Sashe 103
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
in da ya sakama part in. Sosai tawaro idanunta waje, sai kuma ta tunzura baki gaba da fa in, Besty ALLAH baka da kunya . Ta are maganar da murgu a baki, sai kuma ta arasa ta auka pant in ta saka dan tana ganin yanda Didin ta suke amfani da shi ai. Kayan ta saka tsaf tanata kumbure-kumbure. Sai kuma ta auka wayarsa data riga tasan password in ta bu e. Hayewa gadon Oum tai ta sake kwanciya. Dan wani kalar jirin barci take ji sosai. Takai mintuna goma da kwanciya akai knocking ofar. Umarnin shigowa ta bada sai ga Bestyn ta. auke yake da tray a hannu, suna ha a ido ta risinar da nata. Shima baiyi magana ba ya ajiye abincin kawai ya wuce toilet in Oum in kamar wasu masu jin kunyar juna. Kayan data cire ya tattare hadda p inta dake a ace sosai. Tsabar rashin hankali da rashin wayo irin na Maanal maimakon ta wanke sai shima ta bar masa saboda yace tabar masa kayan data cire. Abin mamaki Ajwaad Sarkin yami da tsantseni sai gashi tsaf ya wanke kayan har sau biyu kafin ya sakasu a injin wanki harda bedsheet in Oum ya wanke fes. Sannan ya wanke bayin ya fita da kayan can backyard ya shanya amma banda p in daya shanya anan toilet in. Zuwa lokacin Maanal ta jima da komawa barci. Sai ma auke tray in abincin yay ya ajiye gefe sannan ya fice akinsu domin yin wanka... Rai a ace Oum ta dawo gidan tare da Ammie dake wani irin kuka mai ban tausayi saboda abinda ya faru a gidansu Maanal in. Da farko bata lura da canja kayan Maanal in ba dana bedsheet sai da ta zauna idonta akan trayn dake ajiye. Hannu takai ta ta a wuyan Maanal, sanyi alau zazza in ya sauka. Barcinta take hankali a kwance. Ajiyar zuciya ta saki mai kauri, sai kuma ta maida dubanta ga Ammie. Kiyi ha uri Asiya kukan nan ya isa. Kada kanki yazo yana miki ciwo. Tashi ma kiyi wanka ki shirya gidan baba zamuje. Dan na fahimci wannan karon sai na dangana al'amarin Habib da baba tukkuna, tunda baya gane yaren Aban su Fadeel da nawa. Kai kawai Ammie ta jinjina mata, ta tashi ta shiga toilet. Ita kuma ta bu e wadrobe ta akko mata wata sabuwar atamfa da bata ta a sakawa ba da gyale da duka abinda zata bu ata sannan ta fita. Harta nufi akin Mamy sai taci karo da Ajwaad. Sannu ya mata, ta amsa tana kallonsa ganin shima ya sauya kaya. Fita zakayi ne Auta naga ka canja shiga? Kansa ya girgiza mata, A'a Oum, wancan sun aci ne an jimm tayi sai kuma ta ce, Mamy fa? Tana ciki tunda kika fita. Oum ina kikaje wai? Naje nan wajen Ammien ku ne, yanzu ma zamu sake fita da ita gidan Baba. Idan Mamy ta tashi ka sanar mata, ga kuma Maanal nan na barci..... Kansa kawai ya jinjina mata. Ita kuma ta juya ta koma akinta ranta duk a dagule. __________ Shigar Baba Sardauna a cikin al'amarin Ammie yasa aka samu sau i tsakaninta da Babu a lokacin. Ga gwaggo ne dai babu abinda ta fasa wula anci yima Ammie take iya iyawarta. Tunda kuma ta yalla ido taga Maanal ta fara jini sai ta fara surutai, yara duk sun zama iyayen mata miye-miye. Saboda ayin Ammie kuma duk sun la ema masu ku i, indai kwa ayi abun yine suyi tayi watarana sai amma yaran cikkunan shege a titi. Babu wanda ya kula gwaggo da zatunkanta sai Maanal, rashin kunya ta mata sosai ranar har sai da ta saka Gwaggon kuka. Sai Ajwaad ne yazo yasa Maanal barin gidan da yar. Aiko gwaggo ta ha ata da Babu yace sai ya daketa. Jin haka Maanal ta daina shigowa gidan har kwana hu A yammacin ranar Maanal ta nema jini ta rasa. Tana son gayama Oum tana jin kunya. Gashi bata shiga gidansu saboda Babu yace zai daketa. Kawai saita yanke shawarar samun Ajwaad, akinsu ta le a, babu kowa sai babban yaya dake barci, dan haka ta fito. Can harabar gidan ta nufa, inda ta wuce Mamy da anwarta da suke kira Maman Saheeba suna hira. Kallon banzar da Maman Saheeba ke mata yasa ko gaisheta bayi take ba idan tazo gidan. Dan haka yanzun ma bata kulasu ba har Mamy in ta wuce garden neman Ajwaad. Tasan shi baya yawo, indai ba aikensa akai ba to zaka samesa ne a garden yana karance-karance daya aukama kansa yanzu. Wani lokacin har fa a suke yi dan ita karance-karance haushi yake bata, ya rage bata kulawa, bata san miyyasa ba bai son su cika ka aicewa daga ita sai shi a yanzu. A hankali ta zare novel in dake a hannunsa, fuska ya yamutse tare da ago idanunsa ya saukesu a kanta. Zama tai kamar zatayi kuka tana kallon littafin, sai kuma ta sake kallonsa idanun nata cike da hawaye. Besty wai mike damunka kwana biyun nan. Sosai ka canja min, musamman tsakanin nan. Ka auka dukkan hankalinka ka maida ga karatun novels. Baka son mu zauna muna hira mu ka ai, ko assignment zamuyi sai kace sai a gaban Oum ko Mamy. Kana yin abu kamar ma baka son ganina. Maimakon amsa mata sai kawai ya lumshe idanunsa masu haske sosai ya sake bu ewa a kanta. Tsohon lokaci kafin ya motsa lips insa ka an ya furta, Babu komai yanayi ne kawai Yanayi? Kansa ya jinjina mata kawai. Kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Fuska ta an shagwa e tare da fa in, Besty akwai matsala fa? Cikin an tsireta da idanu ya ce, Tami? Sake shawa e fuska tayi asa- asa kamar mai tsoron a jita ta ce, Na daina ganin jinin, kuma ALLAH kunyar fa ama Oum nakeyi. Ina son zuwa wajensu Didi ina tsoron Baabu ya kama ni Oh nine ba ya jin kunya? . Ya fa a yana tsatstsareta da idanu. Sai da ta waro idanunta waje sosai sannan ta ce, Kai kuma zanji kunya Besty? Kai fa Besty nane. Ni dan ALLAH ka gaya min yaya zan gane ya auke in kenan naje nai wanka. Kuma ai irin wankan da aka koya mana a islamiyya zanyi ko? Idanunsa kawai ya rumtse yana datse la ansa da arfi da ha ori. Miyyasa yarinyar nan bata ganewa ne wai? Ta a shin da tai ya sashi dawowa hayyacinsa. Ta sake marairaice fuska. Sai kawai ya samu kansa da bata amsa. Naji zan fa a miki. Amma lokaci yayi da zaki fara fahimta Fahimta? Mizan fahimta? Ba komai Ya fa a yana mi ewa. Tashi tai itama ta bishi, amma sai yay mata nunin ta koma ta zauna. Zaman tayi, shi kuma ya fice a garden in. Babu jimawa ya dawo da takarda ya bata. Kafin yace mata, Tashi kije na rubuta miki komai Batai musu ba ta mi e, hannu ya mi a mata. Idonsa akan novel insa dake hannunta. Sai da ta tura baki gaba sannan ta mi a masa ta wuce.... Kwana biyu dayin haka zazza i mai zafi ya kwantar da Ajwaad. Zazza in daya sanya har sai da ya kwanta a asibiti. Kwanansa biyar aka sallamesa. Ana sallamarsa kamar jira itama Maanal ta fara nata ciwon. Tasha jiki sosai kafin itama ALLAH ya bata lafiya.. _________ Zancen da Fawzan yayma Oum itama ta samu Abah da shi, shi ba mutum bane mai son takurama yaransa. Sannan yakan nutsu akan abu idan sunzo masa da shi ya dubi halaccinsa da haramcinsa a wajen UBANGIJI. Sosai yay nazari akan batun ya kuma nema shawarar Baba Sardauna. ari bisa ari Baba Sardauna ya bada goyon baya shima akan hakan, dan tunda har Fawzan in ya furta ai masa auren ai masan kamar shine yafi komai dacewa. Dan haka su Abah suka shirya zuwa Giro. Sun kuwa je. Alhamdullah Baba Haruna ya basu auren Shahidah da Amaal, basu baro ba kuma sai da suka bada komai har sadaki. Aka kuma tsaida ranar aure. Kasancewar Baabu ya zama abinda ya zama yasa sai da suka dawo Abah ya sanar da su daga shi har gwaggo. Wannan al'amari yay matu ona zuciyar gwaggo dan itafa duk wani jin da in duniya bata son ganin Ammie a cikinsa. angaren Mamy kam komai batace ba, sai ma addu'a datai da sanya albarka kawai. Haka an uwanta ma albarkar suka saka. Babban Yaya ya koma makaranta, haka Ajwaad da Maanal ma. Yayinda akema Fawzan nasa shirin yin sabuwar jarabawa shi da Amaal. A haka aka shanye watanni kusan biyar, su Amal sun kammala exam, akai bikin saukar Maanal da Ajwaad tare da walimar data ayatar. A wajen wannan walima ne Baba Sardauna ya arsa nasa burin akan Ajwaad da Maanal. Sai kuma bayan kwana biyu dayin walimar yazo har gidan abinda bai cika yi ba. Zaunar da Oum da Abah da Mamy yayi, bai oye musu komai ba akan batun da yazo da shi na son ha a auren Ajwaad in da Maanal tare da an uwansu. Ya kuma kawo musu hujja mai arfi akan abinda ya hango game da sha uwar yaran. Dan gara ya kasance akwai igiyar aure a tsakaninsu gudu sharrin shai an saboda kusancinsu yayi yawa. Gashi kuma suna a wata ga a ce mai ban tsoro akan duk wani yaro dake a wannan shekarun musamman ma shi Ajwaad da Babban Yaya ya sameshi ya warware masa komai akan halin da Autan yake ciki tun kafin ya koma, shiyyasa ya saka ido shima ya fahimci komai ya ya kuma tabbatar. Su duka ukun babu wanda ya musa ko jayayya akan abinda Baba Sardauna yazo da shi. Sun kuma gamsu da cewarsa akan ai shiru da batun kada a sanarma Ajwaad in da Maanal. Su kuma barsa da Baabu shi zai yi magana da shi. Haka kuwa akayi, Baba Sardauna ya kira Babu har gidansa sukai magana ta fahimta. Ya kuma gamsu shima ya bada goyon baya. Bayan haka Baba Sardauna yay kiran Baba Haruna shima a waya suka tattauna. Shima kuma ari bisa ari ya gamsu. Daga haka aka fara shirin bikin an gata su shidda. A angaren Babu babu wani waran shiri, dan