← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 104

Sashe 5

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a gefen hannunta itama tana fa in, Ke dai zauna nan kamar za'a hureki. Ni kin san bana wasa da cikina Murmushi kawai Manaal in tayi batare data bata amsa ba. Hakan yasa Amrah jan hannun Munaya tana mata wasa. Da wannan damar Maanal ta arasa cikin falon sosai. Cike da girmamawa ta kai du e duk da kallon wula ancin da Hajiya Yaya ke mata da sauran yaran ta shiga gaidata a mutunce. A yatsine ta amsa mata sau aya ta auke kanta. Hakan ya ona ran Maanal matu a amma sai ta daure, fuskarta da an murmushi ta maida ga sauran yaran ta shiga gaishesu dan duk sun girmeta. Babu wanda ya amsa mata sai ma tsoki da wasu suka ja mata. Dai-dai nan saurayin nan dake zaune a dining ya mi e zai fita a falon yana kai waya kunnensa alamar zaiyi magana. Ina kuma zakaje Yazeed? Uwar ta atse masa hanzari da ar tsawa-tsawa. Cikin dakiyarsa ya juyo da hannu yay mata nuni da waya zaiyi, batare da ya jira sake cewarta ba ya fice abinsa. Hummm! Wai shi mai wayo fa Mamma aya daga cikin ammatan ta fa a fuska a kumbure. Kafin wani ya bata amsa Maanal taja hannun Munaya suka fice suma. Duk rakata sukai da harara, sai kuma wadda tai maganar ta mi e zumbur tana fa in, Ina zuwa bari na muku le en asiri. Dan nasan ko rantsuwa zanyi babu kaffara dan ita Yaya ya fita a falon nan babu wata waya da zai amsa ALLAH nima na fahimci haka Nanah, dan tunda ta shigo ya dakata da cin abincin ma sai wani binta da kallo yake. Kinga muje A hasale Hajiya Yaya ta furta, Aiko da naci ubansa a gidan nan yau. Tunda na rabashi da yarinyar nan na kuma haramta masa ala a da koda inuwarta ma balle ita. Amma kuje ku ganar min yana ina Ai kafin ma uwar ta rufe baki sun fice da sauri har su uku. A dai-dai fitowar tasu kuma Manaal ke shigewa sashen Hajiya Basariyya. Hajiya Basariyya itace mace ta biyu a gidan. Itama dai in ba kanwar lasa bace ba. Dan ba mutuncin ne da ita ba. Sai dai ita akwai banbanci tsakaninta da Hajiya Yaya. Dan a zahiri baka isa fahimtar ita in wacece ba saboda macece mai fuska biyu. A zahiri akwai faran-faran da jama'a da son nuna ita in ta ALLAH ce. Shiyyasa mutane da yawa sai ta gama musu illa suke farga da ita in wacece. Macijin sari ka no e ce ita ta bugawa a jarida. Yaranta biyar itama a gidan kuma duk mata, dan ita bata da namiji ko aya. Huznah da Maanal ta fara ha uwa sanda ta dawo itace arta ta farko. Itama in dai family nata akwai ku i, dan Yayanta daya ri eta hamsha in mai arzi i ne. Kuma babban aminin Alhaji Usman Chalawa ne, suna hu ar kasuwanci sosai da har wasu ma ke ganin dukiyarsu a cu e take da juna. Shiyyasa itama bata yarda Hajiya Yaya ta aga mata hanci ta angaren dukiya dan kar ce tasan kar. Kowa najinsa a wani shege. Komawa su Nanah sukai nasu sashen cikin ta e bakuna. Dan Manaal na arin shiga sashen Hajiya Basariyya shi kuma yayansu nama ficewa a gidan da motarsa. Tun ma kafin su araso Hajiya Yaya data cika tai tab ta fara jeho musu tambaya cikin huci dan macece mai iba sosai. Irin ibar nan bata wasa ba. Dan ko daga nesa ka hango ta kasan ALLAH yayi manyan mata a wajen nan. Zaune duk suka zube cikin takaicin rashin samo abinda za'aci mutuncin Maanal da uwarta yau a gidan. Nanah tace, Mamma yama fita a mota. Ita kuma ta wuce sashen Momyn Suhana Cikin wafa da takaicin itama bata samu yanda take so in ba ta ce, Ya taimaki kansa. Dan wlhy da yau har shegiyar uwartata sai sun bar gidan nan. Kai na tsani mutanen nan a rayuwata Ai bake ka ai ba Mamma . Cewar arta ta biyu mai tana huci. Auren nata ne ya mutu kusan shekara uku kenan tana gidan. Dama ita kawai ta aurar, rana aya akai bikinsu da su Shahidah yayun Maanal. Sauran kuma ALLAH bai kawo ba, ko muce ruwan ido da jiran an masu hannu da manda irinsu ya hanasu auruwa. Burin kowannensu da ma uwarsu shine suyi auren warya tabi warya.. Bu e shafin zagin su Manaal sukai a falon kamar sun tare musu numfashi, sai Amrah ce keta ata fuska dan ita bata son hakan. Ita birgeta ma Ammien take a rayuwarta mace mai dattako da sanin ya kamata. Babu ruwanta da duk abinda iyayen nasu keyi a gidan sabgar gabanta takeyi kawai da anta. Ko su duk abinsu bazasu ta a cewa ga randa Ammien taima wani abu mara da i ba, amma tasa miyasa basa sonta da yaranta?... angaren Maanal can ma door bell ta fara dannawa kafin ta shiga. Shima dai sashen Hajiya Basariyya da suke kira da Momyn Suhana ya matu ar ha uwa. Girmansa kuma aya dana Ammie. Ita dai bata falon sai su Huznah da annenta dake cin dafaffen gya a suna hira. Duk sun zubar da kohon a saman lallausan carpet in tsakkiya ko'a jikinsu. Dan sun san mai-aiki ce zata gyara basu ba. Har zata juya batare data musu magana ba sai ga Hajiya Basariyya in ta fito daga kitchen ri e da kofi tana waya fuskarta da murmushi. A'a an Jos an dawo kenan? Ta fa a cikin katse hanzarin Maanal kamar tuni arta Huznah bata kawo mata labarin dawowar Maanal in ba tun azun. Juyowa Maanal in tayi fuskarta kadaran kadahan ta an kalla Hajiya Basariyya in da nata fuskan ke auke da murmushi mai ayatarwa, sai dai acan asan zuciyarta wani irin ma on tsanar Maanal in ne ke mata kaikawo. Risinawa Manaal tai tana gaisheta. Nan ma ta amsa cike da fara'a tana nuna ma Maanal in kujera da fa in, Haba sai kace wata ba uwa zauna mana Maanal ga an uwanki nan na bikin cin gya a ka kuci. Da fatan dai kun dawo lafiya? Kuma komai ya kammala? Kai kawai Maanal in ta jinjina mata kanta a asa, sai dai yanzu da an gajeren murmushi a fuskarta. Ganin bata zauna in ba Hajiya Basariyyar ta sake nuna mata kujera. Kai ta girgiza mata da kama hannun Munaya ta ce, A'a Momy mun gode dama munzo gaisheki ne kawai Masha ALLAH aiko ina godiya. Sai dai ni bana cin mi e gaskiya azo mini hira dai. Suma su Shahidah ki fa a musu ina godiya sun barni da jira. Tun azun har abinci nasa akayi dasu ga gya a da aka dafa amma shiru kake ji Zan fa a musu in sha ALLAH Momy . Maanal ta fa a cikin muryarta mai zurfi da nutsuwa. Daga haka ta kama hannun Munaya tana mata sallama. Da harara duk suka bita har Hajiya Basariyyar. Sai da ta gama ficewar harda turo ofar Huznah taja tsoki da fa in, Ni wlhy Momy ina mamakinki, kiyita wani musu magana mai da i. Shegu sunzo sun gaje mana gida baka isa kai magana ba Daddy ya kama fa in yayansa ne suma na halak. Ko ina suka zama an nasa agololi. Ni ko wanda ma yakema kallon an nasa ilama da cikinsu tazo. Hummm Kawai Hajiya Basariyya ta fa a tana kaiwa zaune batare data kula maganar Huznah in ba. Hakan ya sake bama yaran haushi suka cigaba da zagin Maanal dan kamar ma sunfi tsanarta fiye da sauran an Ammien. Duk da kuwa sun i jinin Hameed ma da Waleed da Ammien ta haifa a gidan suke matsayin uba aya dasu. Balle da Daddyn ke tsananin nuna musu soyayya. Dan yanzu haka ma yana tare dasu asar Amurika yin hutu. Duk da dai yace taro zaije ya tafi da su. Amma babu wani taro kawai yaje dasu ne dan hutawa na sati har biyu... Rai ace Manaal ta koma sashensu. Sai dai yanda bata gayama kowa abinda ya faru ba babu wanda ya tambayeta. Sai ma zama tai suka fara hirarsu. Babu jimawa kuma Daddy ya kira Ammie ta video call. Daga nan suka gaisa da shi ya bama Hameed da Waleed da Ammien ta haifa a gidan. anensu kenan guda biyu. Yarane matasa da zasu iya kai shekara sha biyar da sha uku. Suma duk kamanin Ammie suka biyo kamar su Maanal in. Sai dai su farare ne sun kwaso hasken fatar Alhaji Usman Chalawa sosai kasancewarsa farin mutum tas.. Suna cikin hira da annen nasu ne babu zato akai knocking ofar falon. Kafin wani yay magana a cikinsu mai knocking in har ya shigo. A take Maanal ta shanye fara'ar fuskarta da maganar da take da Waleed ko nace fa a irin na sako duk da kuwa ta girmesa sosai. Kauda kanta tai da jan mayafin abayarta daya zame ta rufe gashinta da yau, yayinda su Amaal ke masa barka da shigowa. Shiko yana amsawa da an murmushi hankalinsa akan yaransu dake gaishesa duk da sai da ya gama arema Maanal kallo a kai-akaice. Gaban Ammie da hankalinta itama ke kansa tana an murmushi ya araso. Cike da girmamawar da yake bata ya rissina yana gaisheta. Da kulawa take amsawa itama, kafin ta ora da fa in, Baka wuce Abujan ba kenan? Eh Ammie fasawa nai saboda wanda zanje wajensa yace yana Lagos sai gobe zai dawo. Nima kawai sai na bari sai goben na tafi dan bana son naje naita zaman jiransa ina kuma da abinda zan anyi anan To ALLAH yayi jagora. Yay muku albarka, ya kuma saka muku hannu a dukan al'amuranku Amin ya rabbi Ammie Nagode sosai . Ya fa a cike da jin da i yana maida hankalinsa kan Maanal dake arin tashi tabar falon. Kansa tsaye ya furta, ar hidimar asa yaushe kika dawo? ........ Hummm yanzu fa aka fara shimfi ar bama wasan ba. Mi kuke tsammani. Yazeed, ga kuma RK. Ga Maanal da bama musan al iblarta ba. Shin wai mi aka AJIYE A DUHUN nan ne? Ya dai kamata a haska mana mu gani ko zamu tayasu lalube Maza garzayo cikin tawagar littafan zafafa
Chapter 5 · 0% Book details