Sashe 95
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 9:48 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ .........Alhamdullah bayan dogon zaman jira da fargaba da kasancewa a tashin hankali an samu nasarar ciro yara an biyu a jikin Fateema duk maza. Sai dai aya bashi da rai, rabin jikinsa ma har ya an fara ru ewa. Wannan yanayi ya saka farin ciki da alhini a wannan zuri'a duk a lokaci guda. Sai babbar damuwarsu sanin halin da Fateema ke a ciki kuma. Dan Doctors in dai since su basu lokaci. Haka suka sake koma a yanayin damuwa da taraddadi musamman ga Aliyu har zuwa washe garin safiyar ranar. Dan wajen arshe sha biyu aka samu nasarar farfa owar Fateema. Dama wannan shine tsaikon da likitocin suka samu na zahiri. Zuwa yanzu kam kowa ya warware, farin cikin kowa ya fito a bayyane, anatama juna barga da addu'a ga jaririn da ya rage, wanda ma bai zo da ran ba ana masa addu'a..... Watan Fateema aya cif a asibiti aka sallesu, jikinta da sau i sosai, sai dai yanayin cs na wancan lokacin ba dai-dai yake dana yanzu na zamani ba. Sai ya kasance wasu tsarabe-tsarabe kan biyo baya da har mutum kan iya aukar dogon lokaci yana mafa da jiyya sama-sama har komai ya zama normal. Zuwa lokacin tuni an ra a sunan jariri da aka barsa da sunansa wato Hussain. Dan Hassan inne baizo da rai ba kasancewar shi aka fara cirowa. Ra in suna kawai akai, sai bayan sallama aka shirya taron suna. Ansha shagalin kam mai birgewa da nunama tsara, sai dai maijego na dauriyane kawai dan sam bata jinta cikin isashiyar lafiya har lokacin. Sai dai bata son agama mijinta da an uwanta da iyayenta hankali, shiyyasa ta cigaba da daurewa har taro ya tashi lafiya ta cigaba da wankan jegon da Umma ke mata da kanta. Wato matar baba Sardauna. Sun gama wankan jego lafiya, dan kusan ma arba'in biyu sukayi, ta an zaga dangi harda Saudiya ita da Aliyu sukayo sati uku sannan suka dawo. Abin addara satinsu biyu da dawowa Hussain ya fara wata mura mai ban tausayi, murar fa ko numfashinsa da yar yake fisga. Hankali tashe suka wuce asibiti da yaron, sai dai UBANGIJI shi mai hikima ne, a daren shima yabi an uwansa. Kuka rurus Aliyu ya dinga yi, amma a mamakin kowa Fateema ko igon hawaye, sai ma ta koma itace ke lallashin mijin nata kuma an uwanta. Bayan rasuwar Hussain da kusan wata biyar sai ga Fateema ta fara laulayin sabon ciki. Murna a wajen Aliyu ba'a magana ko kwatantawa. Hakama sauran ahalinsu kowa na fatan alkairi da addu'ar ALLAH ya inganta. Sosai wannan ciki yazo ma Fateema da tsanani fiye dana an biyu, dan bata sati guda a gida sai a asibiti, arshe dai suka ri eta a asibitin domin samun bedrest. Dan haka kawai saita dinga bleeding, doctors sunyi iya arin ganin sun shawo kan matsalar amma al'amarin ya gagara, har takai mahaifin ta dake matsayin babban likita a saudia wato Kasheem Kura ya nufo Nigeria da kansa. Shine ya tsaya akan matsalar, inda ya fahimci ar tasa tana fuskantar babbar addarane mai girma. Ya shiga tashin hankali amma haka ya daure ya jure ya fito fili yama uban ri onta da uwar ri on ta da mijinta bayani akan dole ne fa a raba Fateema da wannan ciki, dan sam mahaifarta bazata iya ri eshi ba. Hasalima sai an rabata da mahaifar kanta sakamakon ciwo mai ha ari data kamu dashi, in ba hakaba kuma ciwon zai fara girma wataran a wayi gari ya harbi dukkan illahirin jikinta. Amma idan sunyi arin cirewa yanzu in sha ALLAHU an rabu kenan. Wannan al'amari ya matu agama kowa hankali, musamman ma Aliyu. Amma lafiyar matarsa tafi masa duniya da abinda ke cikinta. Dan haka babu wani ja'inja ya amsama Abbu cewar kawai a cire in. Haka kuwa akayi, aka cirema Fateema cikin da dama bai wani zauna da yau ba, aka kuma cire mata mahaifa. Wannan shine ya kawo mata sanadin yin doguwar jinya ta kusan watanni takwas, kafin ALLAH ya bata lafiya komai ya daidaita tamkar ma ba'a ta a yi ba. Har kuma lokacin bata ta a sanin an cire mata mahaifa ba. Bayan samun lafiyarta abu na farko shine nema mata gurbin shiga jami'a da Baba Sardauna yayi ana BUK. Dan danan kuwa ta fara karatunta. Dan Fateema yarinya ce mai haza a matu a da son karatu. A randa ta fara shiga makarantar aukar darasi a ranar suka fara ha uwa da matashiyar budurwa da bazata wuce sa'arta ba, in ma ta girmeta baifi da shekaru uku zuwa hu u ba. Kamila Shu'aibu yawar yarinya, ba ace amma ba inta mai yau ne. Tana da matu ar sanyin hali da rashin son yawan magana. Wajen zama ya fara ha a su da Fateema a ranar farko, Fateeman ce kuma ta samu Kalima. Bayan ta mata sallama fuskarta da murmushi tai nuni da kusa da ita tana fa in, Sis... Kozan iya zama? Murmushi mai sanyi Kamila tai mata itama, tare da nuna mata wajen ta ce, Bismillah mana ki zauna Murmushi Fateeman ta sake mata sannan takai zaune da fa in, Thanks you . Daga haka babu wanda ya sake shiga sabgar an uwansa suka maida hankalinsu ga malamin. Tun daga wannan ranar sai ya zam duk wanda ya riga wani zuwa a cikinsu sai ya tanadarma an uwansa waje a kusa da shi. Tun abin na musu kamar wasa har sha uwa ta fara tasiri a tsakaninsu. Sai dai babu wanda yasan komai daga rayuwar an uwansa, karatun kawai suke yi har tsawon watanni. A hutun farko da suka farayi har aka dawo akaci kusan sati biyu babu Kamila, hankalin Fateema ya fara tashi ta fara bincike a wajen an ajinsu, sai dai kowa kance shi bai san inda Kamila take ba ba tare ake ganinsu ba. Kamar wasa Kamila ta shafe watanni har biyu bata dawo school ba. Har Aliyu ya fahimci matsalar Fateema ya tambaye ta. Bata oye masa komai ba ta sanar masa, shiko dama yasan labarin Kamila a wajenta tun farko. Haka domin farin cikinta yazo har makarantar ya tayata bincike har ALLAH yasa suka samu wanda yasan gidan su Kamila in. Shine yay musu rakkiya. Sosai Kamila ta shiga matu ar mamaki tare da jin aunar Fateema a ranta. Suka rungume juna suna kuka. Aliyu ne ya shiga basu baki, inda sai a lokacin Kamila ta ganshi. Mutuwar tsaye tayi dan lallai bawan ALLAHn ya ha u, ya kuma daki zuciyarta da nashi tsarin, amma sai ta danne. Da farko tayi zaton yayan Fateema ne kawai saboda tsananin kamanni da sukayi, dan haka ta gaisheshi da girmamawa da kiransa da sunan Yaya. Shima ya amsa mata kadaran kadahan dan babu wata mace dake birge Aliyu sai Fateemansa. Hatta sauran yara matan family insu sam baya sakar musu fuska. Anan soro aka masa shimfi a, su kuma suka shiga daga ciki. Su Kamila talakawane sosai, sannan tana rayuwane a hannun kakarta Iyale. Ashe ciwone ya kwantar da Iyalen ita kuma Kamilar ke jiyyarta shiyyasa bata koma makaranta ba. Ta wani gefen kuma babu ku in da zataje tai bu atun makarantar ma. Dan mahaifinsu ka ai Iyale ta haifa, su uku kuma suka haifa duk mata. Mahaifiyarsu ta rabu da babansu tuni saboda tsananin rayuwar talauci da suke a ciki. Yayi yun urin wacesu a hannunta amma sai ALLAH ya bata nasarar guduwa da yayarta da anwarta. Ita kuma a lokacin tana hannun Iyale dan tun yaye dama take anan. To a yanzu hakan dai ance Maman nasu na Saudia tana tukari, suma an uwanta biyu na'a tare da ita. Babansu na son karatu shiyyasa ya tsaya mata cewar zatayi, dan baya son nan gaba an uwanta dake a wajen mahaifiyarta su fita cigaban rayuwa. To da yar da ya ALLAHU aka ha a ku in makarantar ta fara saboda takardunta sunyi yau, sai kuma gashi tunkan aje ko'ina karatun na neman fara tangal-tangal, dama Sakandire in ma dayaya aka gama, mahaifiyarta ce ke turo ku an tsakanin nan kuma ta auke musu wuta saboda ro on da Iyale ke mata akan ta dawo garesu kodan an dake tsakani. Zuwan Fateema da Aliyu gidan shine ya zamewa Kamila rahama da tarin alkairi, dan ka an daga tarihinta da Fateema taji ya aga mata hankali, suna dawowa gida ta sanarma Aliyu komai tare da ro onsa ya taimakawa Kamila ta koma makaranta. Baiyi musu ba kuwa ya taimaka da iya nasa arfi Baba Sardauna ya arasa sauran shi kuma. Hakan ya zama sanadin komawar Kamila makaranta, aka kai Iyale asibiti, aka kuma bama mahaifinta jari ya fara sana'a tare da tsaya masa ya ara aure. Wannan hidima mai ban mamaki daga ahalin Fateema shine ya sake dun ule Fateema da Kamila waje aya, wadda zuwa yanzu ta fahimci Aliyu mijin Fateema ne Kuma yan uwane na jini. Tayi kuka sosai dan harga ALLAH Aliyu ya shiga ranta sosai, amma ta dannema zuciyarta tare da arin ciresa a ranta duk da tasan abu ne mai matu ar wahala. Haka wannan abota ta cigaba da tafiya, sha uwa da zumunta mai arfi na ara tasiri a tsakanin Kamila da Fateema. Har takai Kamila kanzo gidan Sardauna tai kwanaki a wajen Fateema. Babu wanda ya ta yamatarta ko yararta balle kallon banza. yautata mata suke da iya iyawarsu har ma da iyayenta. Suna da shekara biyu sun shiga farkon ta uku a jami'a hankalin Fateema ya fara tashi da ganin bata sake samun ciki ba. Ta fara takurama Aliyu suje asibiti amma sai yay biris da ita. Ta cigaba da masa naci daga arshe yace babu inda zaije. Haihuwa ta ALLAH ce kuma lokaci ce. Idan sukai hakuri lokaci yayi zai basu. Shi ba haihuwar yake so ba ita yake so. Sam kalamansa basu