← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 104

Sashe 78

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai bakinta bai mutu ba sai sake jadadadama Huznah take idan bata fita a sabgar AA ba ALLAH sai dai ta kasheta. AA nata ne ita ka ai. Yanda taketa surutai yasa kowa ya fahimci akan AA suke fa an, dan in ka cire Mamy da su Abdul-hakeem sai ita Saheeba babu wanda yasan ala ar Huznah da zuwa gidan ma. Dole Abdull da Yaseerah da jikinta duk ke faman rawa suka kama Huznah zuwa mota domin kaita asibiti. Ita kuma Saheeba taja Nuratu sashenta. Nibras da bayanin Nuratu ya sata jin wani irin ayin ba in ciki a zuciya fuuuu ta wuce nasu sashen itama. Sai Mamy da Oum da Abah da Fawzan kawai aka bari. Cikin acin rai Fawzan ya ce, Wannan yarinyar sam bata dace da Ajwaad ba wlhy Abah. A haka kuke son aura masa ita tana abu kamar ar daba. Daga zuwan yarinya taji mata wannan mugun ciwon a fuska. Haka dama azun a asibiti tayi akan Lilly, tana wani tambayar wai ba itace tasan labarinta ba, uwar mi ta sani to? Mi aka gaya matan akan su Shahidahn Cike da mamaki Abah ya ce, Wace Lilly da Shahidah? Lilly dai daka sani Manaal da Shahidah na Kano Wani irin girgiza zuciyar Mamy tayi, haka Oum ma sai da ta an rumtse ido. Yayinda Abah ya furta, Fawzan kasan mi kake fa a kuwa? Da gaske kake yi? Wlhy Abah da gaske nake yi. Itama an kwantar da ita a asibitin ne shine suka shigo duba Auta Wani irin lumshe idanu Abah yayi zuciyarsa na masa nauyi a cikin irji........ ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ ........A angaren Maanal kuwa bayan fitar Shahidah text ta turama RK dan tana son su arasa maganar da suka fara. Ko minti biyu ba'a cikaba kuwa da tura sa on sai ga kiransa ya shigo. Kamar bazata auka ba ta dai daure ta aga in tare da saka hans free kawai. Sallama tai masa da sassanyar muryarta da a yau rauninta ya sake fita fili. Shima sai ya amsa mata da tashi sassanyar muryar. Tare da fa in, Gani a compound in ku Sosai mamaki ya kama Maanal, harta kasa oyewa sai da ta furta, Wasa kake amma? Murmushi yayi mai sautin da har taji, Da gaske nake my queen, dama ina gidan kusan minti goma kenan bana son takura miki ne kawai, harma ina shirin juyawa sai kuma ga sa onki Ajiyar zuciya Maanal ta sauke, zuciyarta na sake arfafata akan RK in. Tabbas bata bu atar yin rayuwar aure da kowa. Hasalima bata da burin yin auren kwata-kwata. Amma tasan iyayenta da an uwanta bazasu bari ba. Sai kuma Ajwaad, dole ne ta tabbatar masa da abinda yake ganin bazata iya ba. Zatai auren a cikin zuri'arsa kodan tabbatar masa da wannan Maanal in ta yanzu tafa banbanta da wadda ya sani a baya. Mi ewa kawai tayi ta an gyara hijjab inta na salla da har yanzu bata cire ba, sai an turare data arama jikinta ta fita. Babu kowa a falon dan su Barrah na tare da Abbansu basu dawo gidan ba. Kitchen ta shiga ta auka ruwa a tray da glass cup. A karo na farko ta nufi falon ba i sannan ta fita compound inda RK yake. Iso tai masa zuwa falon ba in, hakan sai ya sake bashi mamaki sai dai baice komai ba ya bita. Koda suka shiga ita ta zuba masa ruwa da kanta sannan ta zauna. A karan farko da yaji ya kasa daurewa ya furta, Gaba aya sai mamaki kike bani. Gani nake kamar bake ba Guntun murmushi kawai Maanal tai masa. Sai kuma ta kallesa. Idan ki a ya canja itama rawar canjawa take yi ai. Ina son ka san yanzu muna akan ga ar serious ne Hakane. Nima hakan nafi so mu kasance in Maanal. Na kuma ji da i da godema ALLAH daya kawo mu wannan ga A hankali ta ha iye an kwallar data ciko idanunta. azun mun fara magana sai dai bamu arasa ba, shiyya nace kazo yanzu dan in sha ALLAHU kamar yanda na sanar maka gobe zan wuce Kaduna. batare da jiran amsarsa ba ta mi a masa diary in data shigo da shi a cikin wata kyakkyawar bag. Amsa yay yana ciro sa daga jakan, sai kuma ya an jujjuya shi a cikin hannunsa sannan ya ago ya kalleta. Itama shi take kallo, dan haka ta janye nata idanun. Na yarda da kai fiye da yanda kake zato. Badan komai ba sai dan wasu dalilai. Sannan kai in koba komai jinin Oum ne. Wadda nake kallo uwa nagartacciya bayan mahaifiyata. Kaje da wannan zaka samu dukkan tarihin rayuwata data shu e a ciki, dan in har akwai abinda na rage ban rubuta ba to zai kasance alilan ne, ko kuma baida muhimmanci. Bayan ka gama karantawa zaka iya sake tun-tu ar Oum dan sake samun gamsuwa. Daga nan sai ka yanke dukkan hukuncin daya dace koyaya ne zan amshe shi. Dan ALLAH in har baka gama karanta shi har arshe ba kada ka kirani a waya, kada kazo kaduna. daga haka ta mi e tsaye, shi dai kallonta kawai yace yama rasa abin cewa. Dare ya farayi sai da safe A karo na farko ya an ja numfashi ya fesar, sai kuma ya jinjina mata nasa kan yana mi ewar shima. Haka suka fito a tare kamar wasu kurame. Dai-dai nan motar Abdull ke shigowa gidan. Duk tsayawa sukai suna kallon motar har wanda ke ciki suka gama fitowa. Da mamaki RK ya furta, Abdul-hakeem . Sai kuma ya juya yana kallon Maanal. Itama shi in ta kalla, tare da fa in, Ka sanshi ne? Kafin ya bata amsa Yaseerah ta fito da Huznah, fuska duk facin bandage musamman arinta na dama. Nufarsu RK yayi, dan haka badan taso ba itama tabi bayansa. Duk da Abdull yayi mamakin ganin RK a gidan sai ya danne, sai da suka gaisa RK yake tambayar abinda ke faruwa idonsa akan Huznah. Bayani Abdull yay masa a ta aice. Kamar RK in zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya yana kallon Maanal. Inaga ni bara naje, ki musu iso ciki ko? Kai kawai Maanal ta jinjina masa, sai kuma tai masa ALLAH ya kiyaye hanya tai gaba abinta batare da tace ma su Yaseerah komai ba.. Suma komai basu ce in ba suka bita kawai, yayinda Abdull yake ta satan kallon Maanal in. A ransa yana raya aji da nutsuwar yarinyar, gata yawa da wani skin nata mai aukar hankali da yay aranci ga matan wannan zamanin da suka maida kansu fararen dole da bleaching..... Gaba aya Shahidah kasa cewa komai tai da bayanin Abdull in. Dan Yaseerah taso su oye amma Abdull ya kware zance ga mijin Shahidah abinsa, dan shi dai namiji ne babu ruwansa. Godiya sukai musu, suma suka mi e suna musu sallama dan dare ya fara. Dama ita Maanal bama ta tsaya a falon ba ganin kallon urullar da Abdull in ke mata a kaikaice duk da kuwa hijjab ne a jikinta har asa. Ko bayan wucewarsu da Huznah ta shigo akin Maanal bata kulata ba, tanata ma ha an abubuwan da zata wuce da su Kaduna ne kawai. Itama Huznah in bata kulata ba tai kiran mamanta a waya. Basu wani jimaba sukai sallama dan ta sanar mata ne kawai zata dawo Kaduna gobe.... _______________ A Kaduna kam kamar yanda Daddy ya fa a sunje Kebbi garin Giro asalin tushen su Maanal. Sai dai an samu sa ani tsakaninsu da manyan da ya kamata su gana da su. Dan kuwa an tabbatar musu kakarta da babanta da baffanta sunje Kaduna, wani kuma babban Senator ne ya aiko aka aukesu a mota wai zasuje wajen Asiya daya tabbatar musu yasan a inda take. Rasama abin fa a Daddy yay, Dan ya rasa yanda zai fassara zancen musamman akan batun senator da suka ce. Haka dole suka baro garin gwiwa a sage. Basu iso gida ba sai dare, zuwa lokacin kuma kowa yay barci, sai dai hakan bai hanashi zuwa ya sami Ammie a sashensa ba tana jiransa. A kallo aya da yay mata ya fahimci hankalinta a matu ar tashe yake kuma....... ___________ Washe gari Shahidah, Maanal, Huznah da yara suka tashi da shirin wucewa Kaduna. Dan yaran ma babansu yaje school insu ya daidaita komai. Jirgin asa zasu bi, dan haka Uncle Sadeeq in da kansa ya kaisu train station bayan sallar zuhur. Basuyi ko mintuna goma ba suka wuce. Koda suka iso Kaduna Amaal ce tazo aukarsu. Dan ita ka ai tasan da zuwan nasu sai Hajiya Basariyya. Itama saboda Huzna ne ta sani A dai-dai sashen Ammie Amaal tayi parking motarta. Bata ko gama kashewa ba Huznah tai ficewarta daga motar. Da kallo duk suka bita, sai kuma Amaal ta ta e baki da fa in, Wawuya kawai . Babu dai wanda yace komai tsakanin Maanal da Shahidah. Sai ma ficewa da sukai daga motar suma. Itama Maanal bata jira su ba tai sashen Ammie da sauri, dan kewarta take sosai, burinta kawai ta ganta a jikin Ammien. Da sallama ta bu ofar, sai kuma ta an tsaya turus tana kallon yarinyar dake arin bu ofar itama alamar zata fito. Yarinyar Maanal ta zubama ido. Dan sam bata santa ba. Itama dai yarinyar kallonta take yi. Sai kuma ta nuna ofar dake da takalma kusan afa goma tana fa in, Ki shigo mutanen gidan suna ciki. Muma ba i ne yau muka zo Kamar Maanal zatai magana sai kuma ta jinjina kai kawai tayi gaba, a ranta tana maimaita zancen yarinyar
Chapter 78 · 0% Book details