Sashe 47
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baby anya kinyi murna da dawowata kuwa? RK dake kallon Maanal cikin wani yanayi ya fa a murya a raunane. Karo na farko ta an dubesa, sai kuma tai murmushi da bata cika yi ba. Shi kansa saida ya lumshe idanu saboda yanda murmushin nata ya wani ratsa masa zuciya. Idanunta ta an janye daga kallonsa ganin yanda yake wani ance nasa idanun. Daga dawowa zaka fara rigimar taka ko . Ta fa asa- asa batare da tunanin zai jita ba. Amma a mamakinta sai taji ya saki aramar dariya da fa in, Oh ashe kallon rigimamme ake min ni Rafeeq Murmushi kawai ta sake yi batace komai ba. Shima sai ya tada motar suka fice a kamfanin. Sun an yi nisa da tafiyar yanata mata labarin inda yaje. Ita dai bata cewa komai shi kuma bai damu ba. Sai da suna gab da shiga anguwar su Shahidah tace masa, Yaya jikin Aunty kuwa? Ka i dai bani address in naje na dubata Ayya! Amin afuwa gimbiya. Kin san tafiyar nan ce da babu shiri kawai ta kawo tsaikon. Amma idan babu damuwa gobe idan ALLAH ya kaimu dai ki shirya nazo muje bayan sallar magrib an jimm tai sai kuma ta ce, Okay ALLAH ya kaimu, zan dai fara sanarma Didi yanda tace Ba damuwa hakan ma yayi . Ya are maganar dai-dai yana horn a ofar gate in. Da sauri maigadi ya wangale ofar bayan ya le o yaga shine. Sun saba sosai saboda RK akwai sau in kai ga yauta, da wannan halayen nasa yake saurin saye zuciyar mutane da yawa. Mutum ne mai sau in kai matu a, da wahala ka zauna da shi bai shiga ranka a lokaci aya ba. Sai da ya gama dai-daita parking idanun Maanal suka sauka akan motar Yazeed. Motar ta zubama idanu na tsayin sakanni, sai kuma ta bu e ta fito. Shima RK in fitowar yayi hannunsa auke da ledar da bata san da ita ba, sai lunch box inta daya ha a ya akko. Ganin inda take kallo shima sai ya kalla wajen, a take fara'ar fuskarsa ta canja, har zai mi a mata kayan dan baida niyyar shiga ciki amma sai ya fasa. Cike da basarwa yace mata, Muje Kallonsa tayi, sai ya auke kansa. Baki ta bu e kamar zatai magana amma sai ta fasa, dan ta tabbatar sai ya shiga in tunda yaga Yazeed in na ciki. Ita kam bata san yaya zatai da wannan mutanen ba an rigima. A tare suka shiga falon tana gaba yana biye, Yazeed kuwa na zaune tare da su Barrah kasancewar yau babu islamiyya alhamis ce. Tunda ta shigo shima idonsa kyam a kanta, sai dai yana ganin RK ya tsuke fuska. Jitai kamar ta fasa ihu, amma ta daure dai ta arasa, sannu da zuwa tai masa tare da gaishesa. Shima RK sai ya mi a masa hannu a age. Shima Yazeed in a agen ya bashi nashin suka gaisa sama-sama. Daga haka RK ya kai zaune yana janye ra'ayin su Haneeff. Shi kuma Yazeed sai ya maida hankali ga Maanal duk da dai yanzu babu fara'ar data shigo ta an gani a fuskarsa. Dama dai can shima in kamar ita ne ba gwanin fara'a bane ba. Magana Yazeed in ke mata asa- asa tana bashi amsa cikin yanayinta na rashin son magana. Yanda RK ya maida hankalinsa akan shirmen su Barrah sai ka auka bai damu dasu ba, sai dai gaba aya kunnesa da hankalinsa na akansu. A haka Shahidah tai sallama ta shigo falon. Wata irin ajiyar zuciya Maanal ta saki acan asan ma oshi, kamar an saita sai ga Huznah itama ta shigo, sai dai ita tana cin karon da Yazeed tayi wani turus na an firgici, shima in kallonta yake da mamaki. Cikin ari- ari ta gaida shi gefe kuma tana satar kallon RK da tunda yay mata kallo aya ya auke idanunsa ya maida ga Maanal. Amsa mata Yazeed in yay da fa in, Ke daga ina haka? Yaushe kika zo Abuja? Daburcewa Huznah tayi, dan duk fitsararsu suna tsoron Yazeed kasancewar baya aukar raini dukansu uban kowa yake ci a gidan. Cikin an sar ewar murya ta bu e baki zata masa bayani Shahidah ta tari numfashinta. Ayya yaya Yazeed zumunci tazo yi mana. Jiya ta iso zata mana hutu ne Shahidahn ya kalla kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Da wannan Huznah ta samu ta gudu aki cikin sassarfa. Maanal nason shigewa ta an watsa ruwa babu dama, sunzo sun sakata tsakkiya. Haka dole ta ha ura har ALLAH yay balling ta akai kiran sallar magriba sannan suka mi e dan zuwa massalaci. RK dai ya mata sallama alamar bazai dawo ba. Amma Yazeed baice komai ba, hakan ba nufin shi yana nan kenan. Sanda ta shiga aki baje-baje ta iske Huznah a gado tana waya. Sai yala dariya takeyi. Komai Maanal batace da ita ba ta wuce bathroom. Daga cikine take an jiyo hirar Huznah Ai ki bari kawai guy in nan arshe ne. Ga yau, ga aji, ga ku i ga iya wanka. Kin san ALLAH yau jinai kamar na rungumesa. Dariya ta yale da shi alamar ana magana daga can, caraf ta cigaba da fa in, Ai gara kam kuyi sauri ku kaini kada naja muku abin kunya a gari, wlhy har gida yasa aka kawoni a wata azababbiyar motarsa. Wa ai gobe ma komawa zanyi dan ya tabbatar da arfina na shigo Kai kawai Maanal ta girgiza da ta e baki, sai ma ta auke hankalinta daga sauraren zantukan shirmen. Ita dama tasan ba banza ta kawo Huznah Abuja ba, ashe kuwa namiji ta biyo. Kai wannan abun kunya dame yay kama mtsoww!. __________ Washe gari sai ga Yazeed wai yazo kaita office da kansa. Rasama abin cewa Maanal tayi, tadai cigaba da cusa breakfast in da Shahidah ta tsareta yi saboda shan magani. A haka yazo ya samesu. Ta gama shan maganin tana tattara kayanta sai ga maigadi yazo yana sanar mata ga RK yazo, wai ya kira wayarta switch off. Gaba aya sai Maanal ma ta kasa motsi, idanunta cike da walla ta kai dubanta ga Shahidah da abin yama fara bata dariya. Dan ita kam Yazeed da RK in yanzu dariya al'amarin nasu ke bata. Kowanne baya iya oye kishinsa akan Maanal. Ta wani gefen kuma tausayi suke bata su duka ukun ma. Inda Yazeed yake Shahidah ta juya, sai ta samu wayam alamar ya fita. Tofa, shi kuma Ya Yazeed yaushe ya fita Da sauri Maanal ta juya inda Yazeed in yake, itama ganin wajen empty sai ta an waro idanunta tare da maida kallonta ga Shahidah. Didi ina kuma yaje? Wajen abokin takararsa mana. Ai wannan samari naki Maanal na kula kowanne da zafinsa yake. ALLAH dai yasa a rabu lafiya kawai. Kinga muje kawai ni na saukeki da kaina sai a raba rigimar. Ya kamata ma su duka ki hutar dasu zuwa kaiki da akkokin nan dan na fahimci abin yana neman aukar wata hanya ne a tsakaninsu Koda suka fito sun samu rayukan Yazeed da RK in duk a ace, kallo aya Maanal tai musu ta wuce ga motar Shahidah tai shigewarta. Sai ita Shahidahn ce ta arasa wajensu. Maanal bata san mi yayar tata ta sanar musu ba, koda ta dawo motar kuma batai mata bayani ba ta tayar suka fice. Haka ta kasance a office babu wani walwala a tare da ita. Dan fuskarta tafi kowacce rana kasancewa a tsuke. Yau ma anyi zama tsakaninta da Marketing and sales manager, sai Head of operation da quality control manager, bayan sun gama meeting akai kiranta da mata tambayoyi akan dai wannan zane nata da company zai fitar. Yau ma da yake bata bu atar kowa yazo aukarta da wuri ta tashi. Ta fito harabar companyn hankalinta akan agogon hannunta tana kallon lokaci suka kusa cin karo da assistant in CEO. Ha uri ya shiga bata itama ta bashi. Ta ra esa zata wuce idonta ya sauka akan AA Darma in dake tsaye shi da wani dattijo suna magana. Yau dai sanye yake cikin farar shadda al datai masa shegen yau da sake fitowarsa a cikakken bahaushensa an arewaci dan harda hula. Da sauri ta kauda kanta tare da ara sauri a takunta duk da hakan bai hanata kasancewa a nutsenta ba. Sarai AA Darma ya ganta shima. Amma ya basar ya cigaba da maganarsa da Alhaji Wakili. Alhaji Wakili tamkar uba ne a wajensa, dan kuwa abokine ga mahaifinsu, sai kuma hu ar kasuwanci ta ha asu, dan yanzu haka ma akan wannan project da zasuyi wanda Maanal tai zanen agogon Alhaji Wakili inne ya kawo mutanen.... Dai-dai Maanal ta fito gate in da nufin samun abun hawa wata taxi ke arin shiga cikin Companyn. Sai dai securitys sun hana mai taxi in shiga, sun tabbatar masa da dole wanda ke ciki sai dai ya fito ya arasa ciki da afarsa. Yanda aka bu ofar motar a fusace ya an ja hankalin Maanal, a mamakinta sai taga Huznah ce ke fita a motar. Jitai ma gaba aya ta ame a wajen ganin yanda Huznah in ke musu masifa da tabbatar musu akanta zasu iya rasa aikinsu. Sukuwa dai securitys in sunce bafa zasu bar mai taxi ya shiga ba dan dokar companyn ce hakan. Ko ma'aikatan wajen indai motar haya suka shigo a'ida anan suke sauka su arasa ciki da afarsu. Ran Huznah ya kai ma ura a aci, kuma dole ta ha uran ta sallami mai taxi in ta arasa da afar zuwa ciki. Ga ma'aikatan sun fara fitowa sai kallonta ake ana us, itako tana wani yau i da taku ai. Maanal dai tuni ta shige taxi in da Huznah in ta fita. Haka ta iso gida al'amarin nata mata kaikawo. Har jitai ta agara Didin ta ta shigo. Zuwa duba Auntyn RK yasata watsar da komai bayan tayi wanka ta shiga kitchen. Da taimakon Linda ta fara ha a cake da wasu an kalolin snacks da suka shirya zatayi dan dubiyar ita da Shahidah. Suna tsaka da aikin Shahidah ta shigo tare da yara data biya ta akko a makaranta yau da kanta. Dama haka take musu duk juma'a sai dai idan aiki ya