Sashe 79
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da daga gani zatai an karen surutu. Sallama ta sake yi bayan yarinyar ta matsa ta bata hanya, batare da jiran amsa ba kawai ta shiga auke da handbag nata tana fa in, Ammie, Hameed, Waleed wai duk kuna in...... Turus ta ha iye sauran maganar sakamakon saukar idanunta akan Ammie dake zaune kanta a sunkuye kamar ma tana kuka. Da sauri ta saki bag in hannunta ta nufeta, a gabanta ta dur usa tare da ri o hannunta tana mai le a fuskarta. Ammie miya sameki kamar kina kuk....? Nan ma ta kasa arasawa ganin fa da gaske kukan Amma keyi. Amma sai Ammie in ta sakar mata murmushi da sake jim e hannunta cikin nata tana arin sharce hawayen da ayan hannun. Ina tuni Manaal da zuciyarta ta tsarga tai wata irin juyawa tana kallon wanda ke cikin falon. Nene ta fara kalla. Sai Daddy, sai wani dattijo daya sata an sakin baki, tana kai dubanta ga wanda ke a gefensa ta mi e zambar, jikinta har wani tsuma yake ta nuna tsohuwar dake a gefen mutumin da ta zuba mata idanu. Sai dai kuma ta kasa ma magana lips inta ne kawai ke an karkarwa. A hankali Ammie ta ri o hannun nata cikin tsawatarwa ta ce, Manaal minene haka kike yi. Ki zauna ki gaishe su Ammie never!! Ta fa a wani irin kuka dake zuwa maka batare daka shirya ba na kufce mata. Hannunta dake cikin na Ammie ta warce ganin mutumin ya yun ura ya mi e da alama wajenta zai nufo. Tuni tai ofar dake cikin falon da gudu abinta tana sakin wani irin kuka mai ban tausayi da ta a zuciya. Duk kallo suka bita da shi. Yayinda mutumin ya furzar da zazzafar iskar bakinsa ma oshinsa na wani irin kaikawo a wuyansa da sauri-sauri alamar shiga tsananin damuwa. Tsohuwar nan ya kalla, itama kallonsa take cike da damuwa. Kanta ta an girgiza masa. Sai ya sake furzar da huci mai kauri yana komawa ya zauna a inda ya tashi saboda maganar da tsohon nan yay masa. Nene ce ta katse shirun nasu da fa in, Kuyi ha uri mu bata lokaci zata huce. Kunga ana saka ran sai ma gobe in ALLAH ya kaimu zata iya tazo gata ma tazo yau babu zat....... Sauran maganar ta ma ale sakamakon shigowar Shahidah da Amaal dake dariya Barrah da Haneeff biye da su... Sororo Amaal da Shahidah sukai suma cikin wani yanayi, sai Shahidah ce tai arfin halin juyawa ta an kalla Ammie. Ganin kan Ammie a gefe ita bama kallon ta inda suke take ba ya sakata maida kallonta ga Amal da itama ta ago. Sai kuma duk suka maida kan suka du asa fuskokinsu na sake bayyanar da fushinsu. Nene ce tai arfin halin musu sannu da zuwa. Sai kuma ta nuna musu wajen zama na kujerun dake kusa da su. Wani irin tsuma jikin Babu dake tsaye kamar ma wanda ya daskare yake, gashi ya zubama Amal da Shahidah idanu kawai... Shahidah bakuga ba i bane? Nene ta fa a cikin son katse musu yanayin. Kallonta duk sukayi, da ido tai musu nuni da mahaifin nasu. Wani irin taunar lips Amal tayi, sai kuma tai yun urin barin wajen tana hawaye. Ganin haka yasa itama Shahidah yun urawa zata bar wajen da sassarfa, amma sai carab Babu ya ri o hannunta. Cak ta tsaya hawayen da take ri ewa na rige-rigen zubowa. Shahidah Ya kirata cikin tsananin taushin murya da sanyi. Hawayenta ta share tare da juyowa cikin dakiya ta kallesa. Hannun nata ya saki, dan duk da ba kallon raini ta masa ba ko wula anci har tsakkiyar ransa yaji nauyi da tasirin kallon. Batace masa komai ba itama tabar wajen tabi ar uwarta data shige akin Ammie. Duk abinda ke faruwa a idon kowa ne harda Daddy dake a falon, hatta Ammie datai uwar watsi da su tana kallonsu ne ta gefe ido...... Tsohon nan ne yayi murmushi, da fa in, Masha ALLAHU girman an mutum ba wuya. Shekara bakwai da wasu watanni kawai da bamu gansu ba sai duk suka canja mana kamar ba su ba Murmushi Nene ta sake yi mai fa A sosai su Maanal duk sun canja musamman ma Maanal in. Dan wannan gaba aya ba waccan Maanal in da kowa ya sani bace ba. Sai dai muyi fatan kuma yanzu ALLAH ya kawo miji na gari A tare suka amsa da Amin. A hankali Ammie ta mi e tana fa in tana zuwa. Babu wanda ya dakatar da ita ta nufi akin da Maanal in ta shiga, dan tafi tsoron yanayinta fiye da na Amaal da Shahidah. Gashi taga su akinta suka shiga, ita kuma Maanal nasu ta shiga..... Fitowar ta daga bayi dai-dai da shigowar Ammie akin. Juyawa tai da sauri zata koma cikin bayin Ammie ta dakatar da ita. Maanal! Cak ta tsaya sai dai bata juyo ba. Sai ma hawaye dake rige-rigen zubowa daga idanunta wanda dama su takeyi tunda ta shiga wankan. Cikin acin murya da fitar sautin kuka ta ce, Ammie waya kawosu garemu? Mi sukazo yi mana? Mi suke bu ata kuma yanzu a garemu. Ko anan in ma sun zo su koremu ne? Sun zo su sake tozartamu a idanun mutanen arzi inmu na nan ne suma? Ko sunzo su sake shegantamu su aibanta ki..... kuka yaci arfinta ta kasa cigaba da maganar. Hannu Ammie takai ta share hawayen da suka wanke mata fuska itama. Tare da matsowa kusa da ita, hannunta ta ri o tare da juyo da ita suna fuskantar juna........... ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ ......... Maanal! Ammie ta kira sunanta cikin rawar murya tana mai share mata hawaye da sakin murmushi mai ciwo. Da yar ta sake arin yin magana amma ta kasa saboda muryarta dake neman sar ewa. Sai kawai ta jawo Maanal in jikinta ta rungumeta tsam-tsam. A tare suka saki kuka mai arfi. Ammie kice su tafi, bana son ganinsu wlhy. Sam bana aunar sake ganinsu a rayuwata. Ko tunasu nayi ara jin tsanarsu nakey..... yanda take magana cikin kuka itama Ammien cikin kukan ta ce, Shiiiiii bana son irin wannan maganar sam Maanal. Shi in mahaifinku ne. Ita in kakarku ce. Sunada muhimmanci mai girma da hakki a kanku. Koma mi kike tunani ki bari kinji, wannan tsakanin ni da su ne. Kuma ai komai ya wuce ko Bai wuceba Ammie, bakuma zai wuce ba, har abada kuma bazai wuce ba. Ni dai kawai su tafi. Idan ba hakama zan bar musu gidan. Gara na wuce na koma Abujan. Idan sun wuce sai na dawo Babu inda zaki je Autana. Kin san yanda nayi kewarki kuwa. Wata nawa ban ganki ba sai video call da bai gamsar dani. cikin lallashi Ammie take maganar, tare da kama Maanal suka koma bakin gado. Sosai take matu aunar Autar ta, dan ita ta fuskanci jarabawa guda uku ne a lokaci aya. Shiyyasa ta fisu jigata da galabaita. Ga babbar jarabawar ciwo mai ha ari da take tare da shi. ALLAH ma dai ya addara tana da sauran kwana da tuni ta zama tarihi a cikinsu. Shigowar Nene ya katse Ammie daga lallashin Maanal in. Kofin hannunta ta mi ama Maanal in da fa in, Ga masoyiyar taki tunda kun mamemu, muda ke muku shirin zuwa wani satin biki sai kawai ku diro mana yau babu notis ja'irai kawai Hannu takai ta share hawayen da suka gagara tsaya mata. Fuskarta a e ta ce, Ni garin ya isheni Nene kuma ina kewarku sosai. Cike da dabara irin ta manya Nene ta sanya dariya da dungure kan Maanal. Ja'ira baki son garin amma gaki nan kinyi yau ai. Nifa har wani iba naga kinyi ma, ji kumatu dan ALLAH ko Asiya? . Ta are maganar da kallon Ammie tana jan kumatun Maanal. Murmushi Ammie tayi cike da ara jin aunar Nene dake tamkar mahaifiyarta a yanzu, ta matu ar taka rawar gani akan lamarin Manaal musamman a sanda take a halin mutuwa da rayuwa. Ta jinjina kanta da share sauran hawayenta tana fa in, Sosai kuwa Nene. Autah tayi iba ba kamar sanda ta dawo sarvese in nan ba. Ga fatanta yay wani kwanciya luff abinta halan ma bata tunawa damu ne a can Da sauri Maanal ta waro idanu akan Ammie, sai kuma ta shagwa e fuska da fa in, Kai Ammie kema kina biyema Nene ko? Dariya Nene da Ammie sukayi a tare. Nan fa suka cigaba da tsokanar Maanal har sai da sukaga ta an sake tasha kunun gya ar da Nene ta kawo matan. Ammie da kanta ta akko mata kaya ta tashi ta shirya. Tana arin maida towel in datai wankan cikin toilet Daddy yay sallama.... ___________ A bala'in hargitse Hajiya Basariyya ke kallon Huznah. Hakama sauran an uwanta. Sai kuma duk suka zaburo kanta suka baibayeta suna tambayarta accident tayi?. Babu wanda ta iya amsawa a cikinsu, hakan yasa Hajiya Basariyya ta kama hannunta kawai suka shiga bedroom. Kamar jira take suna shiga ta rungume mahaifiyar tasu tana mai fashewa da kuka. ameta itama Hajiya Basariyyar tayi hankalinta na ara tashi. Sai dai bata iya cewa komai ba har sai da Huznah tai kuka sosai sannan. Ruwa ta bata tasha kafin ta tambayeta abinda ke faruwa. Huznah bata oyemata komai ba daya faru tun daga zuwanta Abuja har yau da suke tahowa. Shiru tayi tana nazarin komai daki-daki. Ta jima shiru kafin ta mi e tana cema Huznah, Tashi kije kiyi wanka zan saka Afrah ta kawo miki abinci da magani, sai kisha ki kwanta ki huta zamuyi magana anjima Kai kawai Huznahr ta