← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 104

Sashe 89

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka an ya rage sukai biyu. Ita dam bata san Giro ba bata san an Giro ba.... ________ Babu wanda ya sake bi takan su Ammie a gidan duk da wasu suna son kawo musu abinci suna jin tsoro ne. Anan ofar akin sukai sallar magrib da isha'i. Sai kusan tara saura Babu ya shigo tare da Baba Haruna. Ganinsu a inda ya barsu su da kayansu ya sosa masa zuciya sosai. Baba Haruna kam a fusace ya shiga akin Gwaggon. Sosai ya mata tas da abinda tayi in, ya kuma tabbatar mata wlhy a wannan karon idan tace zatai wani abu to ta tabbatar shi bazai auka ba ofa a bu e take gareta. Wannan kalmar na tayar mata da hankali akan mijin nata. Dan tasan igiyar nan aya tak ke ri e da aurensu yanzu. Bakuma zata so ace ya tsinketa a yanzu da suke a shekarun tsufa surukai cike da gari ba. Shi da kansa ya fito ya shiga dakin dake a mallakin Ammien, akin duk tarkace ne ma a ciki, dan haka ya fita babu jimawa sai gashi da almajirai kusan biyar, su ya saka gyaran akin, shi kuma Babu ga fita nema musu abinci da maganin da Maanal zata sha dan zazza in ya dawo. Dandanan aka gama gyara akin, aka kawo katifa da tabarmi aka saka musu. Harda turaren wuta na tsinke baba Haruna ya akko a akinsa aka kunna, dan yanzu shine ya mayi mahaifinsu a gidan, shine ke da almajirai yake koyarwa, dan haka ya koma akin zaure inda suka samesa na mahaifinsu da zama kenan. To da yake tunda yaga Gwaggo na niyyar kashe katifar dakin Ammien sai ya saka aka auketa ya maidata can akin nasa aka lullu eta, sai idan Babu yazo ake kawo masa, daya tafi kuma yasa a maidata can. Gajiyar tafiya tasa basu ma wani iya cin abincin kirki ba dan ma harda shayi, suna son yin wanka basu san yaya zasuyi ba, dole suka hakura suka kwanta a haka. Dama ita Maanal tuni tayi barci abinta, duk da barcin nata bana da i bane ba. Washe gari dai sun an samu kulawar mutanen gidan sakamakon ganin Baba Haruna tsaye akan al'amarin su. Dan har koko an kakkawo musu a wasu sassan. Duk da ma dai su yaran sun kasa sha sai Ammie ce tasha. Kosan da Baba Haruna da bread ya saya musu kawai suka iya ci, sai naman jiya da Babu in ya saya musu basu ci ba. Yanda Maanal ta tashi da zazza i sosai dole Babu ya auketa zuwa asibiti. arin ruwa suka saka mata dan jikinta duk babu arfi, hakan yasa suka jima can har sai bayan zuhur ya dawo da ita. Anan ne yake sanarma Ammien Abban Fadeel ya kira shi sun gaisa, itama Oum nata nemanta wayar a kashe. Sai lokacin Ammie tama tuna da wayar tata, ta bincikota a bag sai taga ashe ta mutu ma babu caji. Dole ta bama su Shahidah tace suje waje su nema yara su rakasu inda ake caji sukai mata. Badan sun so ba suka fita, dan basa aunar ganin hararar da Gwaggo ke musu da kallon tsana. Sai zuwa yamma suka amso mata tai kiran Oum, lokacin Maanal ta tashi a barci amma sai unci take ta i kula kowa abinci ma sai da Ammie tace zata zaneta sannan taci sa ka an. Amma yanzu tana jin ance Oum tai wata irin zabura tazo ta nanu e Ammie. Dole Ammie ta ta aita gaisuwar da suke da Oum in ta bata wayar, dan yi take ma kamar zata warceta. Oum na jin muryar Maanal itama ta saki murmushi... Oh oh! My Baby I miss you Cike da zumu i Maanal ta ce, I miss you too Oum. Oum ina Besty? Dariya Oum tayi tana mai jinjina kanta idonta akan Ajwaad dake kwance a gadonta, tunda yaji ta ambaci sunan Maanal shima ta kafeta da idanunsa. Wayar ta mi a masa tana fa in, Gashi nan kin barsa da ciwon kewa Baki Maanal ta tura gaba, cike da shagwa a ta ce, Oum ai nima banda lafiya ina ciwon kewarsa Dariya Oum ta sanya, hakama Shahidah da Amaal. Ammie kama sai ta girgiza kanta kawai. Ganin su Shahidah na mata dariya ta tashi tana harararsu da murgu a musu baki ta fice a akin. Ammie na kiranta akan ta kawo mata wayarta kar tai mata arna bata dawo in ba. Gwaggo na tsakar wajen nasu tana ha ama dabbobinta dusa, suna ha a ido da Maanal ta harareta, itama ko ta rama da murgu a mata baki ta auke kanta. Ai sai Gwaggo tai mutuwar tsaye da mamakin wannan fitsararriyar yarinya. Ita zata harara ta rama wannan jaririyar ar?. Oho ko'a jikin Maanal, dan kujerar Gwaggo dake a ofar akinta ta zauna abinta. Sai kuma cikin shagwa a ta ce, Besty! Wata irin ajiyar zuciya Ajwaad ya sauke yana lumshe ido da ya zame masa abi'a duk da arancin shekarunsa. Sai kuma a cikin muryarsa mai sanyi da zurfi ya amsa da, Oummyim! Haushina kake ji dan na tafi na barka? Banfa da lafiya nima, yau har asibiti Babu ya kaini akamin karin ruwa . Ta are maganar muryarta na rawa alamar son yin kuka. Tashi zaune Ajwaad yayi sosai, cikin damuwa ya ce, To kar kiyi kuka, nima banda lafiyan ai, jiya saida aka min arin ruwan Kukan ta sakar masa kuwa, da fa in, Besty nidai kace Babu ya dawo dani wajenka. Ni bana son nan. Akwai muguwar mata a garin. Yanzu ma ka ganta sai hararata take... kuka sosai yaci arfinta Sosai hankalin Ajwaad ya sake tashi daga can, sai arin lallashinta yake yi amma tana ara arfin kukan harda tutturza afafu. Ga Gwaggo ta zuba mata wani shegen kallo. Kukanta yasa Shahidah fitowa. Sai dai suna ha a ido da Gwaggo ta koma ciki da sauri. Dama a tunaninsu ko wani abu akama Maanal in tunda sun san halin muguwar kakar tasu sai a hankali ce. Sosai Maanal take kuka har sai da Oum ta amsa wayar daga hannun Ajwaad da duk ya rikice da kukan nata itama tana lallashinta da tabbatar mata Bestien nata zaizo ya sameta. Da yar tai shiru sannan Oum ta maida ma Ajwaad waya suka cigaba da hirarsu mai cike da shirme da shiririta musamman ga Maanal dan ko yaya shi Ajwaad ya an tasa ya fara hankali.... Sam rayuwa a Giro batama Ammie da yaranta da i. Maanal ce ma dai babu ruwanta, tashin hankalinta kawai ace ta yini batai waya da Ajwaad ba. Anan ne zaka ganta kamar mara lafiya. Amma da sunyi waya sai ka walwalarta ta dawo. Sai ma ta fice wasa cikin gida abinta. Maanal dai dama jaruma ce a fagen iya fa a da tsokala, anan in ma duk da matsin da suke a ciki bata canja ba. Dan kuwa jibgar an mutane take yi, idan kafi arfinta kasha asa a cikin ido. Gwaggo kuwa idan ta harareta itama ta rama. akinta kuwa kai tsaye take shiga tace tana son abu kaza. Idan Gwaggon ta korota da zagi ta i fitowa. Kota warto abinda take so in ta fito a guje. Wannan hatsabibancin nata yasa Gwaggo tafi tsanarta fiye da kowa. Kullum cikin aibantata take da zaginta. Abin na damun Babu da Ammie sai dai babu yanda zasuyi, dan Ammie tama Maanal fa a akan shiga harkar Gwaggon amma yarinyar nan data faki idon Ammie sai tasan abinda taima Gwaggo. A haka dai sukai sati uku a Giro, duk sun fita hayyacinsu sunyi ba i sun rame saboda rashin abinci mai inganci. Suna a kwana na ashirin da biyar Babu yazo ma Ammie da batun wai zai yi aure. Sannan suma kawunan sa sunyi magana akan Shahidah da Amaal ya kamata a musu aure dan sun isa, musamman ma Shahidah data fara zama uwar mata. Dan haka sun yanke hukuncin ita Shahidah ta auri Lado an wajen Badaru. Ita kuma Maanal asimu an wajen Sagiru. Wani irin tashin hankali ne ya ziyarci Ammie. Ita ba auren Babu in ne damuwarta ba, batun Shahidah da Amaal......... ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 9:48 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ .......Kuka sosai Ammie ta sanya ma Babu da ro o da magiya, amma sai ya nuna mata shima bada son ransa bane. Dan bazai so yaransa suyi rayuwar garin ba, ba kuma zai so a yanke musu karatunsu ba. To amma bazai iya jayayya da an uwan mahaifinsa da an uwansa ba. Ina sam wannan batu bai shigi Ammie ba. Dan tasan wannan ba umarnin kowa bane sai Gwaggo. Hankali tashe taje ta samu Gwaggo da kuka da ro o, sai Gwaggon ta rufeta da zagi ta kuma juya maganar. Dan kuka ta sanya da kururuwa wai Ammie ta sameta har aki tana mata garga i idan bata saka Babu ya janye batun ara aurensa ba sai tabi dare ta kasheta. Dandanan wajen ya cika da mutanen gidan harda makwafta. Kasancewar Ammie nada tabon fitar kishiya yasa kowa ya yarda da batun Gwaggo. Nanfa akaita cancana magana da zagin Ammie har saida Baba Haruna ya shigo gidan ya tsawatar. Sam Ammie bata san miya rufema Babu ido ba, yana dawowa gidan Gwaggo ta fa a masa arya da gaskiya sai ya hau ya zauna. Aiko ya birkice mata yayta tujara a tsakar gida mutane naji, shi bazai yarda a raina masa mahaifiya ba. Ai ba a kanta aka fara kishiya ba. Shi ya gaji da ba in halinta. Idan bata gode masa ba bata tsine masa ba. Shekara nawa yana zaune da ita zaman ha uri badan ya ta a jin sonta a zuciyarsa
Chapter 89 · 0% Book details