ta cika tai fam. Ita dai Ammie ha uri ta bata, yayinda su Amal ke mamakin abinda Hajiya Basariyyan tayi. Ita kanta Nene abin ya bata mamaki, dan bataga abin wani orafi ba a wajen tunda gasu Shahidah suma ba'a barsu sun ganta ba. Ita kanta dan Ammie tace bazata iya gogema Maanal in jiki bane aka barta ta shigan. A haka Yazeed da yaje Kaduna ya dawo ya samesu, tare da duk yaran gidan yake tafe, amma abin mamaki yau in ma Hajiya Yaya bata zo ba.... Da mamaki Amrah ke kallon RK, har dai ta kasa ha uri sai da tayi magana. Murmushi yay mata da tambayarta ya gajiyar biki. Hakan data faru tsakanin Amrah da RK sai ya tsayama Yazeed a zuciya har sai da ya kira Amrah in gefe ya binciketa. Kanta tsaye ta sanar masa abinda ta sani. Yayi mamaki warai da gaske. Haba no wonder yake mamakin yanda RK in ke tsaye very serious akan case in Manaal in. Ya jima yana son ha a al'amarin a ransa amma ya gaza samun makama, tunda shi dai sun fitone kawai suka samu motar RK in a ofar gida, daga wannan taimakon kuma na kawosu asibiti baiyi tunanin cigaba da ganinsa ba amma sai yaga ya tsaya tsayin daka komai anayi da shi, yayi tunanin kawai tausayi da taimakone sai da aka dawo Abujar nan ya an fara zargi a ransa sai kuma dai yay saurin kaudawa tunda bashi da tabbas musamman ganin RK in matsayin likita shima. Ashe kuwa hakanne. A ranar su Amrah suka koma Kaduna harda Hajiya Basariyya data wuce bisa tirsasawar Daddy dan kuwa badan taso ba, taso ace sai taga kwal uwar daka. Ta zata da Daddyn zasu tafi sai yace mata shi yana nan har sai yaga yanda hali yayi akan jikin Maanal in. Hakan ya masifar ona mata rai, dan ta kalla abunne a sigar rainin hankali irin na maza kawai. A ganinta Daddyn nason holewa da Ammie ne a wannan ayataccen gida shine ya fake da ciwon agola. Ita Ammie tsaf ta fahimci manufar Hajiya Basariyya in, amma sai ta basar kawai tama dinga arfafa Daddy in akan yaje suma suna da hakki a kansa, tunda dai Maanal in tana samun dukkan kulawa anan in gasu kuma ga Yazeed shi yaje ya huta gashi ya dawo daga tafiya. Sam Daddy in saurararta yayi, daga arshe ma ya fara fushi da ita dole tai shiru ta zuba masa ido kawai su Hajiya Basariyyan suka wuce... angaren Yazeed kuwa ya fara janye jikinsa daga RK. Tun RK in bai fara fahimta ba har ya fahimta. Dan sai wani isa ma Yazeed ke nuna masa akan Maanal in yanzu da gadara. Mamaki hakan ya bama RK, dan shi a zatonsa Yazeed da Maanal uwa aya uba suke ko uba aya dan yana an tantamar Ammie ta isa haihuwar kamar Yazeed in. Bai daiyi magana ba yabar abin a ransa dan ganin iya gudun ruwan Yazeed in. Ana cikin wannan dambarwa a tsakaninsu Hajiya Majdiya yayarsa tazo duba Maanal ita da yaranta tun daga Zaria. Dan shine ya kirata yake sanar mata, aiko baiwar ALLAH sai gata tazo. Ammie tayi mamakin hakan kasancewar batai waya da Hajiya Majdiya in ba akan hakan. Sai Hajiya Majdiyan ke sanar mata, Sirikinki ne ya kirani yake sanar min ai. Murmushi Ammie tai da fa in, Haba nayi mamaki fa, sai kuma hankalina bai kawo nan in ba. Ai babu abinda zamuce da Rafeeq sai fatan alkairi. ALLAH yay masa albarka Amin ya rabbi. Yaya jikin nata yanzu? Dan naga hankalinsa a tashe yake matu a yau har cewa yay na nema masa masu saukar Alkur'ani yana son ai mata Ajiyar zuciya Ammie ta sauke. Zuciyarta na sake jin nutsuwa da RK in. ALLAH sarki, ALLAH ya saka masa da alkairi. To Alhamdullahi zamu ce. Sai dai har yanzu bata san wanda ke kanta ba. Amma dai suna tabbatar mana bugun zuciyarta na dai-daita zuwa yanzu. Kowane lokaci kuma zata iya farfa owa cikin hayyacinta. ALLAH ya bata lafiya, yasa ya zama kaffara. Abin tausayi yarinya arama haka da wannan irin babban ciwo mai ha arin gaske, ALLAH ka bamu ikon cinye jarabawoyinmu. Shiyyasa gata nan sanyi-sanyi ko kuzarin kirki bata da shi. Ban ta a sanin tana da wannan lalurarba ai da tuni na ha aku da Rafeeq in dan aikinsa ne. Yanzu haka reshen wannan asibitin suka bu e acan garin jos shine yaje can da kansa yake ri e da asibitin kusan shekara aya kenan, anan ne ma ALLAH ya ha asa da ita Murmushi Ammie tayi tare da jera addu'a ma RK in. Ganin yanda Ammie ta auki zancen da muhimmanci Hajiya Majdiya ta cigaba dama an uwanta campaign wajen Ammie. Yinin gaba aya suna a tare sai bayan Magrib RK ya aukesu ya maida can gidan babbar yayarsu dake nan Abujan zasu kwana anan dan sai gobe idan ALLAH ya kaimu zasu koma Zaria. Sosai Ammie taji da in kasancewa da Hajiya Majdiya a wannan rana. Dan zaman ya sake tasirantar da abinda take ji a zuciyarta game da RK da Maanal idan har ALLAH ya tashi kafa unta. Bata oyema Nene da su Shahidah ba akan ala ar Dr Rafeeq in da Maanal. Suma sai abin yay musu da i matu a, dan suna ganin idan har ALLAH ya baiwa Maanal lafiya wannan itace hanya mafi sau i da maganar Yazeed zata janye cikin sau i batare da sun ata ran Daddy ba kamar yanda duk suke gudu. Dan gwara dai a ha ura da batun Yazeed in nan haka nan tunda dama ita wadda ake dan ita bawai tana sonsa bane. Abu na biyu sudai a haka yanayin Dr RK ya musu hundred percent, dan mutum ne mai sau in kai ga girmama na gaba da shi, ga yanda yake awainiya dasu a asibitin nan cike da mutuntawa ma abin a soshi ne. Shi kansa Daddyn sun fahimci RK in ya shiga ransa. Sai dai babbar matsalar sun san ga Yazeed za'a sameta kam. Dan kowa yasan Yazeed na matu ar son Maanal wannan a bayyane yake. Sannan shi kansa mutumin kirki ne, dan yana da nagartattun halaye masu yawan gaske daya gada ga Daddy, tako ina Yazeed ya cancanci zama mijin Maanal kodan halaccinsa garesu, dan hatta Daddy ya sansu ne a dalilin Yazeed. Sannan kodan Daddy a bama Yazeed auren Maanal, mahaifiyarsa ce kawai matsalar gaskiya, dan Hajiya Yaya sam ba kanwar lasa bace. Bata da kirki ko mis ala zarratin, kanta kawai ta sani, kuma tabbas zata iya aikata komai akan wannan auren kamar yanda take shan fa a idan har akayisa. ALLAH dai ya bama Maanal in lafiya, zasu cigaba da tayata addu'ar za in alkairi dan duk MAZAJE biyun nan sun matu ar cancanta da aurenta... A mota Hajiya Majdiya ke bama RK labarin hirarrakinsu da Ammie, babu abinda yake sai murmushi da ara jin aunar ar uwar tasa. Sai da ta gama bashi labari tsaf sannan ya jeho mata tambayar abinda ke cimasa zuciya.. Humm Aunty Alhamdullah na samu kar uwa wajen Ammie da an uwan Maanal, sai dai ba duka ba Kamar ya ba duka ba miye matsalar to? Yazeed Aunty, Yazeed shine matsalar kuma na fahimci yana da arfin fa a aji akan an uwan nasa. Da farko dai ni da shi normal gaskiya. Amma kwana biyun nan ban san miyyasa ba ko ya fahimci ala ata da Maanal in sai naga yana jajja baya dani, sannan yana min gadara da al'amarin Maanal in. Dan ma baida yanda zaiyi ne kasancewata aya daga cikin likitocinta shiyyasa. Har abin ya fara bani mamaki dan kamar wani mai kishi da ni. Sai dai nasan ba hakan bane tunda mizai sakashi yin kishi akan wadda suke Uba aya ne ko uwa aya ma ban sani ba . Ya are maganar cikin damuwa sosai. Fuskar Hajiya Majdiya cike da damuwa itama ta furta, To kodai Yazeed ma son Maanal yake? What?!!! RK ya fa a a an razane yana taka birki da sauri.........