← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 104

Sashe 88

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da firgici Gwaggo tace ai ciki bana Habib bane tunda ba kwana yake a akin ba, dama ai Shahidah ma ba arsa bace. Magana kamar wasa ta nema zama babba. Dan har gari ya auki wannan zance. ALLAH gafurin rahimun sai ga Baba Haruna ya dawo hankalinsa a lokacin, dan kuwa asirin Gwaggo ya sakesa. Shine ya bama Asiya kariya har ya sake yina Gwaggo saki aya. Ya rage saura igiya aya a tsakaninsu kenan. Wannan saki shine fa ya sake haddasa wutar iyayya tsakanin Gwaggo da Ammie. Da yar dai Mahaifiyar Baba Haruna tasa ya dawo da Gwaggon dan anwarta ce dama auren zumunci akai musu. Gwaggo ta dawo amma ta ara ninka iyayyarta ga Ammie, sai dai a yanzu Baba Haruna na tsaye akan al'amarin Asiyar, dan ya ma fara shirin Asiya tabar giro tabi mijinta. Amma sai ta haihu kodan yanayin samun cikin. Haka Asiya taita rainon ciki cikin matsi da takurar surukarta. Ga Shahidah dake ta fama da ciwo. Babu mai taimaka mata a gidan har tsoffin gidan saboda Gwaggo ta zama boss ga kowa. ALLAH ya sauki Asiya lafiya ta sake samun mace mai kama da ita itama kamar Shahidah. Aiko Gwaggo ma ta sake aibanta jinjira tace ba iyar Habib bace. Sai da Baba Haruna yay mata tas. Baba Haruna shine ya tsaya akan komai akai suna yarinya taci suna Lubabatu, amma sai suke kiranta Amaal koma ace Asiya da Habib ke kiranta. Dan su dai an gidan Lubabatu suke cewa. Zuwa lokacin an ma Habib transfer zuwa Maiduguri. Dan haka ana gama bikin suna ya sake shirya komawa. Sai Baba Haruna yace ya auki matarsa su tafi. Hankalin Gwaggo ya tashi akan hakan amma Baba Haruna yace bata isa ba kuwa Habib kamar ya tafi da iyalinsa ya gama. Hakan yama Habib da i, ya auka Asiya da yaransa biyu suka wuce abinsu, suka bar Gwaggo na tujara. Wannan tafiya ita ce ta samawa Ammie sau i, suka koma Maiduguri da zama ta samu damar rainon yaranta cikin aminci, anan ta koya gyaran jiki da ha in turarruka. Shekararsu biyu a Maiduguri aka sake masa transfer zuwa jihar Nasarawa. Nan ma ya kwashesu suka koma. Anan in ma shekararsu uku aka sake maida shi Sokoto, zuwa lokacin kuma bata sake haihuwa ba. Yaransu Shahidah da Amaal sunyi yau abinsu yara kamar ka lashe, dan Ammie ma yawa ce kamar mahaifiyarta. Dole kaga yaran nan sai ka tanka, dan kamar wasu iyan hamsha in mai ku i bana an sanda mai aramin mu ami ba. Shima Habib yana son yaransa, sai dai irin mutanen nan ne shi da bai cika jan yaro a jiki ba, komai dai na bu atar rayuwa yana tsaye a kansu. Dan ko ita Ammie bazata ce ga wata soyayya a bayyane da yake nuna mata ba. Baya dai takura rayuwarta ko hanata duk abinda take so, ba kuma ya nuna mata tsantsar soyayya a zahirance. Ga wanda ma bai sansu da yau ba idan yaga rayuwar zamansu sai ya auka tana a cikin matsin rayuwa ne. Sun tattaro sun dawo Sokoto, a lokacin Shahida nada shekara bakwai, Amaal nada shekara biyar da wasu watanni dan tsiransu da Shahidah ka anne. Saida sukai sati biyu a Sokoto sannan suka je Giro. Babu wanda bai firgita da canjawar Asiya da yaranta ba. Dan ta koma ar gayunta kamar batai rayuwar Giro ba. Tuni kishinta da hassada ya shiga zukatan jama'ar gidan kamar yanda suka dingama mahaifiyarta Lubabatu. angaren Gwaggo ma babu abinda ya canja, dan iyayyar Asiya sai wacce tai gaba. Haka su Shahidah ko kallo basu isheta ba dan tace ita ba jikokinta bane ba uwarsu dai tasan inda ta samo su. Hakan na ma Habib ciwo amma baya cewa komai. A wannan zuwa kuma Gwaggo ta tsira sai Habib ya ara aure, dan a haifa masa namiji. Kai tsaye ya nuna mata bashi da wannan arfin, dan shi dai bamai ku i bane, dukiyar da yake juyawa kuwa kowa yasan ta Asiya ce da iyayenta suka bar mata duk da ma dangin nasu sun kusa cinye rabi da kwata. Aiko ta tujaresa da masifa da bala'in daya sashi tattara matarsa da ansa suka koma abinsu. Sai kuma suna komawar sai ga Asiya da ciki. Yayi farin ciki matu a, ya kuma shiga addu'a da fatan ALLAH yasa Asiya ta haifa namiji dan shima fa yana son a haifa masa namijin, ga maganar mahaifiyarsa ta sake kwa aita masa abun a rai. Kawai dan bashi da arfin aure ne. Amma tabbas a ransa yana son ara auren ma. Dan yana an neman mata batare da Asiya ta sani ba, tun kafin yay aure yake yi, bayan aurensu ya rage sosai sai dai kuma ita dama zina masifa ce. Faratane mara wuya, amma indai ka fara sai ALLAH ya soka da rahama kake dainawa. Ammie tayi rainon cikinta cikin aminci da kulawa, har ALLAH ya kai cikin watan haihuwa ta haihu lafiya. Ta samu a mace ma a wannan karon. Sai da Habib yaji wani iri a ransa, sai dai kuma yana aura idonsa akan yarinya yaji aunarta ta shigesa. Dan ita kam tayo kamannin mahaifiyarta da an uwansa, ta kuma yo kammaninsa ta bangarori da dama da suke a bayyane........ ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ .........Wannan karon ma dai Giro suka koma suna, sai dai babu wanda ya nuna murna da wannan haihuwa kamar ta Amaal daga Baba Haruna sai uban jegon sai kuma su Shahidah dake murna an haifa musu anwa. Wannan karon dai Gwaggo babu damar aibanta yarinya tunda tana kama da ubanta a abubuwa da dama. Amma hakan bai hana sako batun haihuwar a namiji ba data fahimci yana tasiri a zuciyar an nata. Haka dai akai bikin sunan babu wani armashi sosai sukai shirin komawa Sokoto amma sai Gwaggo ta hana wai su zauna anan suyi wankan jego. Ganin yanda bata kawo tashin hankali ba a sunan yada baba Haruna tunanin ta sauya ne. Dan yanzu ta an rage wasu abubuwan a zahirance saboda tsoron kada ta tsinke ar sauran igiyar aya dake a tsakaninsu. Ta koma zuba rashin mutuncinta ta asa, dan Habib ta koma takuramawa akan sai ya ara aure, ita kuma Asiya ana mata a kaikaice. Shima dai Habib wannan karon bai damu ba ya barsu anan ya kuma yarda da batun ara aure, dan ya samu damar she e ayarsa da sabuwar karuwarsa da suka ha u anan Sokoto in kwanan nan. Zama kamar wasa ya nema zama gaske. Dan bayan gama wankan jegon Maanal Habib bashi da niyyar cewa su shirya komawa Sokoto, sai dai yana zuwa duk arshen wata yay musu weekend ya koma. A haka aka tado batun aurensa. Auren daya bama kowa mamaki ya kuma saka Ammie a tashin hankali. Amma sai Baba Haruna ya dinga kwantar mata da hankali da nasiha ta sakama kanta dangana kuwa ta rungumi anta. Cikin anin lokaci akasha biki kuwa, yarinya arama da bata wuce shekara sha bakwai ba. Inda Ammie ta burge kowa shine tattara komai ta watsar kamar ma ba ita akama kishiyar ba. Sai shima kansa Habib in ya dinga kiyaye duk wani abu da zai ta a mata zuciya ba kamar yanda Gwaggo taso ba. Itama yarinya da aka oro akan rashin kunya da zata dinga yima Ammie sai ta dinga jin shakkarta. Abinda ya ragema amarya armashi samunta ba'a cikakkiyar mace da Habib yayi ba, dan tun a daren farko sai da tasha maruka a wajensa a aki batare da sanin kowa ba. Ko sati kuma bai cika ba na amarci ya tattara ya koma wajen aiki. Aiko akaita gutsiri tsoma wai Ammie ce tayi wani abu, dan Gwaggo har aki ta sameta ta mata wankin babban bargo. Ita dai batace komai ba. Habib bai zo gida ba sai da yay wata guda kamar yanda ya saba, ya kuma murje idonsa ya sauka akin Ammie, itako tanata ro onsa bai kulata ba, ana cikin haka sai ga Gwaggo har aki, tas taima Ammie da zaginta akan muna fuka ta tasa anta gaba har akin amarya Sailu. Ai ko ranar ma maimakon ta samu kulawa a wajensa sai duka taci a banza, dan ya fahimci bata da kunya, Habib kuwa irin mazan nan ne da basa aukar raini, shi hatta macen bariki tai masa hauka duka take ci a wajensa, Ammie ce ka ai ta tsira da irin wannan halin nasa, duk da yana shan marinta itama a wasu lokutan. To ata aice dai wannan aure bai rufa wata biyar ba a wani zuwa ya saki Sailuba saki har uku. Nan fa gari ta auka Ammie ce ta koreta. Babu kalar abunda Ammie bata gani ba akan wannan rabuwar auren amarya da mijinta, an gidan suka kara tsananta, na Gwaggo kam ai ba'a magana. Ga Habib bashi da niyyar cewa su shirya subar garin har sai da Maanal ta shiga shekara aya da rabi sannan akaima Habib transfer zuwa Kano. Aiko Baba Haruna da'a yanzu ya fahimci Habib na neman matan banza yace ya tattara matarsa da iyalansa su wuce tare. Gwaggo ta nuna bata yarda ba, Baba Haruna ya nuna mata shima bata isa ba. Kamar Habib baya so haka ya wuce da su Ammie Kano, dan yasan an rage masa jin da insa ne kawai. Anan ya samu gida ya kama musu haya, daga baya kuma ya saye shi da ku in Ammie na gado, shine dalilin komawarsu da zama garin Kano. Tunda suka koma kuma basu sake zuwa Giro ba sai dai shi yazo sau uku sai yanzu shekara kusan shidda kenan dan tun Maanal nada shekara aya da wasu watanni da
Chapter 88 · 0% Book details