← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 104

Sashe 100

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

an daga aikinta tama fita itama koda safe ta tsare Babu in da tambayoyi. Wannan kuka da amarya tasha da ihun iskanci yasa kowa ya yarda ta kawo mutuncinta. Shi ko Babu tai masa aurin goro dan bashi da damar musawa. Ga wata irin kunya da nauyin Ammie da ALLAH ya jarabceshi da ita. Dan iri- iri ya kasa yarda ya ha a ido da ita a wannan yinin baki aya. Ko hanya suka ha a duk sai ya daburce. Itako Ammie ta dake abunta ko'a fuska bata nuna masa ba. Amma a dare na biyu saita tura Amaal da Shahidah kwana akin Zainabu aya daga cikin matan gidan, kasancewar tasan mijinta baya gari. Dan gara ta nesanta yaranta da shiyyar gaba aya kafin su fahimci abinda ke faruwa. Aiko Ammie tayi dabara, dan daren yau in ma bata canja zani ba. Sai da Safara tayi duk iya yinta ta hillaci Babu ya kasance da ita. Gashi dama ta irki magunguna shima an irka masa ta hanyar abinci. Ai sai ihun ya zama nasu su biyu yau ita da shi. Kai jama'a wannan iskanci dami yay kama haka. Cewar Gwaggo cikin mitar son yin barcin da suka hanata. Amma da safe ko'a fuska bata nuna ba saima kulawa take bama amarya ta musamman dan Ammie taji haushi. Sai kuma Ammien ta tabbatar mata ita ar halak ce dan bata nuna damuwarta ba koda a fuska. Kasancewar daren jiya ta kwana salla da karatun Alqur'ani sai ta tashi sakayau zuciyarta cike mamaye da farin ciki. Musamman daya kasance da safe ta kira Oum a waya sun sha hirarsu harda Maanal dake ta faman bata labaran da in da Oum da Bestyn ke ciyar da ita. Shi kansa Babu in sai yanayin na Ammie ya sake jefa shi a aulani da unbin kunyarta da shakkarta ma.......... ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 9:48 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ .......... Ni bazan je ba barci nake ji Maanal ta fa a tana ture hannun Ajwaad dake arin sauketa a saman gadonsa. Dan akin ta shiga ta masa uwar arna a wadrobe insa da duk abubuwansa. akin nasu ne su uku amma a tsare yake, kowa da sashen kayansa da abubuwansa da kuma an gadonsa. Maanal kan shiga akin amma bata ta a komai na Fawzan da Babban Yaya sai na Ajwaad. Yau kamar abin arzi i suna tare a akin suna duk wani assignment in da aka basu na islamiyya kasancewar zuwa gobe zasu koma. Sai Mamy tai kiran Ajwaad ta aikesa kai mata marka en alale da zatayi a gidan yau matsayin abincin rana. Wannan dama Maanal ta samu ta canja akalar assignment in nasu ta koma zane-zanenta na fama. Dan tana son zane-zane sosai tun bata kai haka ba. Kai a makaranta makinta dabanne akan subject in ma saboda yanda tai matu warewa. Ko aiki aka basu awannan fanin hatta Ajwaad itace ke masa kai har su Fawzan bata suke da su Shahidah. Tana cikin zane-zanen ta ajiye ta sauka a gadon inda take ta koma masa bincike a kaya wai tana neman colours wanda take amfani da su sun fara bushewa basa mata da yau. Daga haka ta ige da arnarta tai kaca-kaca da komai. Tana jin zai shigo ta haye gadonsa da sauri tai likimo ita adole barci ma take yi. Shi ko tsaye yay kawai yana kallon fallasar datai masa da kayayyaki. Amma sai baice komai ba ya arasa saman gadon ya agota yana fa in, Tashi kije akin Oum tana kiranki. Shine ta e fuska da fa in itafa bazataje ba barci ma take ji. Shiru yay yana kallonta, sai kuma ya saki hannun nata ya koma kan kayansa ya fara tattarewa yana maida komai inda yake. Dan shifa duk da arancin shekarunsa komai nasa akan tsari yake da tsafta. Dan Ajwaad sam baya aunar azanta. Shiyyasa komai nashi a tsaftace a killace yake. Yana tsaka da maida kayan kuma sai ta sakko ta dawo wajensa tana masa surutu da nuna masa zanen agogon da tayi. Harara ya zuba mata ya auke kansa. Ita kuma ta tsaya tana kallonsa kawai. Sai kuma ta kumbura baki da jefa masa book in ta fice tana kuka wai ita babu ruwanta da shi kada ya sake mata magana kuma. Baiko kulata ba sai da ya kammala maida komai har books in nasu dake baje a gadonsa ya gyara gadon sannan ya auka book in data jefa masan. Shiru yay yana kallon zanen agogon da tayi, yayi matu yau tamkar ka saka hannu ka cirosa. Sai yaga ya banbanta masa da duk abinda ta ta a zanawa kodan bata ta a zana agogon bane sai yau oho. Samun kansa yay da bu e box in da yake adana muhimman abubuwansa ya saka shi ciki ya maida ya rufe. Daga haka ya shiga bayinsu dake a akin yay wanka ya canja kayansa sannan ya fito.. Wannan zanen agogon shine tushe kuma sila na ginuwar buri mai girma a zuciyar Ajwaad game da Maanal akan harkar zane-zane musamman agogo.... ____________ Sosai Giro tama Ammie zafi, zafi mai tsanani ita da yaranta. Dan haka ta ro i Baabu komawa Kano. Da farko ya turza, saboda gwaggo ta sakashi a aki ta kitsa masa cewar yabar Ammie ta cigaba da zama anan Giro. Itako a karo na farko tattara kayanta tsaf dana yaranta washe gari ya fita shi da amaryar tasa da Gwaggo zuwa can gidansu wai babanta babu lafiya ta baro Giro bisa taimakon Baba Haruna. Taso ta kwana a kabbi. Sai dai rashin mukulli dan yana a hannunsa yasa haka suka fallo hanya. Cikin amincin UBANGIJI suka iso cikin Kano kusan tara na dare. Sai da suka shiga gida ta kira Oum ta sanar mata. Sosai Oum tayi mamaki, amma sai ta ture mamakin ta kwantar da Maanal datai barci a jikinta ta fita. Kitchen ta shiga ta ha a musu abinci sannan ta kira Abah a waya Fawzan ya mata rakiya. Sosai hankalin Oum ya tashi da ganin yanda duk Ammie ta rame ta lalace. Gashi suna ha a ido kawai Ammie ta sakar mata kuka. Jiki na rawa ta ajiye abincin ta rungumeta tana lallashi. Sai da tayi kukan sosai sannan Oum tace ta tashi tai wanka. Wankan duk sukayi sukaci abinci, sannan Oum da Fawzan suka koma gida. Damuwa fal kan Oum. Washe gari rijib Ammie ta tashi da ciwo, dole suka wuce asibiti. Aiko aka basu gado dan likitocin sun tabbatar da jininta ya hau sama matu a. Sai da Ammie tayi kwanaki hu u sannan aka sallemta suka dawo gida. Washe gari cikon na hu u sai ga Baabu da amarya sun iso. Ammie batayi mamaki ba, kuma batace komai ba, duk da taga da wani wutar bala'i da rashin mutunci yazo garin. Dan babu kunya ya rufeta da zagi harda mari wai ta taho bada izninsa ba, ta raina masa mahaifiya miye-miye. Ko ci kanka batace da shi ba, hakan sai ya dake hasalashi ya fara nemo hanyar da zai musguna mata ta mangantu ya juye mata abinda ke a ransa. aki uku ne kacal a gidan, nata, nashi, sai na yara. Haka ya murje ido yace ta koma na yaran ita amarya ta zauna a nata. Ammie ta ce wannan ne kuma bai isa ba. Dan ita ba wula antacciya bace, ba gori ba gidan nan mallakinta ne idan ya manta tunda da ku inta aka sayeshi. To dama fa ta samu, haka Baabu ya dinga zuba tijara har sai da Abah yazo ya fiddashi a gidan aka samu masalaha. Daga arshe dai dole amarya ta zauna a akin shi. Tun wannan dawowa komai ya canja, canji mai ban mamaki daga ma'auratan dama gidan kansa. Musamman daga Baabu. Hatta ansa yanzu ja baya suke da shi, dan abu ka an zakayi ya hauka da zagi. Ranar ma ar lelen tashi Maanal har duka taci, aiko ta ha a inata-inata ta koma gidan Abah. Tafi sati bata shigowa gidan nasu kafin ta saki jiki kuma ta manta bisa tirsasawar Ajwaad ta koma shigowa. Ga amarya dai babu wata matsala. Ta kwantar da kanta yana fahimtar komai daki-daki kamar babu komai. Sai dare ta ishesu da ihu ita da miji. Wannan abu shine mafi girma tadama Ammie hankali, dole ta maida kwanan su Shahidah gidansu su Oum gaba aya. Dama yanzu batun miji Ammie bata da shi a gidan, Baabu yana tare da amaryarsa tunda suka dawo. Sai da suka cika wata aya cif sai gashi da takarda wai ya saki Ammie saki aya. Murmushi kawai Ammie tayi da fa in, ALLAH yasa haka shi yafi alkairi, amma kuma babu inda zanje. Zan zauna na cigaba da rainon ana har lokacin aurensu sai dai kai ka bar min gidan tunda dama nawa ne Wannan furuci nata shine y a kawo tashin hankali, tashin hankalin da dole sai da Abah da Oum suka shiga yanzu ma. Da yar dai aka sasanta bayan Abah ya nusar dashi illar abinda yake shirin aikatawa. Shine fa ya maida Ammie. Haka aka cigaba da ha uri Ammie bata da miji, bata ta a tada kai ta kallesa ba har tsawon shekara biyu. (Kenan dai tun da amarya ta tare ) Ko'a fuska Ammie bata nuna masa damuwarta, karatunta kawai take na Islamiyya da take zuwa da kula da tarbiyyar yaranta da sana'arta. Dan takai yanzu ma itace ke ciyar da kanta. Zuwa yanzu su Maanal fa an shiga secondary, Dan suna aji biyu ma duk da da yar suka amsheta saboda sunce tayi arama da yawa, yayinda Shahidah ke shirin kammalawa ita da Fawzan, babban yaya kuwa ya wuce asar Saudiya karatu. Amarya bata shiga sabgar Ammie,
Chapter 100 · 0% Book details